Sunday, 25 May 2014

MUSULMAI AL'UMMA CE GUDA


"Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah a kanku, a lokacin da kuka kasance makiya, sai Ya sanya soyayya a tsakanin zukatanku, saboda haka kuka wayi gari, da ni'imarSa, 'yan'uwa. Kuma kun kasance a kan gabar rami na wuta, sai Ya tsamar da ku daga gare ta. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa, tsammaninku, za ku shiryu # Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umurni da alheri, kuma su na hani daga abin da ake ki. Kuma wadannan su ne masu cin nasara # Kuma kada ku kasance kamar wadanda suka rarrabu, kuma suka saba wa juna, bayan hujjoji bayyanannu sun je musu, kuma wadannan suna da azaba mai girma". (Surar Aali Imrana, 3: 103-105)
"Saboda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini, kana mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah da Ya halitta mutane a kanta. Babu musanyawa ga halittar Allah, wannan shi ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba # Kuma masu mai da al'amari gare Shi kuma ku bi Shi da takawa, kuma ku tsayar da salla, kuma kada ku kasance daga mushirikai # Watau wadanda suka rarrabe addininsu, kuma suka kasance kungiya-kungiya, kowace kungiya tana mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai. (Surar Rum, 30: 30-32)

"Kuma abin da kuka saba wa juna a cikinsa, ko mene ne, to hukumcinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah. Wancan Shi ne Allah Ubangijina, a gare Shi na dogara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al'amarina. (Surar Shura, 42: 10)
"Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga ManzonSa da ma'abota al'amari daga cikinku. Idan kun yi jayayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kuna imani da Allah da Ranar Lahira. Wannan ne mafi alheri, kuma mafi kyau ga fassara". (Surar Nisa'i, 4: 59)
"Kuma lalle ne wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Ni, Ubangijinku ce, sai ku bi Ni da takawa". (Surar Mu'uminun, 23: 52)
"Kuma ku yi da'a ga Allah da MazonSa, kuma kada ku yi jayayya har ku raunana kuma karfinku ya kau, kuma ku yi hakuri, lalle ne Allah Yana tare da masu hakuri". (Surar Anfal, 8: 46)
Tun al'ummar musulmi tana jaririya a hannun Manzon Shiriya, Muhammadu (s.a.w.a), abokan gaban musulmi daga masu bautar gumaka da yahudawa da nasara da munafukai da masu neman fadanci domin arzurta kansu, suke kokarin kekketa al'ummar da hura wutar sabani da rarraba. Hakika da'awar Musulunci a karkashin jagorancin Manzon Allah (s.a.w.a.) ta fuskanci wannan kaidin ta kuma yi nasara kan yahudawa da mushrikai da munafukai, albarkacin jagoranci Annabi (s.a.w.a) da kuma lizimtar sahabbansa, zababbu.
Tarihin yadda Musulunci ya sha kokawa da wadan-nan magabta a zamanin Annabi (s.a.w.a) yana cike da abubuwa masu bayyana mana yadda masu jayayya da Musulunci, magabtan al'umma suka yi aiki da makamin rarrabawa da shuka sabani. Duk wanda ya bibiyi Alkur'ani Mai Girma da Sunnar Annabi (s.a.w.a) da dalilan saukar ayoyin Alkur'anin, sannan kuma ya dubi tarihin farkon sakon Musulunci zai lura da cewa sakon ya yaki wannan ciwon mai neman rusa addini, yakin da ba kakkautawa. Ya kuma gargadi musulmi kan kada su fada cikin sabani da rarraba kamar yadda al'ummar da suka shude suka fada. Alkur'ani ya hori musulmi da hadin kai da riko da juna, ya kuma yi gargadi kan rarraba da sassabawa da jayayya, yana mai suranta irin makomar masu yin hakan da cewa:
"....Kuma kada ku yi jayayya har ku raunana, karfinku kuma ya tafi....".
Hakika Alkur'ani ya yi gargadi kan jayayya da sabani wanda shi yake kai mutane da makoma mai muni da rauni da ragwanci da kasawa da gushewar karfi da daula. Haka nan kuma ya gargade mu kan zamowa kungiyoyi masu gaba da neman halaka juna, sashi na dukan sashi, sashi na la'antar wani sashin tamkar yadda mushirikai da batattun al'ummai masu keta kalmar Allah da wasa da shari'o'inSa suka kasance.
Alkur'ani mai girma yana fuskantar da wannan al'umma da ta hada kai bisa kalmar tauhidi:
"...Saboda haka ka tsayar da fuskarka ga addini... wannan shi ne addini madaidaici".

No comments:

Post a Comment