Saturday, 24 May 2014

MAI DOKAR BARCI YANA GYANGYADI

                                                                      


Mai karya doka sunan sa mai karya doka: Shiah kuwa "Itiqadi" ne da aikin kirki
Jagoran harkar musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaquob El-Zakzaky ya jawo hankalin al'umma game da dokar nan ta hawa mashin da gwamnatin jihar Kaduna ta fara aiki da ita a jiya Laraba 21 ga watan Mayu 2014 bayan kammala tafsirin Al-kur'ani da yamma a Husainiyya
2014/5/22 12:26
Ga yadda jawabin ya kasance.
"To akwai wani abu da akace, ko jiya ne, ko yau ne dokar hana goyo a babur a jihar Kaduna ta fara aiki. To tun kafin ta fara aiki naji ana ta wadansu rade-radi, cewa su 'yan Shi'a fa ba zasu bi doka ba, kuma in ba su bi ba, to muma ba zamu bi ba.
Toh ni iyaka abin da na sani wannan ba al'amarin 'Islam' ne ba ko 'Christianity' ba, ko Shi'a ko Sunna ba. Doka ce ta Jiha, ta rashin kan-gado da hikima. Bata shafi Shi'a ko Sunna ba, banga inda ta shafi addini ba. Ballantana ace akwai wani dan Shi'a, sunanshi dan Shi'a shi ba zai bi dokar ba.
Har ma wasu akace sun dauka ma kansu wai za su ba wasu kariya, ya zama sun ki bi. Nace to wannan wauta ne. In ma har ba za ka bi doka ba, to ba zaka ki bi da sunan Shi'a ba. An fahimta ai? Ba Sunanka Shi'a ba. Sunanka wanda ya karya doka, na wawayen gari. Ba sunanka Shi'a bane.
Su wawayen da sukai doka tsabar wauta ne wannan! Ba doka tasa mutane suke hawa babur ba. Talauci ne da wahala, tilas ta sa su. Saboda haka ba doka za'ayi a hanasu ba, za'a samar musu da yanayi ne da ba zasu bukaci babur din ba.
Mene yasa mutane suke hawa babur a matsayin haya? Tilas ne. In da ainihin akwai wadata, da can ana hawa babur ne? Wa ya san ma za'a hau babur ai haya da shi? Saboda haka idan kuka samar da yanayi da ba za'a bukaci babur ba, ba za ma a ga babur ana haya da shi ba. Khalas ya kare.
Kuma sai suka zo suka ce, ba wai sun hana haya ne da babur ba, sun hana goyo ne. Wato ma'ana koda naka ne na kanka, zaka hau, ba zaka goya wani ba. To wannan ne ya kara rashin hikima. Har ma wai ance wani 'commissioner' yace wai ko matar mutum ne ko zai kai ta asibiti ne ba zai goya ba. Ma'ana ko zata mutu ne sai dai ta mutu.
Toh haba Mista 'Commissioner', kai yanzu a gari kasan tsofaffin Kwamishinoni masu garari a gari kasan yanzu guda dubu nawa ne? Kwanan nan zaka shiga garari a gari. Inda ake yin hukuma ma na gado na gidan sarauta ba sun kakkare ba? Ballantana Hukumar Nigeria kwana biyu babu.
Wato abin da ya kamata mutanen nan suyi ba shine suyi doka ba! Kamata ya yi su samar da yanayi, wanda ba za'a bukaci ya zuwa ga ayi haya da babur ba, sai ya zama ba'a haya da babur. Khalas! Amma doka bata da ma'ana!
Kuma zakuce na gaya muku, batun kwana biyu ne. in dai talaucin mutane yana nan, za su yi abin da yafi hawa babur. In dai talaucin yana nan. Dan a nan ma ba'a yin na keke, a wani wuri ana yin na keke, a goya mutum a keke sosai a matsayin haya. A wani wuri ana na Jaki, wani wuri ma ana na mutum ya ja. Amalanken mutum, duk ana yi. Da amalanken Jaki. To kamata ya yi suyi tunanin yanayi.
Amma abin da ni nake cewa shine; In mutum har bai bi dokar nan ba, ba sunan shi Shi'a ne ba. An fahimta ai. Ba sunanshi Shi'a bane, sunanshi wanda ya karya dokar Gwamnati. Ba sunan shi Shi'a bane.
Kuma ina fadin wannan ne domin akwai abin da naji da dama yake ta faruwa musamman a Kano inda dama dokar ta dade, cewa ainihin mutane sun gane cewa wai suna yin shiga ne irin wanda suke cewa na 'Yan Shi'a, ko su saka bakin kyalle.
Aka bani labarin wani ya zo da matarsa da nikabi, sai wani dan Sanda yace mishi, to ni dai ba zan saukar da kai ba, amma nasan in kaje gaba za'a hana ka wucewa. Saboda su wadanda suke wucewa bamu tsare su ba, ba irin wannan Hijabin suke yi ba. Kuma suna sa bakin kyalle a babur din. Sai yace ma matar kawo wannan nikabin, sai ya daura a babur din. Sai farr ya wuce shi Dan Shi'a ne.
To kuma aka ce nan ma anji wasu suna cewa, wai me 'yan Shi'a suke yi ne sai a bar su, su wuce? (Wannan kafin a hana goyo, amma ana hana wucewa 'Check point' da babur), sai su wuce abinsu da babur dinsu. Sai akace ai suna sa YA HUSAIN ne. Sai wasu 'yan Kungiya suka ce, an gama! A nemo musu YA HUSAINI din suma. Haka suka manna YA HUSAIN, su manna LABBAIKA YA RASULALLAH su je su wuce da babur dinsu, sai ace ah ai 'yan Shi'a ne.
To har ma aka bani labarin wani yazo sun tsai da shi sun ce sauka (wannan a Kano akai wannan), sai yaga wani yazo ya wuce basu tsai da shi ba, kuma yace ya ganshi biji-biji, daga gani Makanike ne, amma ya zo ya wuce. Sai yace me yasa aka kyale wancan? Yace ai kai irin shigarka ba irin nasu bane, kai kana da gajeren wando, Shi ko wancan kaga bakin kaya yasa. Alhali yace ko da gani Makanike ne. Biji biji amma sai kawai yazo ya wuce abinshi, ya sa bakin kaya.
To Shi'a ba shine bakin kaya ba! Ko bakin kyalle ba! Ko wuce 'check point' da babur ba! Ba shine Shi'a ba, Shi'a I'itikadi ne, goyon bayan A'immatu Ahlulbaiti ne, da halin kirki. Yauwa! Kar ya zama yanzu kowane shima ya nemi wani kyalle ya rika wucewa furr, sai shi Shi'a.
Kamar yadda aka yi yayin da aka yi mana na su hotuna da su jan hula, yazo ya kwaranye. Sunyi yayin lokacin manna hotuna suyi ta wucewa ba'a ce musu komai, sukai ta wannan. Har ma wasu direbobin 'yan'uwa suka zo suka same ni suka ce abin yana damunsu, kowane sai ya manna hoto. Sai nace ku rabu da su kwanan nan zasu bari.
Sai kuwa ilai kuwa ba'a dade ba, sai akai Waki'a, ana neman masu hotuna a bindige. Kowa ya cire hoton.
Saboda haka ma'anan, Shi'a I'itikadi ne da aikin kirki, ba bakin kyalle ne da wuce 'Check point' ba ko kuma goyo a babur ba. An fahimta ai?
Ina fadin wannan ne don, na'am nasan lokacin da muke zaman makoki, lokacin sunyi dokar cewa bayan tara (9pm) babu hawa babur. Kuma muna zaman makokin mu nan muna tashi wajen tara da rabi ne zuwa goma. Su mun nemi alfarmar su ne, cewa mu muna kaiwa wannan lokacin, za mu zo mu wuce wani lokaci guda. Kuma sun yarda.
Saboda haka lokacin mutanen mu sukan zo su wuce. Don haka ne ma akan ba da sanarwa a nan, in za su tafi subi gungu ne kar mutum ya tafi shi kadai. To saboda haka ta wannan kuma wasu sukan fake da wannan suma su jira in sunga 'yan'uwa zasu suma su bi su. To wannan za mu iya cewa babu damuwa mu muka nemi alfarma.
Ko lokacin da suka sa 'check point' din ba'a wucewa da babur, mukan wuce da 'escort' dinmu amma sun sani. Ba wai muna wucewa da unwanin wai sunan duk Shi'a yana wucewa bane. Ko ba'a lura ba?
Saboda haka, Janibi biyu;
Kada wani a kul yace shi Sunanshi Shi'a ne, saboda haka zai karya doka da sunan shi Shi'a ne. Domin ba shine ma'anar Shi'a ba.
Su kuma janibin su wanda sukai dokan na wauta, ku gane lallai kunyi tsabar wauta, domin ba doka ya kamata ku yi ba, kamata ya yi ku samar da yanayi, wanda mutane ba za su bukatu ga yin haya da babur ba. Kuma bai kamata kuce goyo ne mujarradin goyo ba za'a yi ba. Ya kamata ace haya ne ko?
Eh in mutum yana da babur dinsa zai kai matarsa asibiti to sai yayi yaya, ko zai dauki matarsa su tafi wani wuri sai yaya, da ya zama ya yi laifin meye? Ko zai dauki dansa ya kai shi makaranta, sai ya zama mene? Sunce goyo ne gaba daya ba za'ayi ba, ba ko kan gado dokar.
Ala ayyi halin, ya kamata su suyi la'akari da dokarsu. Amma in ma mutum ya karya dokan, sunansa mene? Me karya doka. Sunansa Shi'a? (A'a) Yauwa!
Wa sallallahu ala Muhammadin wa alihid-Dahireen.

1 comment: