An bude wannan shafi ne domin amfanar da al'umma kan al'amuran da suka shafi mu'amalar rayuwa ta addini.
Sunday, 25 May 2014
KA'IDOJIN FAHIMTAR ALKUR'ANI DA TAFSIRINSA
Ka'idojin Fahimtar Alkur'ani Da Tafsirinsa
A cikin abin da ya gabata, mun ambaci yadda tafar-kin Ahlulbaiti (a.s) da mazhabarsu suka tabbatar mana da cewa Littafin Allah madawwami ne, ba jirkitarwar da ta same shi, shi ne kuma kundin dokokin Ubangiji dawwa-mammu, shi ne tushen shari'a, shi ne ma'auni mai hukumci kan ingancin ruwayoyi da hadisai, shi ne kuma hujja wajen tabbatar da kuskure ko dacewar kowane abu. Hadisi ya zo daga Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa:
"Idan wani hadisi ya zo muku daga gare ni, ku gwada shi da Littafin Allah, abin da ya dace da shi ku karba, abin da ya saba masa kuwa ku yi jifa da shi [106] ".
Bayan tabbatar wannan da soke dukkan raunanan maganganu na barna, za mu gane cewa tafarkin musulun-ci na asali ya nuna wa musulmi da ma'abuta ilmi da sani hanyar fahimtar Alkur'ani da tafsirinsa da mu'amala da nassin Alkur'ani, ya kuma kayyade mana hanyar. Wannan batu na fahimtar Alkur'ani da tafsirinsa da kuma tawilinsa, batu ne mai tushe, wanda kubutar tunani a Musulunce da ingancin akida da shari'a da masaniyar Musulunci duk sun dogara a kansa ne. Domin duk wani karkata ko takaita ko takaitawa wajen fahimtar Alkur'ani da binciken taskar shari'a da akida da fitar da hukumce-hukumcensa da riskar iliminsa da dokokinsa na zamanta-kewar al'umma da na siyasa, tattalin arziki, tarbiyya, zartar da hukumci da dai sauransu, duk suna kai wa ga karkata da rarrabar musulmi, da kuma yin tawaye ga tsarin asalin addinin Musulunci da tsabtarsa.
Wajibi ne a farkon magana kan wannan batu mai tushe da muhimmanci, mu rarrabe tsakanin tafsiri da tawili.
Tafsiri dai a wajen malaman lugga, shi ne: "Gano ma'anar lafazi da kuma fito da ita[107]".
Tawili kuwa shi ne: "Mai da dayan ma'anoni biyu da lafazi ke iya dauka ya zuwa dacewa da zahirin al'amari [108]".
Ahmad Ridha ya ce: "Kalmar tafsiri an dauko ta ne daga kalmar "fassara" wacce aka ciro ta daga "assifru", shi ne kuwa fitarwa da bayyanarwa. Ana cewa "asfaras subhu" wato asubahi ya bayyana, ana kuma cewa "asfaratil mar'atu an wajhiha" wato mace ta fito da fuskarta, an yi amfani da kalmar "asfara" wajen fitowa.
Ko kuma ace kalmar tafsiri an dauko ta ne daga "fasara-yafsiru" kamar "daraba-yadribu" ko "nasara-yansuru" "fasara-yafsiru-fasran. Fasru tana nufin bayyana da fito da rufaffen abu. Mutum ya kan ce "fasartu" ga abu idan ya bayyana shi [109] ".
Shaikh Tabrisi (Allah Ya daukaki mukaminsa) ya fadi cikin gabatarwar tafsirinsa mai daraja wato Majma'ul Bayan fi Tafsiril Kur'an cewa:
"Tafsiri shi ne fito da manufar lafazi mai rikitarwa, tawili kuwa shi ne maidowa da dayan ma'anoni biyu da lafazi ke iya dauka, ya zuwa ga dacewa da zahiri. Tafsiri shi ne bayani".
Abul Abbas Mubarrid ya ce: "Tafsiri da tawili da ma'ana duk daya suke. An ce 'fasru' shi ne fitowa da rufaffe, tawili kuwa shi ne karshen abu da makomarsa, da abin da al'amarinsa yake komawa gare shi... [110]".
Hanyar Da Ake Bi Wajen Tafsirin Alkur'ani:
Yayin da tafsiri yake bayanin ma'anar kalmomin Alkur'ani da jumlolinsu da kuma fito da ma'anoni a sarari, sannan kuma sashen kalmomin Alkur'ani da jumlolinsa ana iya fassara su da tafsirin zahiri wanda mai yiyuwa ne ya kasance ya yi nisa da manufa ta hakika ga Alkur'ani, shi kuwa tawili shi ne aikin fito da ma'anar da ake nufi, hakan kuwa ta hanyar mayar da ma'anoni da ke ajiye cikin ayar - bayan jujjuya su tsakanin fuskoki biyu ko fiye[111] - ya zuwa ga makomarsa. Burin da muke so mu cimma a nan shi ne daidaiton tawili da tafsiri a matsayin sakamako. Shi ne kuwa fayyace ma'anonin Alkur'ani da bayanin abin da Allah Madaukakin Sarki Yake nufin bayaninsa ga bayinSa.
Duk wanda ya yi bitar littattafan tafsiri da tafarkin masu tafsiri, zai samu cewa akwai tazara mai fadi da ramuka masu hadari, wadanda sashin masu fassara suka fada, sai suka karkace daga manufar tafsiri domin hanyoyin tafsirin wadanda suka bi da bayanin tawilin da suka yi wa ayoyin Alkur'ani. Wani lokacin a samu sun dogara da raunanan ruwayoyi da aka sossoka, wani loton kuwa a samu sun bi son zuciya sai su tankwarar da Alkur'ani zuwa ra'ayoyin kungiyoyin da suke bi, da kuma son zuciyarsu kebantacciya. Sai ka ga suna kokarin sa ayoyin Alkur'ani su dace da abubuwan da suka auku a tarihi kuma danganta su ga wadansu daidai-kun mutanen da Alkur'anin ba su yake nufi ba. Kai sun ma nemi su sa ayoyin Alkur'ani su dace da girmama ra'ayoyinsu da karkatar su kebantattu.
Misalin karkata cikin tawili shi ne fuskartar da ayoyin Alkur'ani da sashen masu falsafa da ilimin kalami suka yi bayan sun riga sun yi imani da tunani da mazhabobin kalami da falsafa sannan suka tankwara ma'anonin ayoyin zuwa wadannan mazhabobin.
Misali kuma shi ne cewa akwai abin da sashen marubuta da masu tafsiri ke yi na fuskantar da ayoyin Alkur'ani domin su dace da nazarce-nazarcensu na ilimin kimiyya da tunaninsu na tattalin arziki da zamantakewa da siyasa wadanda marubuta da amsu nazari suka bijiro da su suka kuma yadu a zamanin wadannan masu fassara. Suna bin fadar masu nazarce-nazarcen nan ba tare da akwai wata dangantaka ta hakika ko dacewa ta gaskiya ba. Haka nan muke samun yadda ake murda ayoyi zuwa son zuciya, ko ka ga mai tafsiri ya yarda da wasu ra'ayoyi sannan daga baya ya karkata ayoyin Alkur'ani zuwa ra'ayoyi da halaye da dama, tun da can da kuma ma yanzu.
Hakika masu tafsiri da yawa sun fada cikin wannan kuskuren, kuma daga mazhabobi daban-daban, na Ahlussunna ne ko na Shi'a ko kuma waninsu. Bayan sun yi wannan kuskuren sai su dora kawo hujjoji da dalilai don kare wadannan ra'ayoyi nasu.
Idan muka koma ga tafarkin Musulunci na asali wajen tafsiri za mu ga cewa ya yi watsi da wannan tafarki da muka fadi a baya da kuma tabbatar da asasai ingantattu na tafsiri.
Don kuwa tafsiri kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fadi, kuma tafarkin Ahlulbaiti (a.s) da duk wanda ya bi tafarkinsu ba tare da karkata ba da malaman tafsiri masu lizimta, yana da asasai da ginshikansa wadanda suke shiryar da mai tafsiri da mai bincike zuwa dacewa mayalwaciya.
Bari mu kawo bayanin da ya zo daga Manzon Allah (s.a.w.a.) da Imamai Masu shiryarwa (a.s.) da malaman al'umma kan batun sanya ginshikai wadanda ba su da wata karkata, domin tafsiri da tabbatar da ma'aunai da kuma dokoki masu kiyaye wannan ilmi mai daraja, domin shi ilmi ya ba da gudummawarsa tare da cikakkiyar kula da kubuta daga karkatarwa. Kuma domin wannan ilmi ya wadatar da duniyar dan'Adamtaka da ma'anoni da tunani da fahimce-fahimcen da za a iya riska da kuma hukumce-hukumce, ba tare da wata tawaya ko kirdado ko jidali ko bin ra'ayi ko kuma tankwara tafsirin domin ya bi son zuciya ba.
Allama Dabrisi ya ambata cewa: "Ya inganta daga Annabi (s.a.w.a), ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) cewa: "Tafsirin Alkur'ani ba ya halatta sai da asari (wato hadisi) ingantacce da kuma nassi bayyananne[112]".
Lalle Ahlulbaiti (a.s) sun kasance suna bin wannan hanyar, suna kuma watsi da yi wa Alkur'ani tafsirin da ya yi nisa daga wadannan ginshikai guda biyu, wato:
1. Tafsirin Alkur'ani da Alkur'anin, wato wasu ayoyi su yi wa wasu tafsiri.
2. Tafsirin Alkur'ani da ruwayoyi da kuma hadisai ingantattu.
Don haka ne ya wajaba cewa dole tafsirin ya lizimci wadannan ginshikai biyu, cikakkiyar lizimta. Sannan kuma wajibi ne kada mu gafala kan cewa hankali yana da fagensa na asasi da ja-goranci wajen fahimtar Alkur'ani da tafsirin ma'anoninsa da fuskantar da zahirinsa, bisa sharadin cewa shi hankali zai lizimci iyakokin Littafin Allah da Sunnan Ma'aiki (s.a.w.a.), ba zai kuma sabawa tsarinsu ba. Hakika Manzo Mai girma ya ba wa hankali fage fitacce wajen tafsirin Alkur'ani, inda ya ce:
"Alkur'ani mai saukin korawa ne, mai fuskoki da yawa; to ku dauki fassarar da ta fi kyau[113]".
Har ila yau ya ce:
"Ku bayyana Alkur'ani kuma ku nemi kebantattun abubuwansa[114]".
Alkur'ani mai girma ya bayyana irin rawar da hankali zai taka cikin tafsiri, ya kuma yaba wa ma'abota hankula masu fitar da hukumce-hukumce daga Alkur'ani, yayin da yake cewa:
"Da masu istinbadinsa daga cikinsu sun san shi". (Surar Nisa'i, 4: 83)
Alkur'ani ya yi suka ga wadanda suka bar tunani da lurar hankali cikin ayoyin Alkur'ani mai girma, da gano ma'anoninsa da abubuwa da ya kunsa, da cewa:
"Shin ba su lura da Alkur'ani ne, ko kuwa da kemare ne bisa zukata" (Surar Muhammadu, 47:24)
Daga nan za mu san cewa a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) tafsiri yana dogara ne da asasai uku:
1. Tafsirin Alkur'ani da Alkur'ani.
2. Tafsirin Alkur'ani da Sunna.
3. Tafsirin Alkur'ani da hankali mai lizimtar Alkur'ani da Sunna.
Haka nan muke samun cewa tafsiri yana da asasai da dokoki, kuma abin da ya tafo na tafsirai wanda za a cewa ra'ayin mutum ya shige shi, ko kuwa an dauki wasu nazarce-nazarcen ilmi wadanda mai tafsirin ya yi zamani da su, ko ra'ayoyin falsafa da ilmin akida, ko abin da aka danganta shi da ruwayoyi raunana ko ma wadanda sanadinsu yashashshe ne, ko kuwa masu karo da ayoyin Alkur'anin da suke a sarari ko kuma sunna tabbatatta, ko kuwa tafsirin da mai tafsirin ya daidaita shi da ra'ayinsa da karkatarsa da kuma sauran irin wadannan, dukkansu ababan yarfarwa ne a tafarkin Ahlulbaiti (a.s) da kuma malamai da masu tafsiri wadanda suka bi shiriyarsu. Sau da yawa kuma ana samun cikin tafsiran musulmi, sunna da shi'a, ra'ayoyi da tafsirai wadanda ba su lizimci wannan hanyar ta Musulunci ba, wadanda kuma ba su bayyana ruhin Alkur'ani.
Don haka, ba wa irin wadannan tafsiran kima ba ya inganta, ba za mu kuma rike su mu yi aiki da su ba, sai dai wanda ya tabbatar wa kansa da ingancinsu.
Mai tafsiri kuwa ko wane ne shi, Alkur'ani hujja ce akansa, ba shi ne hujja a kansa ba. Kuma ba zai zamo hujja kan musulmi ba face da gwargwadon abin da ya dace da katari da abin da ya gano na hakika kawai.
Hakika hani ya zo daga wajen Imamai (a.s.) kan magana ba da wani ilimi ko hujja ba. An ruwaito Imam Bakir (a.s.) yana cewa:
"Abin da kuka san shi to ku fade shi, abin da kuwa ba ku sani ba to ku ce "Allah Shi Ya fi sani". Lalle mutum yana tuzgo aya daga Alkur'ani ya fadi cikin tuzgowar da ya yi, faduwar mai nisan fiye da tsakanin sama da kasa[115] ".
Imam Sadik (a.s.) ya ce:
"Ko wane abu ana komar da shi zuwa ga Littafin Allah da Sunna[116]".
106. Majma'ul Bayan na Dabrisi, Mukaddima, juzu'i na 1, shafi na 13.
107. Majma'ul Bahrain na Duraihi, kalmar fassara.
108. Majma'ul Bayan na Dabrisi, Mukaddima, juzu'i na 1, shafi na 13.
109. Ahmad Ridha cikin Mukaddimar Majma'ul Bayan, juzu'i na 1, shafi na 13.
110. Gabatarwar Majma'ul Bayan juzu'i na 1 shafi na 13.
111. Daga cikin misalin tawili, shi ne tawilin da ake yi wa wannan aya: "KujerarSa ta yalwaci sammai da kasa", anan ana yi wa kujera tawili da ilmi da mulki…da dai sauransu, ba wai kujera wacce ake zama a kanta ba kamar yadda aka sani.
112. Gabatarwar Majma'ul Bayan na Tabrisi, juzu'i na 1, shafi na 13.
113. Kamar na sama.
114. Kamar na sama.
115. Sahihul Kafi na Bahbudi, juzu'i na 1, shafi na 5.
116. Kamar na sama, shafi na 11.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment