FAHIMTAR RAYUWAR ADDININ MUSULUNCI
An bude wannan shafi ne domin amfanar da al'umma kan al'amuran da suka shafi mu'amalar rayuwa ta addini.
Saturday, 31 May 2014
MALAMI DA MALUNTA A KASAR HAUSA
1.0 Gabatarwa
A cikin wannan makala za mu yi bayani filla-filla a kan abin da ake nufi da malami, da rabe-raben aikin malami da kuma lakuba da ake kiran malami da su a kasar Hausa. Manufar wannan makala ita ce nuna muhimmanci da kuma martabar da malami yake da shi ko ita a da, da yanzu, da kuma nuna yadda canje-canje na zamani suka shafi matsayin malami da sana'ar malanta a kasar Hausa1.
2.0 Ma'anar Malami
Abin da muke nufi da malami a wannan makala shi ne masanin Alkur'ani Mai girma, da ilmin Furu'a, da shari'ar Musulunci, da na harshen Larabci. Almajiri kuwa, shi ne mai yawon neman ilmi ko sadaka2. A kasar Hausa malami shi ne wanda yake da ilmin addinin Musulunci kuma yake karantar da shi. In malami ne da ilmin addinin Musulunci amma ba ya karantarwa, ya kuma kama sana'a, ba a lissafa shi cikin sahun malamai. Haka nan kuma, in malami ya shagala da neman abin duniya, mutane ba su dubansa da mutunci domin za su dauka ya ci amanar ilmi ke nan. Wani lokaci akan lissafa shi cikin masu bidi'a.
3.0 Sunayen Malamai
A kasar Hausa akwai sunayen iri-iri da ake kiran malami da su. Akwai malamin sunna,3 da malamin bidi'a,4 da malamin tsibbu,5 da sarkin malamai, da malamin malamai, da shehun malami, da kuma waliyyin malami. Ga takaitaccen bayani a kan kowannensu.
3.1 Malamin Sunna:
Shi ne malamin da ke da ilmin addinin Musulunci gwargwado, kuma yana karantar da shi ga jama'a. bugu da kari, yana da takawa da natsuwa da tsentseni da gudun duniya na inna naha. Kuma ga shi ba shi da tsoron fadin gaskiya a kan komai da kowa. Haka kuma, bai damu da fushin wani ba a wajen fadin gaskiya. Ire-iren wadannan na da wuyar samuwa. Amma ana samunsu domin bayin Allah nagari ba su karewa.
3.2 Malamin Bidi'a
Shi ne wanda yake da ilmin addinin Musulunci, kuma yana karantar da shi ga mutane, amma yana da kwadayin abin da ke hannun mutane da kuma tsananin son dukiya a zuciyarsa.
3.3 Malamin Tsibbu
In malami ya shagala da ba maras lafiya magani ta hanyar amfani da ayoyin Alkur'ani Mai Girma, da yin layu, kuma yana bugun kasa don ya fada wa mutane alherin da za su samu ko cutar da za ta same su, to akan kira shi malamin tsibbu6.
3.4 Sarkin Malamai
A wasu wurare cikin kasar Hausa, in malamai na da yawa, sarkin garin yakan nada musu shugaba. Shugaban malamai a gari ko a kasa, shi ne sarkin malamai wanda yake ba dole ne ya zama ya fi dukkan malaman garin ilmi ba. A halin yanzu akwai sarkin malamai a Sakkwato.
3.5 Malamin Malamai
Idan malami ya shahara kwarai da gaske a kan ilmin addinin Musulunci, har wasu malamai da almajirai na zuwa daga nesa saboda neman ilmin a wurinsa, akan kira wannan malami da lakabin 'Malamin Malamai'. Hausawa sun sami wannan suna ne daga Larabawa da ke kiran wasu malamansu da lakabin “Shaykh al-shuyukhi”. Da “Al'allamat”, da faridu dahrihi”. Ana nufi da wadannan lakubba babban malami wanda babu na biyunsa a kasarsa ko a zamaninsa.
3.6 Shehun Malami
Shi ne malamin da ya yi zurfi a cikin ilmin Sufanci da darikun waliyyai magabata. Haka nan kuma, akan kira irin wannan malami da sunan “Malamin darika”. Wani lokaci in malami ya tsufa kwarai har ya ba shekara sittin baya, akan kira shi “Shehun Malami”7.
3.7 Waliyyi
Wani lokaci akan samu malami mai tsananin tsoron Allah da natsuwa da gudun duniya da yawan ibada da ilhami. Har ma in ya yi magana a kan wani abu da zai auku, sai abin ya auku yadda ya ba da labari. Malamai masu irin wadannan siffofi da muka zana, akan yada cewa su waliyyai ne. Abin da ake nufi da waliyyai, shi ne bayin Allah da Allah ke so, wadanda za su shiga Aljanna. Hausawa sun dauka cewa waliyyi yana da ikon nuna karama yadda ya so, kuma a lokacin da ya so. Sun yi imani cewa, waliyyi na iya abin da sauran mutane ba za su iya yi ba, kamar tafiya a kan ruwa ba tare da jirgi ba, ko tafiya wuri mai nisa cikin lokaci kankane, ko kuma rayuwa wata da watanni ba tare da ci da sha ba. Da kuma makamantansu 8.
A kasar Hausa akwai malamai da yawa wadanda suka shahara da walitaka. Mutane da yawa sun dauke su waliyyan Allah ne wadanda za su shiga Aljanna kai-tsaye, ba tare da wahala ba. Daga cikinsu akwai Wali Danmarina,9 da Wali Danmasani,10 da Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo11. Haka nan kuma akwai karamomin iri-iri da aka danganta ga kowannensu.
3.8 Malamin Allo
Malamin da ke karantar da yara Alkur'ani Mai Girma da allo, shi ne ake kira 'Malamin allo'. Sau da yawa malamin allo almajiri ne. Bayan yara sun tashi daga makarantarsa, yakan tafi wajen babban malami wanda ya fi shi sani don daukar ilmi.
3.9 Malamin Zaure 12
Akan kira malamin allo 'Malamin zaure' in ya kasance yana karantar da yara karatun Alkur'ani da allo, kuma yana karantar da manyan littattafai kamar su Lahalari da Ishmawi da Izziyya da Risala.
3.10 Alaramma
Wannan shi ne lakabin malami da ke da sanin Alkur'ani sosai. Asalin kalmar Larabci ce (Allahu Yarhamu ka). Ma'anarta, 'Allah shi rahamshe ka'. Kafin a kira malami alaramma, sai ya haddace Alkur'ani Mai Girma, kuma yana iya rubuta shi da ka, hakanan kuma yana iya bayanin tsari da rabe-raben surorin Alkur'ani da ka.
3.11 Malamin Gafaka
Wannan shi ne malami wanda yake yawo da almajiransa daga wani wuri zuwa wani wuri. Ba shi da sana'ar neman abinci ban da karantar da yara Alkur'ani Mai Girma. Ya dogara ne a kan sadakar da mutane kan ba shi da kuma hidima da almajiransa ke yi masa.
3.12 Ustazu 13
Yanzu Hausawa kan kira mutum 'Ustazu' in sun ga alama cewa yana yin shiga irin ta malamai, kuma yana da ra'ayin rikau game da sha'anin addini, ko da kuwa ba shi da isasshen ilmin Addinin Musulunci. Haka kuma akan kira mutum Ustazu in malami ne shi, amma ba ya son darika, kuma ba ruwansa da ilmin Sufanci. Wani lokaci akan kira irin wannan malami 'Malamin Izala'.
4.0 Aikin Malami
4.1 Karantarwa
Babban aikin malami a kasar Hausa shi ne karantar da mutane addinin Musulunci, Alhakinsa ne ya karantar da mutane Alkur'ani Mai Girma, da Furu'a, da dukkan abin da ya shafi Shari'a. Karantarwa ce ke sa wani lokaci malami ya shahara. Sai sunansa ya kai wurare da dama, kuma almajirai su yi ta zuwa wajensa daga kusa da nesa domin neman ilmi da albarka a wajensa.14
4.2 Wa'azi 15
Wa'azi shi ne kiran mutane zuwa hanyar Allah. Manufar wa'azi shi ne shiryar da mutane yadda ake ibada da zaman lafiya tare da jama'a. Mai wa'azi yakan yi bayanin yadda ake Alwala, da Sallah, da Azumi, da Zakka, da aikin Hajji. Malami mai wa'azi yakan yi albishir ga masu saurarensa. Yakan yi musu albishir da shiga Aljanna in aka yi aikin kwarai a nan duniya. Haka kuma yakan yi gargadi a kan wutar lahira da azabarta wadda Allah Ya tanada wa Fir'auna, da Karuna, da Hamana, da wadanda suka yi aikin assha irin nasu.
A majalisar wa'azi, malami yakan gamu da wautar mutane daban-daban. Wasu sukan halarci wurin wa'azi saboda su kure malamin da tambaya. Wasu kuma sukan zo domin sukan halayen malami mai wa'azi don mutane su watse daga wurin wa'azinsa.16 Wani lokaci akan sami wasu mutane da ke surutu da izgili lokacin da ake wa'azi. Su ba su sauraron wa'azin da ake yi, kuma ba su barin masu saurare su ji abin da ake fadi. Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo ya gamu da ire-iren wadannan abubuwa da muka zana yayin da yake wa'azi a kasar Hausa a cikin karni na goma sha tara na Miladiyya17.
4.3 Talifi
Burin malami shi ne dalibansa su gane abin da yake koya musu. In malami ya gane dalibansa na fama da rashin gane wani littafi saboda tsaurinsa, sai malamin ya yi wa dalibansa sharhi ko bayanin littafin a rubuce don saukin fahimta18.
Saboda haka ne Shehu Usmanu da mukarrabansa suka yi talifi da yawa a kan fannonin addinin Musulunci daban-daban ga jama'ar Musulmi don su gane addini cikin sauki. Kuma ya yi kira ga malaman kowane zamani su yi talifi ga jama'arsu saboda su suka fi sanin matsalolin zamaninsu da na mutanensu19.
Shehu Usmanu ya nuna misali da yin talifi fiye da dari. Haka nan kuma kaninsa Malam Abdullahi Ibn Fodiyo, da kuma dansa Sarkin Musulmi, Muhammadu Bello 20.
4.4 Alkalanci
Babu wanda ya cancanta ya zama alkali sai malami mai tsoron Allah, kuma adali. A kasar Hausa, in aka ga malami yana da takawa da ilmin Shari'a mai zurfi, ga shi kuma adali, akan nada shi alkali. Kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka kasar Hausa 21, mafi yawan sarakunanta malamai ne. Kuma su ne ke alkalanci ga jama'arsu. In aiki ya yi wa sarki yawa ne yake nada wani malami alkali. Zuwan Turawa kasar Hausa ya sa alkalai cikin halin kaka-nika-yi. In sun yanke hukunci a bisa Shari'ar Musulunci, sai Bature ko dan korensa ya soke in ya ga dama. Wannan ya sa yanzu malamai masu tsoron Allah suna guje wa aikin Shari'a. Abin ya kai ga lahaula, har jahilai ne ma ake nadawa alkalai a wasu kotuna yanzu.
4.5 Limanci
Limancin Sallah yana daya daga cikin muhimman ayyukan malami. A kasar Hausa akwai limamai biyu “Limamin Khamsu Salawatu” (Salloli Biyar), da kuma “Limamin Masallacin Jumu'a”. Na farko suna da yawa. Kusan akwai su a kowace unguwa. Na biyu kuwa, sarkin gari, ko hakimi, ko mai unguwa tare da yardar wasu malamai ne ke nada shi. Har ila yau, malami ne ke limancin sallar gawa, da ta Idi, da ta rokon ruwa da ta husufin rana da wata.
4.6 Shawara
Malami mai basira shi ne sarki ke neman shawararsa in yana da matsala. Shi ne kuma babban abokin shawara ga sarki. Saboda haka, a cikin majalisar sarakunan kasar Hausa, akan sami akalla malami guda wanda zai dinga ba da shawara ga sarki a kan al'amuran yau da kullum, da kuma wadanda suka shafi addinin Musulunci.
Wani lokaci akan kira malamai masu ba sarki shawara da “Malaman Fada”. Amma su malaman sun fi son a kira su da sarautar da sarki ya fi ba malamai; wadda ita ce: Waziri, da danmasani, da Sarkin Malamai, da dai makamantansu.
4.7 Rabon Gado
Rabon gado wani babi ne mai wuyar sani a cikin ilmin Furu'a. Amma ga malami mai zurfin sani, abu ne mai sauki. Saboda haka, in magada suka rasa sanin yadda za su raba dukiyar gado a tsakaninsu, sukan nufi malam don ya ilmantar da su a kai, kuma ya raba musu dukiyar gadon, ko kuma a kai wurin alkali.
4.8 Daurin Aure Da Radin Suna Da Saukar Alkuri'ani
In za a daura aure, akan gayyaci malamai su albarkaci taron, da kulla auren, da kuma yin addu'a. Galibi, malamai kan yi wa waliyyansu nasiha a kan hakkokin ma'aura. Kuma sukan roki Allah Ya albarkaci zamansu na aure, da zuriya mai albarka, da 'ya'ya managarta, da kuma yalwar arziki da zaman lafiya. Haka kuma suke yi in an gayyace su wurin radin suna.
4.9 Biyan Bukata
A kasar Hausa, mutane da yawa sun dauka cewa malami yana da tsarkin zuciya da imani fiye da sauran mutane. Saboda haka, sun yi imani Allah ya fi sauraron rokonsa fiye da na wani.
In Allah Ya ba malami ijaba, sai ka ga attajirai, da saraki, da talakawa, da masu sana'o'i iri-iri maza da mata na ta tururuwa zuwa gidansa saboda neman biyan bukata. Wasu tsari suke nema da zai kare su daga sharrin bil'adama da sauran halittun Ubangiji. Matan aure kan so malam ya rokar musu Allah Ya ba su zuriya mai albarka in ba su da da, ko kuma kada Allah Ya ba mazansu ikon yi musu kishiya. Sarakuna sukan nemi addu'ar malami, Allah Ya kare su da jama'arsu daga sharrin abokan gabansu, ya kuma ba su lafiya da zaman lafiya da damina mai albarka. Attajiri yakan je wajen malami don neman tsari da karin arziki. A takaice dai, ba jinsin mutane da ba su zuwa wajen malami saboda wata bukata.
5.0 Matsayin Malami A Yau
A yau an samu sauyi sosai game da aikace-aikacen malami a kasar Hausa. Saboda huldar al'ummar Hausawa da Turawan Mulkin Mallaka da wasu kabilu daban-daban a cikin kasarsu da wajenta. Matsayin malami ya bambanta da yadda aka sani da can karni biyu da suka wuce.
A halin yanzu, an fara samun malamai a kasar Hausa masu ba da taimako ga 'yan fashi da barayi, da 'yan daudu da karuwai. Haka nan kuma, yanzu ana samun malamai masu zaman bauta ga masu hannu-da-shuni. Sai mai hali ya gina katon gida da masallaci da makaranta da gidan yara. Sai ya sa malami a gidan yara yana ciyar da shi da iyalansa. Shi kuma malamin yana karantar da yaran mai gida da matansa ilmin addini, kuma yana ba da sallah a cikin masallacin gida. In mai gidan mai hali ne sosai, sai ya biya wa malamin kujerar Hajji. Amma abin ban haushi shi ne, ranar da malamin ya yi wa mai gidan laifi, sai mai gidan ya kore shi daga gidansa korar kare.
6.0 Kammalawa
A cikin wannan makala mun yi bayani a kan malami a kasar Hausa. Mun tattauna abubuwa da yawa a kan sunayensa, da aikace-aikacensa, da kuma matsayinsa a cikin jama'a a da, da kuma yanzu. Babu shakka, wanda ya yi tsokaci a kan abubuwan da muka fada, zai gane cewa, ba karamin matsayi ne malami yake a cikin al'ummar Hausawa ba. Saboda muhimmancinsa, an dauke shi kamar gishiri ne ga miya. Da shi jama'a ke zama salihai. In kuma sun lalace (Allah Ya kiyaye). Jama'a sun shiga uku. Abin farin ciki kuma shi ne ba ga mutane kawai malami ke da daraja ba. Malamai masu aiki da ilminsu na da daraja a wajen Mahaliccinsu Allah har ma ya ce: “Masu tsoron Allah cikin bayanisa, su ne malamai”22. A wajen Manzo Allah ma, malamai masu daraja ne har ma ya ce game da su: “Malamai su ne magadan Annabawa”23. A kasar Hausa kuwa, in an kira sarki, sai a kira limaminsa.
Ina fata malamanmu za su ci gaba da yi mana jagora zuwa ga tafarkin tsira. Allah ya sa, amin.
TUSHEN BAYANI
1. Ka dubi The Hausa Factor in West Afircan History Mahadi Adamu, Ahmadu Bello University Pres Zaira, 1978, saboda karin bayani a kan kasar Hausa da iyakarta.
2. Ka karanta: Islam in Nigeria A.R Doi, saboda karin bayani a kan yaduwar Musulunci a kasar Hausa, shafi na 307-333.
3. Ma'anar kalmar “Sunna” na da yawa. Ka dubi littafin da ake kira Al-Sunnat Wa Ma'anatuha Fil Islam, na likita Mustafa Alsiba'i, shafi na 45-74.
4. Ka karanta rabe-raben bidi'a a cikin Ihya'u Sunna na Shehu Usmanu Danfodiyo, shafi na 22-28, bugu na Misra wanda Sardauna Sir. Ahmadu Bello ya dauki nauyin bugawa, 1963 a Misra.
5. Asalin kalmar “Tsibbu” daga Larabci ne “Tibbu” (magani).
6. Wani lokaci akan kira malamin tsibbu, “Gobe-da-nisa” in yana ba da maganin kisan mutum.
7. Dubi kamus da ake kira, Al-Munjid Fil Lugati Wal A’lami, bugu na 21, wanda aka yi a Lebanon a 1973, shafi na 41.
8. Ka dubi Lamma Balagtu” na Shehu Usmanu Danfodiyo, za ka ga irin karamomi da Allah Ya ba shi a shafi na 14-17. bugu na madaba'ar Amiriya da ke kano.
9. Akwai labarin tarihin wali Danmarina a cikin littafin Ibrahim Yaro Yahaya Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa NNPC Zaria, 1988, shafi na 36.
10. Ka dubi Hausa A Rubuce, shafi na 37.
11. Ka dubi Hausa A Rubuce, shafi na 49.
12. Ka dubi makalar Mahmud Inuwa mai take “Malaman Zaure: A Legacy of Western Colonial Education System In Northern Nigeria”, Shafi na 13.
13. Akwai ma'anarsa ta asali a cikin “Munjid”, shafi na 10. Shehun malami mai zurfin ilmi ne ake nufi da shi, kamar su Shehu Abdullahi Danfodiyo dai malam Jibirilu dan Umar, malamin Shehu Usmanu Danfodiyo.
14. Dubi tarihin Shehu Usmanu Danfodiyo wanda Ibrahim Imam ya rubuta.
15. Domin karin bayani ka dubi Nasiha Da Wa'azi A Cikin Musulunci, tailfin Habib Alhassan.
16. Domin karin bayani ka dubi Infakul Maisuri, wanda Muhammadu Bello ya rubuta, shafi na 91-94.
17. Ka dubi Infakul Maisuri wanda Alhaji Dan'ige ya dauki nauyin bugawa, shafi na 91.
18. Shehu Usmanu ya yi wa jama'a nasiha da su yi karatun littafinsa da na sauran malamai. Ka dubi karshen littafinsa da ake kira Najmul Ikhwani.
19. Ka dubi Najmul Ikhwani, shafi na 43.
20. In kana neman sunayen littattafansa ka dubi makalar Bashir Osman Ahmad, mai take Al-Ishamul Fikri Li Ulama'i Sakkwato.
21. Saboda karin bayani ka dubi Islamic Law in Nigeria na Sayyid Khalid Rashed, lagos, Islamic Publications Bureau, 1986, shafi na 75-80.
ZIKIRIN DARIKAR TIJJANIYA
ZIKIRIN DARIKAR TIJJANIYA
Abin da ya zama Lazim a Darikar Tijjaniyya Guda uku ne:
1) Wurudin Safe da Yamma.
2) Sai Wazifa a Wunin ko da Dare.
3) Sai Zikirin Juma'a.
To mene ne Wurudin?
Wurudin kashi uku ne:
1) Itigfari 100
2) Salatul-fatih 100
3) Hailala 100
To mene ne Wazifa?
Wazifz abubuwa Hudu ne suka hada Wazifa:
1) Istigfari 30
2) Salatul-fati 50
3) Hailala 100
4) Jauharatul-kamali 12
Gawanda ya Haddace ta kuma ya zaune a gida ba matafiyi ba ko wanda yake kan Dabba ko abin hawa, to sai ya karanta Salatul-fatih 20 kawai ta wadatar banta Jauharatil-kamalin.
Abin da ya zama Lazim a Darikar Tijjaniyya Guda uku ne:
1) Wurudin Safe da Yamma.
2) Sai Wazifa a Wunin ko da Dare.
3) Sai Zikirin Juma'a.
To mene ne Wurudin?
Wurudin kashi uku ne:
1) Itigfari 100
2) Salatul-fatih 100
3) Hailala 100
To mene ne Wazifa?
Wazifz abubuwa Hudu ne suka hada Wazifa:
1) Istigfari 30
2) Salatul-fati 50
3) Hailala 100
4) Jauharatul-kamali 12
Gawanda ya Haddace ta kuma ya zaune a gida ba matafiyi ba ko wanda yake kan Dabba ko abin hawa, to sai ya karanta Salatul-fatih 20 kawai ta wadatar banta Jauharatil-kamalin.
ZIKIRIN DARIKAR TIJJANIYA
ZIKIRIN DARIKAR TIJJANIYA
Abin da ya zama Lazim a Darikar Tijjaniyya Guda uku ne:
1) Wurudin Safe da Yamma.
2) Sai Wazifa a Wunin ko da Dare.
3) Sai Zikirin Juma'a.
To mene ne Wurudin?
Wurudin kashi uku ne:
1) Itigfari 100
2) Salatul-fatih 100
3) Hailala 100
To mene ne Wazifa?
Wazifz abubuwa Hudu ne suka hada Wazifa:
1) Istigfari 30
2) Salatul-fati 50
3) Hailala 100
4) Jauharatul-kamali 12
Gawanda ya Haddace ta kuma ya zaune a gida ba matafiyi ba ko wanda yake kan Dabba ko abin hawa, to sai ya karanta Salatul-fatih 20 kawai ta wadatar banta Jauharatil-kamalin.
Abin da ya zama Lazim a Darikar Tijjaniyya Guda uku ne:
1) Wurudin Safe da Yamma.
2) Sai Wazifa a Wunin ko da Dare.
3) Sai Zikirin Juma'a.
To mene ne Wurudin?
Wurudin kashi uku ne:
1) Itigfari 100
2) Salatul-fatih 100
3) Hailala 100
To mene ne Wazifa?
Wazifz abubuwa Hudu ne suka hada Wazifa:
1) Istigfari 30
2) Salatul-fati 50
3) Hailala 100
4) Jauharatul-kamali 12
Gawanda ya Haddace ta kuma ya zaune a gida ba matafiyi ba ko wanda yake kan Dabba ko abin hawa, to sai ya karanta Salatul-fatih 20 kawai ta wadatar banta Jauharatil-kamalin.
FALALAR DARIKAR TIJJANIYA
Hadisi Na Ishirin Da Uku
An kar’bo daga Malik, Harisu d’an Asimu Al-sh’ari (Allah ya yarda da shi) yace, “Manzon Allah (tsira d aminci su tabbata Agare Shi) Yace, “Tsarki rabin imani ne, kuma Alhamdulillahi ta kan cika mizani. Kuma Subhaanallahi Walhamdulillahi) Su kan cika ma’auni, ko su cika abindake tsakanin Sama da ‘kasa.
Kuma Sallah Annuri ce;
kuma Sadaqa Dalilice, Hakuri kuma haskene, kuma Alqur’ani Hujja ce Agareka ko akanka.
Dukkan Mutane suna Jijjijifi, wani ya sayarda kansa, wani ya fanshi kansa, wani ya hallaka kansa.”
[Muslim ne Ya Ruwaitoshi]
Hadisi Na Ashirin Da Hud’u
An kar’bo daga Abi Zarrin Al-Gifariyu (Allah ya kara yarda Agareshi) Daga Annabi (Tsira da aminci su kara tabbata Agare Shi) cikin irin Abinda Yake rawaitowa daga Allah, Cewa Allah yace, “Yaku bayina, ha’ki’ka na haramtawa kaina zalunci kima Na Haramta shi Agareku, to kada kuyi zalunci.
Yaa Ku Bayina, dukkanku ‘batattu ne, saidai wanda Na Shiryar.
To ku nemi Shiryata in Shiryar daku.
Yaa ku Bayina dukkanku mayunwata ne, Sai wanda na ciyarm to, ku nemi Ciwayarwata in ciyardaku.
Yaa ku Bayina dukkanku huntaye ne saiwanda Na Tufatar. To ku nemi tufatarwata in tufarta ku.
Yaa ku Bayina ha’ki’ka kuna yin laifi dare da Rana. Ni kuma ina gafarta zunubai baki d’aya, to, ku nemi Gafarata in Gafarta maku.
Yaa ku Bayina Bazaku iya cutar dani ba, Balle ku cuceni.
Kuma baku isa Amfanata Ba, Balle ku Amfane Ni.
Yaa ku Bayina, tundaga farkonku har izuwa na ‘KashanKu.
Da Mutanenku, da Aljaninku, za suyi dai dai da Zuciyar mafi ashararancinku, wannan Bazai rage komi daga Mulki Naba.
Yaa Ku BayiNa da dai tundaga Na Farkonku har izuwa na ‘Karshanku, da mutanen ku da Aljaninku, zaku taru awuri guda, sannan kowannan d’aya ya Rokeni ni kuma in ba kowanne d’aya bukatarsa, wannan Bazai rage komi daga Abinda Na Mallaka Ba.
Sai kamar yadda Allura zata rage in antsoma ta cikin kogi.
Yaa ku Bayina, aiyukankune kurum Nake ‘Kidaya Maku, sannan in Baku Ladansu, To, Wanda duk ya sami Alheri Sai ya godewa Allah. Wanda Kuwa ya sami wanin haka, to, kada ya zargi kowa sai kansa.”
Allahu Akbar. Allah ka bamu dacewa duniya da Lakhira, ameen don Darajar Abba-l Qaasim Sallallahu Alaihi Wa’aalihi Wasahabihi Wa’azwaajihi Wassallam.
Annabin Allah tsira da aminci su ‘kara tabbata Agare Shi Da IyalanSa, Mai Gaskyane Kuma Abin Gasgatawa!
TARIHIN SHEHU TIJJANI RTA DA SAHABBANSA
TARIHIN SHEHU TIJJANI RTA DA SAHABBANSA
Bismillarrahmanirrahim...Assalatu wassalamu alaika ya Rasulallah
Ya himmat sheikh Ihdirlee pee hazal mahdar...
Zamu gabatarda wani maqaala akan Shehu Tijjani RA da sahabbansa, bawai don mun isa ba. A'a don cika umurni ne
Magana akan akan mazajen darika da sufaye yana kara taraqqie da kusanci koda kuwa za'a mai maita maka abinda kasani ne.... Kalimatan waahidatan turaqqieka ilaa maqaamin lau abadtallah alpu sanaa.....(Magana daya akan bayin Allah zata iya kaika muqaminda koda ka shekara dubu ne kana Ibada bazaka samu wannan taraqqin ba
Allah yasa mudace
Lamarin Auliya'u ana jawo Imani ne akusa ajiye, don ilmi da bincike baisa ayarda dasu sai dai Imani kawai.
Don lamarin yana keta kwakwalwan maiji ko mai karantawa sai dai sami'ina wa ada'ana
Abune wanda yakeda asali amusulunci tun zamanin ma'aiki SAW ba wai saida aka fara karanta Darikaba
Duniya bata zama saida wadannan mazajen, dasu Allah yake kauda musiba, dasu Allah yake bamu ruwan sama, yakke yaye dukkan bala'oi, da za'a kaudasu to da duniya ta tashi gaba daya.
Wadannan mazaje su ake kirada Ahlul Deewan ko kuma Daa'iratu ahlul deewan..wa minhum Qudbul gausi, Autaad, Nuqbaa'u Nujba'u d sauraNsu wanda shehu Tijjani duk ya hade wadannan mazajen
Kuma ana bamu labarinsu Tun Zamanin shugaba SAW. An ANAS RA yace yaji daga wajen ma'aiki saw yace Albudla'u arba'ouna rajulan isnaani wa ishruona bil shaam wa samaniyati ashraa bil iraq...
Ma'aiki saw yace akwai Budla'u su arba'in ne 22 na sham, 18 na Iraq duk wanda ya mutu za'a dauko wani ya maye gurbinsa..idan lokaci yayi wato kiyama za'a janyesu gaba daya adoron kasa. Daganan duniya zata tashi
Munga ashe ba yanzu aka fara ba, kuma duk wanda yake raye arzikinsu yakeci, ya sani ko baisani ba
Wasu sunce akwai IMAMANi su 2, AUTADU 4, BUDLA'u 7, RAJIBIYYUN 30, ABDALU 40 NUJBA'U 70, NUQBA''U 300 AKHYARU 313 sai kuma sauran AULIYA'U
Wadannan duka duniya bata zama saidasu duk wanda ya rasu za'a dauko wani ya maye gurbinsa.
Allah yabamu albarkansu
Alaa ra'asuhum Qudbul Gaus
Kafin mu koro cikin sahabban shehu tijjani masu wadannan darajojin bari mu taba kadan daga tarihin shugaban waliyyan farko da karshe wato maulana shehu Ahmad tijjani RA
Anhaifi shehu a Ainu maad shekara ta. 1150 hijriyya, ma haifinsa ya sakashi makaranta ya hardace kur'ani yana shekara bakwai, sannan yashiga karatun fiqhu har yazama Bahru
Mahaifansa sun rasu rana guda saboda wata annoba da ake kira Daa'oon'
Wannan hasken Rabbaniyyin ita tasa mashi fita don yaje ya haduda mazaje yana da shekara 21.
Y fara isa wani gari da ake kira Abil samgoon, ansayama garin sunan wani waliyyine babba
Anan shehu ya fara samun FATHUL AKBAR iNda yahadu da shugaba SAW a zahiri ba'a barcici ba, ya laqqana masa darikan Tijjaniyya
Yace masa kai danane, kai dana ne na gaskiya, daga yau kabar duk wasu shaihananka, da darikokinsu, da Auradansu. Daga Yau NINE shaihunka nine murabbinka
Anan garin shehu Ya zauna shekara 17 duk duniya saida tabiyoshi nan
Anan yasamu Qudbaniyyatil uzmaa, nan yasamu siddiqiyyq da Fardaniyya da mafatihul kunuz.
Anan yasamu Khatmiyya. Da Qudbaaniyya shamilah
Khatmu.. Mukamine dake tsakanin Nubuwwa da Kudbaniyya. wasu kuma sunce saboda dashi aka cika zirin waliyyai don daga kansa babu wani waliyyi da zaisake zuwa da Darika
Shehu ya tambayi ma'aiki SAW ya rasulallah shin a waliyyai bayan ni waye yakeda mafi daukakan muqami?
Shugaba saw yace shehu Abdulkadir jailani, da ibnul Arabil hatimi
Shehu yace shin sun isonan wannan muqamin? Ma'aiki saw yace na'am Abdulkadir jailani da Ibnul arabi sun shigo, amma Imamu junaidu, Hasnul basari da Imamu Busree sun shigo sun samu kashi daya bisa goma na mukamin sai Tajalli ya rinjayesu basu karaso ba
Abdulkadir jailani ne da Ibnul Arabi suka shigo tsakiya amma suma basukai muntahal maqaam ba.
Wannan shine ma'anan Qudbul makhtoom
Shehu nacewa dukkanin abinda ya kwararo daga zatil aliyyati zai wucene zuwa haqiqatul muhammadiyyati, abinda ya fito daga haqiqatul muhammadiyyati zai wucene zuwa zawatil Anbiyaa, daga wajen anbiya kuwa zai kwararo zuwa zatina ne... Daga garenine ake rabawa dukkanin halittu madadi
Sun sani ko bsau sani ba
Shiyasa wani kudbi a darikan shazilliyya yake cewa. Shi bashaziline amma Allah yabuda masa ya gane wajen shehu Tijjani yake karban madadi
Kowani darika kake shehu Tijjani ke shayarda shehinka, bama kaiba.
Daga nan shehu yabar Abul samgoon zuwa Faas yanada shekara 63 shekarun kakansa SAW
A wannan shekaran aka haifi sheikh ummarul footee... A fouta toro
Ya shiga fass ranar laraba... Wafil muharrami gadaa gaus rashaad.. Halifatan anil muhaiminul majid..
Inji ibnul babal alawi.
A daren lahadine na. 12 gawatan muharram. Aka tabbatarda shehu shine khalifatullahi pee ardihi wa samaa'ihi
A watan safar kuma 18 gawata me kira ya kirashi zuwa filin arfa ya tafi tareda sahibinsa syd Aliyu harazimi, akayi abinda akayi acan
Daganan ne yazama kudbul makhtoom.. Saboda haka shehu ke cewa munada muqami wanda babu wanda yasanshi sai Allah, da zamu bude da manyan rijalai sun karyatamu, wasuma kafirtamu zasuyi
Daganan ya halifantarda syd Aliyu harazimi muqamul hidmati wato Qudbaniyya
Sayyidu aliyul harazimi shi yafara zama a wannan muqamin, dagashi sai syd Muhammad tunussee, ya kwana 7, kwana bakwai kawai yayi amma aka ganshi ya shiga gari yana ihu yana cewa bazan iya daukaba, bazan iya daukaba, ahaka harya mutu
Bayanshi sai babban namiji wato syd Aliyul Tamasini, dominshi saida ya shekara 30.
Bismillarrahmanirrahim...Assalatu wassalamu alaika ya Rasulallah
Ya himmat sheikh Ihdirlee pee hazal mahdar...
Zamu gabatarda wani maqaala akan Shehu Tijjani RA da sahabbansa, bawai don mun isa ba. A'a don cika umurni ne
Magana akan akan mazajen darika da sufaye yana kara taraqqie da kusanci koda kuwa za'a mai maita maka abinda kasani ne.... Kalimatan waahidatan turaqqieka ilaa maqaamin lau abadtallah alpu sanaa.....(Magana daya akan bayin Allah zata iya kaika muqaminda koda ka shekara dubu ne kana Ibada bazaka samu wannan taraqqin ba
Allah yasa mudace
Lamarin Auliya'u ana jawo Imani ne akusa ajiye, don ilmi da bincike baisa ayarda dasu sai dai Imani kawai.
Don lamarin yana keta kwakwalwan maiji ko mai karantawa sai dai sami'ina wa ada'ana
Abune wanda yakeda asali amusulunci tun zamanin ma'aiki SAW ba wai saida aka fara karanta Darikaba
Duniya bata zama saida wadannan mazajen, dasu Allah yake kauda musiba, dasu Allah yake bamu ruwan sama, yakke yaye dukkan bala'oi, da za'a kaudasu to da duniya ta tashi gaba daya.
Wadannan mazaje su ake kirada Ahlul Deewan ko kuma Daa'iratu ahlul deewan..wa minhum Qudbul gausi, Autaad, Nuqbaa'u Nujba'u d sauraNsu wanda shehu Tijjani duk ya hade wadannan mazajen
Kuma ana bamu labarinsu Tun Zamanin shugaba SAW. An ANAS RA yace yaji daga wajen ma'aiki saw yace Albudla'u arba'ouna rajulan isnaani wa ishruona bil shaam wa samaniyati ashraa bil iraq...
Ma'aiki saw yace akwai Budla'u su arba'in ne 22 na sham, 18 na Iraq duk wanda ya mutu za'a dauko wani ya maye gurbinsa..idan lokaci yayi wato kiyama za'a janyesu gaba daya adoron kasa. Daganan duniya zata tashi
Munga ashe ba yanzu aka fara ba, kuma duk wanda yake raye arzikinsu yakeci, ya sani ko baisani ba
Wasu sunce akwai IMAMANi su 2, AUTADU 4, BUDLA'u 7, RAJIBIYYUN 30, ABDALU 40 NUJBA'U 70, NUQBA''U 300 AKHYARU 313 sai kuma sauran AULIYA'U
Wadannan duka duniya bata zama saidasu duk wanda ya rasu za'a dauko wani ya maye gurbinsa.
Allah yabamu albarkansu
Alaa ra'asuhum Qudbul Gaus
Kafin mu koro cikin sahabban shehu tijjani masu wadannan darajojin bari mu taba kadan daga tarihin shugaban waliyyan farko da karshe wato maulana shehu Ahmad tijjani RA
Anhaifi shehu a Ainu maad shekara ta. 1150 hijriyya, ma haifinsa ya sakashi makaranta ya hardace kur'ani yana shekara bakwai, sannan yashiga karatun fiqhu har yazama Bahru
Mahaifansa sun rasu rana guda saboda wata annoba da ake kira Daa'oon'
Wannan hasken Rabbaniyyin ita tasa mashi fita don yaje ya haduda mazaje yana da shekara 21.
Y fara isa wani gari da ake kira Abil samgoon, ansayama garin sunan wani waliyyine babba
Anan shehu ya fara samun FATHUL AKBAR iNda yahadu da shugaba SAW a zahiri ba'a barcici ba, ya laqqana masa darikan Tijjaniyya
Yace masa kai danane, kai dana ne na gaskiya, daga yau kabar duk wasu shaihananka, da darikokinsu, da Auradansu. Daga Yau NINE shaihunka nine murabbinka
Anan garin shehu Ya zauna shekara 17 duk duniya saida tabiyoshi nan
Anan yasamu Qudbaniyyatil uzmaa, nan yasamu siddiqiyyq da Fardaniyya da mafatihul kunuz.
Anan yasamu Khatmiyya. Da Qudbaaniyya shamilah
Khatmu.. Mukamine dake tsakanin Nubuwwa da Kudbaniyya. wasu kuma sunce saboda dashi aka cika zirin waliyyai don daga kansa babu wani waliyyi da zaisake zuwa da Darika
Shehu ya tambayi ma'aiki SAW ya rasulallah shin a waliyyai bayan ni waye yakeda mafi daukakan muqami?
Shugaba saw yace shehu Abdulkadir jailani, da ibnul Arabil hatimi
Shehu yace shin sun isonan wannan muqamin? Ma'aiki saw yace na'am Abdulkadir jailani da Ibnul arabi sun shigo, amma Imamu junaidu, Hasnul basari da Imamu Busree sun shigo sun samu kashi daya bisa goma na mukamin sai Tajalli ya rinjayesu basu karaso ba
Abdulkadir jailani ne da Ibnul Arabi suka shigo tsakiya amma suma basukai muntahal maqaam ba.
Wannan shine ma'anan Qudbul makhtoom
Shehu nacewa dukkanin abinda ya kwararo daga zatil aliyyati zai wucene zuwa haqiqatul muhammadiyyati, abinda ya fito daga haqiqatul muhammadiyyati zai wucene zuwa zawatil Anbiyaa, daga wajen anbiya kuwa zai kwararo zuwa zatina ne... Daga garenine ake rabawa dukkanin halittu madadi
Sun sani ko bsau sani ba
Shiyasa wani kudbi a darikan shazilliyya yake cewa. Shi bashaziline amma Allah yabuda masa ya gane wajen shehu Tijjani yake karban madadi
Kowani darika kake shehu Tijjani ke shayarda shehinka, bama kaiba.
Daga nan shehu yabar Abul samgoon zuwa Faas yanada shekara 63 shekarun kakansa SAW
A wannan shekaran aka haifi sheikh ummarul footee... A fouta toro
Ya shiga fass ranar laraba... Wafil muharrami gadaa gaus rashaad.. Halifatan anil muhaiminul majid..
Inji ibnul babal alawi.
A daren lahadine na. 12 gawatan muharram. Aka tabbatarda shehu shine khalifatullahi pee ardihi wa samaa'ihi
A watan safar kuma 18 gawata me kira ya kirashi zuwa filin arfa ya tafi tareda sahibinsa syd Aliyu harazimi, akayi abinda akayi acan
Daganan ne yazama kudbul makhtoom.. Saboda haka shehu ke cewa munada muqami wanda babu wanda yasanshi sai Allah, da zamu bude da manyan rijalai sun karyatamu, wasuma kafirtamu zasuyi
Daganan ya halifantarda syd Aliyu harazimi muqamul hidmati wato Qudbaniyya
Sayyidu aliyul harazimi shi yafara zama a wannan muqamin, dagashi sai syd Muhammad tunussee, ya kwana 7, kwana bakwai kawai yayi amma aka ganshi ya shiga gari yana ihu yana cewa bazan iya daukaba, bazan iya daukaba, ahaka harya mutu
Bayanshi sai babban namiji wato syd Aliyul Tamasini, dominshi saida ya shekara 30.
TARIHIN HARKAR MUSULUNCI KARKASHIN SHEKH IBRAHIM ZAKZAKY
TARIHI
Harkar Musulunci karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky ta tsiro ne tun kafin cin nasarar juyin juya hali na kasar Iran, watau tun lokacin shi Sheikh din yana dan makaranta a jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria. Sai dai a hankali ne harkar ta rika daukan siffa yayin da su yan uwa na harkar suke kara yawa kuma suke kara samun tarbiyya da ilmi na addinin musulunci. Daga cikin irin ayyukan tarbiyya da harkar ta dauka akwai irin su karantarwa da ake kira Ta'alim,Ijtima, Daura,Ribat... | |||
| |||
TA'ALIM
Wannan wani dandali ne na karantarwa da ake yi mafi yawa a masallatai na unguwowi daban daban na garuruwan da yanuwa din suke. Akan sa rana guda ne ko biyu gwargwadon yadda zai zama daidai da zarafin su yan uwa din inda ake taruwa maza da mata tare da jagorancin wakilin wannan gari inda za'a karanta hadisai da ayoyi na tarbiyyar dabi'u da ruhi don kara samun kusanci da Allah tabaraka wa ta'ala. Baya ga wannan ta'alim na kowa da kowa kuma kawai wani na daban wanda mafi yawa ake yi tsakanin wasu zababbu daga cikin yan uwa don karantarwa ta musamman ta yadda su wadannan yan uwa sun kasance sun fi sauran fadin ilmi da fahimta da dai sauransu.
IJTIMAH
Wannan ma wani bangare ne na ayyukan da aka sa agaba a harkan domin ganin an inganta tarbiyyan yanuwa koda yake ita ijtimah ta kasance tun a farko-farkon kafuwan harkan inda ake taruwa a daya daga masallatan jummu'a na garuruwan Kano da Zaria domin gudanar da manyan ijtima'oi ko kuma masallatan jummu'a na garuruwa daban daban don gudanar da kananan ijtimao'i. Daga baya bayan da harakr ta kara bunkasa sai ya zamana wannan nauin tarbiyyar ba zai yiwu ba saboda dalilai masu yawa ciki har da yawan jama'a don haka sai aka koma yin "Daura" maimakon ijtimah.
DAURA
Kamar yadda muka ambata a sama "Daura" ce ta maye gurbin ijtimah bayan da matsayin ijtimah din ya zama ba mai yiwuwa ba. Yadda aka saba gudanar da wannan abu kuwa shine ta hanyar shirya jawabai na malamai tare da mauduai daban daban da suka shafi tunani watau kyautata fikra kyautata dabi'au gayaran ruhi da dai sauran su wanda ake yi da manufar budawa yanuwa hanyar gyaran kai na tsawon kimanin kwanaki kamar bakwai watau sati daya. Mafi yawa a karshen ko wacce daura akan rufe ne tare da jawabin jagoran harkan Mallam Ibrahim Zakzaky. Galibi wannan daura kan banbanta da Mu'tamar wanda ake gabatar da shi ta hanyar gayyatan sauran musulmi na gari kowa da kowa kuma galbi yakan fi yawan jama'a.
MU'TAMAR
Kamar yadda muka ambata wannan shima wata hanya ce ta haduwan yanuwa da kuma bayar da tarbiyya domin akan hadu ne a daya daga cikin dakunan taro na zamani ko daya daga cikin masallatai na gari don gudanar da shi. Inda ake gayyatar Malamai daga bangarori daban na kasar don gabatar da laccocin su akan mauduai daban daban don kyautata tarbiyyar juna. Shima a mafi yawan lokutta ana rufewa ne tare da jawabin jagoran harkar Mallam Ibrahim Zakzaky.
WA'AZOZIN RANAKUN JUMMA'A
Wa'azozin ranakun jummu'a na daya daga cikin manyan ayyukan wannan harkar inda ake samun haduwa da jama'ar musulmi a garuruwan daban daban don bijirar da matsaloli na duniya da kuma musamman ma abin da yake damun musulmi a wannan lokacin saboda samun karin haske kan abin da kuma shiray tunanin musulmi din don ingantacciyar mafihimta game da yanayi da kuma siyasar dake cikin irin wannan abu. Haka nan kuma ta wannan hanya ana samun yin magana kan al'amurran da suke bijirowa kamar irin su lokutan watannin azumi, Hajj, da dai sauran watanni na ibada na musulmi, don karin haske kan irin abin da suka doru akan al'ummar musulmi na farilla da mustahabbai.
Babu shakka a wasu masallatai da ya zamana ba zai yiwu a aiwatar da wannan abu kafin huduba ba ana samu ne a aiwatar bayan salla jumma'a kafin mutane su watse su nufi gidajen su.
BUKUKUWA DA RANAKUN JUYAYI.
Daga cikin abin da yanuwa suka sa a gaba akwai tunawa da ranakun farin ciki da kuma na bakin ciki watau bukukuwa da kuma juyayi na munasabobin ma'asumai da magabata don yin nazari kan rayuwarsu mai albarka da kuma daukan darasi a cikin rayuwar mu ta yau da kullum. Shima wannan wasu lokuta ana yin su ne ta hanyar wakilan wannan harka din a garuruwa daban daban ko kuam ta jagoran hakar Mallam Ibrahim Zakzaky. Cikin irin ranakun da ake gabatar bukukuwa don tunawa da su akwai kamar su ranar 17 ga watan Rabiul Awwal watau ranar haihuwar fiyayyen halitta Manzon Allah[SAWA], 15 ga watan Sha'aban watau daidai da ranar da aka haifi Sahibuzzaman Imam Mahdi[AS], ranar haihuwar sauran a'imma da dai sauran bayin Allah na gargaru. Ranakun juyayi sun hada da ranar wafatin Manzon Allah[SAWA], ranar shahadar Imam Hussain[AS] a Karbala... da dai sauransu.
MUZAHARORI
Muzaharori ko kuma jerin gwano na daya daga cikin hanyar da wannan harka ke bi saboda bayyana abu muhimmi daya shafi al'ummar musulmi kamar ranakun Qudus wanda akae gabatar da jerin gwano na gaba dayan kasar sannan kuma ko wanne gari su gabatar nasu na daban don nuna goyon baya ga al'ummar Palasdinawa da kuma yin tofin Allah ya tsine ga su haramtacciyar kasar Isra'ila kan irin ta'addancin da take tafkawa a yankin na Palasdin. Koda yake dai a mafi yawan lokaci ana kokarin gabatar da wannan muzahara ta ruwan sanyi amma lokuta da dama ana samun matsalar kawo hari daga bangaren yan sanada da jami'an tsaro.
| |||
TAKAITACCE TARIHIN SHEKH IBRAHIM EL-ZAKZAKY (H)
Takaitaccen tarihin rayuwar jagoran harkar musulunci a Nigeria Sheikh Ibrahim Zakzaky.
2008/5/29 10:17
Rana da wajen da aka haifi Sheikh:
An haifi Sheikh ne a ranar 5 ga watan Mayu shekara ta 1953[15 ga Sha'aban 1372 AH] a garin Zaria dake cikin jihar Kaduna a Tarayyar Nigeria, kuma sunan sa Zakzaky kalma ce dake nufin 'mutumin zazzau'.
Sheikh Ibrahim Zakzaky shine dan Yaqoub shi kuma dan Aliyu shi kuwa dan Tajuddin dan Imam Hussain. Shi Imam Hussain wani bawan Allah ne daya fito daga Mali yazo garin Sokoto a lokacin Mujaddadi Sheikh Usman dan Fodio[RA] ya zauna tare da shi a matsayin almajirin sa, ta haka nema a lokacin da Shehu Usman dan Fodio[RA] ya nada Mallam Musa a matsayin Amir na lardin zazzau sai ya hada shi da Imam Hussain a matsayin mai bashi shawara. Ta haka ne a hankali-a hankali auratayya ta rika shiga tsakanin iayalen su kuma suka zama yan uwan juna ta wannan tun a farkon karni na 19.
Mahaifin Sheikh Ibrahim Zakzaky ya rasu ne tun shekara ta 1972, sai dai mahaifiyar sa har yanzun tana nan raye, Sheikh shine na biyar a wajen mahaifin su.
Karatun sa:
Sheikh Ibrahim Zakzaky ya fara karatu ne tun yana yaro karami a makarantar koyon karatun Al-kurani mai girma a makarantun Allo na al'ada kamar yadda aka saba tare da surkawa da karatun ilmin addinin musulunci wajen manyan malamai na wancan lokacin har ya zuwa lokacin da ya kai shekaru goma sha shida inda ya fara haduwa da tsarin karatu na zamani a shekara ta 1979 inda ya fara karatu a makarantar horar da malaman Arabiyya dake Zaria. Sannan daga shekara ta 1971-1975 ya shiga makarantar koyon larabci ta Kano watau School for Arabic Studies[SAS] wadda aka gina tun 1934 a matsayin makarantar koyon aikin lauya. sannan kuma daga baya ita ce ta haifar da babbar jami'ar Bayero da aka sani a yanzu. Kusan baki dayan alkalin alkalan jihohin Arewa daga wannan makaranta suka sami horon su. Saboda irin yadda Sheikh Zakzaky yake da ra'ayin fadada ilmin sa kan wasu darussa da ba'a koyarwa a wannan makaranta yasa ya gwama karatun nasa na Grade II da wasu maddoji ba tare da yayi su a baya ba kamar sanin gwamnati [Government] da ilmin tattalin arziki[Economics] inda yayi jarabawar GCE a kansu. Daga bisani Sheikh yayi jarabawa ta gaba[Advanced level GCE] akan wadannan maddojin:Government, Economics,Hausa,da kuma Islamic Studies inda ya sami kyakyawan natija wadda ta bashi damar shiga jami'a kai tsaye a shekara ta 1976 zuwa 1979 inda ya fara karatun digirin farko [B. Sc] akan sanin tattalin arziki [Economics].
Sheikh yayi musharaka cikin kungiyar dalibai ta musulmi inda ya zama fitaccen mamba a cikin makaranta da kuma matsayin kasa baki daya inda a shekara ta 1978 ya zama babban sakataren kungiyar na kasa sannan kuma yayi zama mataimakin shugaban kungiyar bangaren harkokin kasashen waje a shekara ta 1979. Sheikh Zakzaky yana daya daga cikin wadanda suka jagoranci kare Shari'ah a lokacin da aka yi wani jerin gwano na nuna goyon baya ga Shari'ah a baki dayan kasar.
Sheikh Zakzaky bisa sha'awar da yake da ita na fadada karatun sa ya ci gaba da zuwa wajen malamai da suka hada da Malam Sani Abdulkadir, Malam Isa na Madaka, Malam Sani Na'ibi da kuma Malam Ibarhim Kakaki dukkanin su a birnin Zaria. Haka nan kuma a Kano Sheikh yayi karatu wajen Shawish Abdallah na Sagagi da Malam Nuhu limamin Yola.
Ayyukan sa:
Babban aikin da Sheikh Ibrahim Zakzaky ya sanya a gaba shine karatu da kuma yada ilmi tun yana matsayin dan makaranta har ya zuwa wannan lokacin. An mayar da koyarwan sa cikin yan littafai a harshen Hausa da Turanci wadanda aka watsa su a ko ina cikin kasar sannan da yawa daga cikin wa'azuzzukan sa a yanzu suna cikin CD na Computer da kaset-kaset na Recorder a ciki da wajen kasar. Dr. Iqbal Siddiqui ya taba siffanta Sheikh a matsayin "Kashin bayan harkar musulunci a Nigeria" Babban manufar harkar musulunci da Sheikh yakewa jagoranci shine wayar da kan musulmi abin daya doru a kansu a matsayin su na daidaiku da kuma al'umma.
Yanzun haka harkar musulunci tana da makarantu dake karkashin ta na Primary da kuma gaba da Primary sama da dari uku wadanda suke a garuruwa daban daban dake fadin kasar. Wadannan makarantu an yi musu suna da makarantun Fudiyya. Haka kuma akwai cibiyoyi da da wuraren bincike da dama a manyan garuruwa na kasar karkashin wannan harka. Harkar ta mallaki jaridar da tafi ko wacce a kasar shiga ko ina da harsheen Hausa wadda ake kira Al-mizan. Sheikh ya sami matsala da hukumomi cikin kaki ko fararen kaya wadanda suke ganin cewa irin salon wa'azin nasa yana barazana ga mulkin su. A lokacin General Sani Abacha an kama Sheikh ne da tuhumar yana wa'azin 'babu hukuma sai ta Allah'.
A halin da ake ciki dai yanzun haka harkar musulunci karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky ta cika shekaru 30 tana kira kan komowa karkashin tsari na musulunci.
Tsawon tsarewar da aka yiwa Sheikh:
Sheikh Ibrahim Zakzaky ya kwashe shekaru tara a tsare a kurkuku daban-daban na kasar, daga shekara ta 1981-1984 an daure shi a kurkukun Enugu sai kuma kurkukun neman bayanai da bincike na jami'an leken asiri na kasa dake Lagos[Intorregation center] a shekara ta 1984-1985 sai kuma Kiri-kiri a shekara ta 1985 kurkukun Port harcout daga 1987-1989 sannan daga 1996-1997 duk dai a can Port Harcout. Sai kuma kurkukun Kaduna a 1987 sannan daga 1997-1998.
Tafiye-Tafiyen sa:
Sheikh Zakzaky yayi tafiya zuwa kasashe kamar su Britaniya, Saudi Arabia, Iran, Lebanon, Afrika ta kudu, Amurka, da Rasha. Dukkanin wadannan tafiye-tafiye yayi sune ta hanyar gayyata don dalilai na addini ko halartan tarurrukan karawa juna ilmi.
Mata da yara:
Sheikh yana da mace daya da kuma yaya tara.
Subscribe to:
Posts (Atom)