Friday, 30 May 2014

MATSYIN JIKI


MATSAYIN JIKI

Jikin shi ne bangaren zahiri na rayuwar mutum kuma yawancin mutane suke fuskantarsa domin gyara shi da kyautata shi, kuma yake kunshe da bangarorin mariskai na zahiri kamar ji da gani. Jikin mutum yana da abubuwan da yake bukata na rayuwa domin ci gaba da samuwa, wadannan abubuwan idan babu su to karshensa ya zo ke nan. Yana bukatar abubuwa biyu na ciki da na waje, da kuma wani abu na uku da ya shafi rayuwarsa a matsayinsa na dan Adam.
Na ciki sun hada da ci, da sha, da magani domin waraka daga cututtuka, sai kuma abin da jiki yake furzarwa wadanda suke fita daga gareshi domin samun sauki kamar kashi, da bawali, da amai, da mani, ko wadi da mazi, da gumi ko zufa, da hawaye, da majina, da daudar kunne, da yawun baki.
Na waje kuwa sun hada da wanke dauda, da sanya tufafi kamar riga da wando, da takalmi da hula, da sanya abu mai kanshi kamar turare, da kayan ado kamar sarka da dan kunne, da awarwaro, da mai domin shafawa, da mai domin gyaran gashi, da jan farce. Kamar yadda yake bukatar wurin zama da inda zai samu rayuwa mai kyau da shakatawa, sannan ya samu wani abu da zai rage masa wahalar cirata daga wuri zuwa wani wurin kamar mota ko babur.
Amma a bangare na uku yana bukatar wasu abubuwa da suka shafi zaman tare na al’umma, da hukumar da yake karkashinta, idan mun duba irin wadannan abubuwan zamu ga suna cikin bayanai kamar haka:

Mutum yana bukatar wasu abubuwan saukaka rayuwa da yalwarta kamar wutar lantarki da ruwan famfo, da titi mai kyau, da amincin gari ta yadda babu wani wanda zai zo domin satar kayansa, ko dukansa ko kisansa, kuma yana bukatar kare duk wani abu da ya shafi jininsa, ko mutuncinsa, ko dukiyarsa. Amma sama da hakan akwai ‘yancin fadin ra’ayi da kare hakkinsa domin kada wani ya takura masa a wannan fage mai muhimmanci. Fadin ra’ayi yana kama da amai ko atisshawa ne da idan ba su fito ba to suna kumewa a cikin jiki, haka nan ra’ayi yakan zama ya kume a cikin tunani sai ya kasance wani bakin ciki da yake taruwa a cikin zuciya.
Akwai wani abu da yake bukatarsa wanda ya fi kowanne muhimmanci wanda shi ne akidarsa, kowane mutum yana bukatar inda zai rayu da imani da akidarsa, yana kare akidarsa da hujjojinsa na shari’a ko na hankali.
Idan mun duba sai mu ga kowane bangare sai da shari’a ta ba shi matsayi na musamman domin kamalar mutum. Don haka ne a nan zamu yi nuni da wasu daga ciki a dunkule, mai son duba bayanai masu fadi sai ya koma wa littattafan shari’a.
Idan mun duba bukatun jiki na ciki sai mu ga shari’a ta muhimmantar da su ta yadda ta hana ci ko shan wani abu da yake cutarwa ko lahantawa, da yawa ayoyin da suka yi bayani kan haka a cikin littafi mai tsarki na Kur’ani, wasu ayoyin sun yi nuni da cewa: “… kuma ba a sanya muku kunci a cikin addini ba...” [1], wasu kuwa sun yi nuni da cewa: “... kuma yana haramta musu mai muni -cutarwa- ...” [2]. A nan muna iya cewa hatta da abu mai sanya maye da aka haramta a shari’a yana komawa ga cutuwar mutum a hankalinsa ko jikinsa ne.
Sai shari’a ta haramta dukkan mai sanya maye da mai cutarwa domin ta kare tarbiyyar mutum ta jiki da ta rayinsa, da gujewa sanya masa kunci a cikin rayuwarsa, da kaucewa ransa ko jikinsa daga fadawa cikin wahala da halaka.

Dogaro da wannan maslahar ne shari’a ta sanya wajabcin yin magani ga wanda ba shi da lafiya domin ba ta halatta masa cutar da kansa ko wata gaba ta jikinsa ba, don haka ne ta hana sayar da wani bangare na jikinsa wanda zai kai shi ga cutar da ransa ko jikin, sai dai idan babu cutuwa a ciki kamar sayar da wani bangare na jininsa.
Sannan hikimar Allah ta sanya masa wasu dokokin da zai samu sauki a cikin jikinsa kamar furzar da majina ko miyau, ko amai, ko kuma fitar da dauda da dattin da ya taru a cikin jikinsa ta hanyar bawali da bayan gida, ko kuma fitar da maikon da yana iya daskarewa ta hanyar gumi da zufa. Da ba a sanya masa hanyoyin da zai samu sauki ba da ya halaka, da rayuwarsa ta kare, amma sai ya kasance an ba shi hanyoyin sararawa.
Sannan aka sanya masa hanyar sanyaya ransa da zuciyarsa ta hanyar yin kuka abin da yake ni’ima ce babba ga bayi da Allah ya yi musu. Kuma iyakacin bala’in da ya fada wa mutum da nauyinsa a kan zuciya ne ransa take bukatar fesar da shi ta hanyar yin kuka domin samun lumfasawa.

Ruwaya ta zo cewa: “Masu kuka mutum biyar ne...” [3]. Kuka wani abu ne da ake son yin sa domin wasu abubuwa da suka hada da tsoron Allah ga wanda ya tuna zunubansa, ko yayin wata musiba kamar mutuwa. Wasu mutane sun so hana kuka yayin mutuwa, sai dai wannan ya taso daga rashin fahimtar maganar manzon Allah ne da wani sahabi ya yi, sai Ai’sha matar Annabi (s.a.w) ta gyara masa cewa ba haka ake nufi ba, sai dai abin da aka hana a kukan mutuwa shi ne fadin abin da ya saba wa shari’a.
Wata hanyar samun lafiya da Allah ya sanya wa bayinsa ita ce hanyar fitar wasu abubuwa da shari’a ta sanya wanka saboda fitarsu, wadannan abubuwan sun hada da mani, da jinin haila da na haihuwa, da na istihala idan yana da yawa sosai. Akwai kuma wasu ruwa masu fita daga mutum da ba a sanya komai a kansa ba don sun fita, wadannan su ne mazi da wadi, kuma shari’a a bisa mahangar Ahlul-baiti (a.s) ta yi musu hukunci da tsarki.
Wasu kuwa an sanya yin tsarki ne saboda fitarsu wadannan abubuwan sun hada da bawali da gayadi, wadannan idan sun fita sai mutum ya yi tsarkinsu. Akwai kuma wasu halaye su ma da ake son wanda ya yi su ya yi alwala, wadannan abubuwan sun hada da yin bacci ko suma.

Amma abubuwan da suke daga wajen jiki sun hada da tsarkin daudar jiki, shari’a ta sanya tsarkake jiki daga dauda domin kada ya yi wari ya cutar da kanda da mutane. Wata ruwaya tana cewa da mu: “An gina addini a kan tsafta ne” [4], wata kuwa tana cewa: “Tsafta tana daga imani ce” [5]. Kazamin mutum ba ya samun kima da daraja a cikin mutane, mutane suna wulakanta wanda suka gani cikin kazanta komai kimarsa.
Akwai kuma kayan sawa da suka hada da riga da wando, da takalmi, da hula, da turare, da gashin mata, da sauran kayan ado kamar sarka da awarwaro da dan kunne, ko jan farce da sauransu. Shari’a dukkaninsu ba ta hana su ba, sai dai a tufafin mace ta wajabta mata rufe dukkan jikinta in banda fuska da tafuka.
Wadannan tufafin kowace al’umma tana da nata yanayin shiga, kuma dukkan shigar al’umma ba ta da wata matsala a shari’a matukar dai ba ta saba wa waccen doka da aka sanya wa mace ba. Al’adun Hausa mace tana iya sanya atamfa da dan kwali da zane, da mayafi, sai ta rufe duk jikinta da wannan, tana iya sanya wando ko ta hada zane da wando.
Muna iya ganin a wasu al’ummun namiji ne yake daura zane mace kuma wando, wannan yana nuna mana kowace al’umma tana da nata yanayin shiga, kuma babu wata shiga da musulunci ya hana sai dai kawai ga mace idan zai kai ga bayyanar da jikinta da ya hana.
Wasu jama’un namiji yakan iya sanya gajeren wando da ‘yar riga, mace kuwa ta sanya siket da riga. Musulunci bai hana su wannan shiga ba, sai dai mace idan zata yi siket ya ja har kasa ta yadda zai rufe dukkan kaurinta har kafarta babu wani haramci a kan hakan, kanta kuwa da jikinta ta sanya riga zuwa karshen hannunta, ta sanya kuma abin da zai rufe kanta.
Muhimmi a cikin tufafi shi ne kiyaye wancan ma’anuni da musulunci ya sanya, idan aka kiyaye wannan babu wani tufafin wata al’umma da ya fi na wata. Babu bambanci, babban tufafi da karami duka daya suke, babu bambanci tsakanin babbar riga da kot da wando a wurin shari’a wannan duk yana komawa ga tunanin al’adun mutane ne.
Muna iya ganin yadda hula take da muhimmanci a wata al’umma, a wasu al’ummu girman mutum yana kan hularsa ne, da zai je taro babu hula to da kimarsa ta fadi ke nan. Amma a wasu al’ummu hula ba ta da wata kima ta a zo a gani, wasu suna ganin cewa sanya hula da dare yana haifar da matsala a ganin mutum, wasu sun tabbatar da matsalar yawan rufe gashi kodayaushe.

Amma wasu al’ummu idan ba su sanya hula ba suna ganin kamar ba su kammala ba, kana iya ganin mutum yana rufe kansa da zafin rana, kansa yana ta yi masa kaikayi amma ba zai cire hular ba, mafi muni shi ne likita yana iya hana shi sanya hula amma don kada al’umma ta gan shi karamin mutum sai ya sanya, haka nan al’adu suke cutar da al’ummu daban-daban.
Musulunci yana son tufafi ne na takawa, don haka kowace irin shiga al’umma take da shi ba shi da muhimmanci a wurinsa, abu muhimmi a nazarinsa shi ne takawar mutum, mutumin da yake sanya gajeren wando da karamar riga yana mai jin tsoron Allah da kiyaye dokokinsa shi ne abin so wurin Allah, amma mutumin da ya sanya rawani da alkyabba, ga babbar riga da mota mai tsada ba shi da wata kima wurin Allah sai idan shi ma yana da takawa.
Wannan ne ya sanya ma’aunin Allah da yake kallon bayinsa da shi ya saba da ma’aunin da mutane suke kallo da shi. Ma'aunin Allah ya doru bisa ganin dukkan halittarsa a daidai a cikin al'adunsu matukar ba su saba wa dokokinsa, amma tsukakken tunanin mutane yana girmama dan Adam ta cikin al'adu da abin duniya ne.
Idan muka waiwayi kayan adon mata haka nan babu wani ado da musulunci ya hana mace kowane iri ne, sai dai bai halatta ta bayyanar da adonta ga wasu mazaje ba sai dai ga mata ko mutane da suke muharramai kamar 'yan'uwanta, babu wani dan kunne ko sarka, ko man shafawa, ko karin gashi, ko rina gashi, ko jagira, ko jan farce, da sauran kayan ado da addini ya hana mace.

Sai dai namiji yana da dabaibayi da shari'a ta yi masa na cewa bai halatta ya sanya zenare ko azurfa ba, ko alhariri bisa sabani, don haka mace tana iya sanya zinare amma namiji bai halatta ya sanya shi ba. Zai iya yiwu wata al'ummar ya kasance namiji yana yin kitso ko ya sanya dan kunne da sarka ko awarwaro don adon namiji, shi ma a nan musulunci ya hana namiji sanya sarkar zinare, wannan haramcin na zinare ga namiji ba shi da bambanci a cikin al'ummu.
Game da wurin zaman rayuwa kamar gida, ko kuma wani abin hawa kamar mota, babu wani wanda Allah ya yi wa haramcinsa kamar namiji ko mace, a irin wannan abubuwan shari'a ba ta hana komai ba sai idan na haram ne. Idan gida ya kasance na kwace, ko filin kwace, to sai shari'a ta haramta zama da yin salla a cikinsa, kamar yadda ta haramta hawa motar sata ko ta kwace.
Wasu masu daskararren tunani game da musulunci sai suka hana mace tuka mota bisa jahilci, irin wannan jahilci ana yin sa a wasu kasase abin takaici da sunan musulunci. Kamar yadda zamu ga wasu kasashen ko kungiyoyi, ko ma wasu masu bayar da fatawa bisa tsukakken tunaninsu sun takaita kaya da irin na al'adarsu suna masu daukar cewa shi kadai ne na musulunci.

Amma a bangare na uku mutum yana bukatar wasu abubuwan saukaka rayuwa da yalwarta da ya hau kan hukumar da yake rayuwa karkashinta ta samar masa da su, irin wadannan abubuwan sun hada da wutar lantarki da ruwan famfo, da titi mai kyau, da amincin gari ta yadda babu wani wanda zai zo domin satar kayansa, ko dukansa ko kisansa.
Aminci wani abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar dan Adam, idan babu shi to al’umma ba ta samun sukunin ci gaba. Don haka yana bukatar mai kare masa jininsa, da mutuncinsa, ko dukiyarsa. Kamar yadda yake matukar bukatar wanda zai kare masa ‘yancin fadin ra’ayinsa, da kare hakkinsa domin kada wani ya takura masa a wannan fage mai muhimmanci.
Sannan akwai wani abu da yake bukatarsa wanda ya fi kowanne muhimmanci wato ‘yancin akida, kowane mutum yana bukatar inda zai rayu da imani da akidarsa, yana kare akidarsa da hujjojinsa na shari’a ko na hankali. Kuma wannan akida wani abu ne da ya kafu a ransa, ya yi rassa a gabobinsa, don haka ne ba a tilasta mutum ya bar akidarsa, idan ana son gamsar da shi cewa akidarsa batacciya ce, to ya zama ta hanyar hankali ko hujjar shari'a.

1. Hajji: 78.
2. A'afar: 157.
3. Almajalisul Fakhira: Sayyid Sharafuddin; s 150.
4. Jami'us Sa'adati: Naraki; j 3, s 248.
5. Annizamus Siyasi fil Islam: Bakir Sharif; s 295.

ISMAR MA’ASUMAI


ISMAR MA’ASUMAI



An yi bayanin Isma da cewa; ita ce martaba ta koli ta jin tsoron Allah, ko kuma shi ne ganin girman Allah da daukakarsa, ko kuma da ma'anar sanin ilimi cikakke da sakamakon sabo, ko kuwa ludufin Allah (s.w.t) ne wanda yake kusantar da bawa zuwa ga bautarsa. Muhimmin lamari a nan shi ne me ma'abota ilimin sanin Allah suke ganin isma; shin daga Allah take, ko kuwa kokarin dan Adam ne?

A nan masu ilimin sanin Allah suke ganin cewa; daga Allah ne take, kuma shi ne yake ba bawansa da ya san zai kiyaye amanarsa wannan baiwa. Sharhu Aka’idus Saduk: 61.
Wannan kuwa yana nuna mana ke nan asalinta kyauta ce daga Allah, sai dai bawansa Allah yana iya yin amfani da ita don kiyaye umarnin Allah, kamar yadda yana da zabin kin kiyayewa, sai dai Allah yana bayar da ita ga wanda ya so, kuma ya san ba zai saba masa ba. Wannan kuwa yana nuna mana cewa a fili yake cewa; isma ba ta kawar da zabi ga dan Adam. Allah madaukaki ya halicci ma'asumai daga tabon haske, sannan sai ya shirya musu hankali da ruhi mai karfi, wanda da su ne zasu iya sanin abin da yake sirrin samammu, kuma ya yi musu ludufin karkata da sanin halittun sama da kasa, da badinin samammu, don haka sai rayukansu suka kasance karkashin ikon hankulansu. Allawami’ul Ilahiyya: 169. Sannan muna ganin karfafar wannan lamarin a cikin shari'a yayin da Allah ya yi nuni da cewa; ya tsarkake Ahlul Baiti (a.s) Ahzab: 33, kamar yadda ya nuna yadda ya kebanci wasu annabawa (a.s), Almizan: j 16, shafi: 45-48.
Sai dai wasu mutane suna ganin cewa; Idan dai Allah ya ba wa zababbun bayinsa isma ne, to ashe ke nan ba su cancanci yabo a kanta ba? kuma ba ta kasance abin alfahari da kamala garesu ba?

Idan dai isma ta kasance tana hana zababbun bayi yin sabo a matsayinta na kyautar Allah, to ashe ke nan ba zasu iya sabo ba koda kuwa sun so, kuma ke nan ba su cancanci yabo ko lada ba don sun bar sabo?
A nan muna iya cewa: Isma ba a bayar da ita sai ga mutumin da rayinsa ta kasance ta tsarkaka, kuma tana iya karbar wannan amanar ta kiyaye da ita, don haka ashe ke nan mai isma yana cancantar alfahari, kuma kamala ce gareshi. Kuma wannan tsarkakar ruhin da mai isma yake cancantar wannan baiwar ta Allah da ita, tana iya kasancewa kala biyu: Imma ta hanyar gado; kamar yadda 'ya'yan annabawa (a.s) suke gadon kamalar badini da ta zahiri daga iyayensu, domin a ilmance, da ruwayance ya tabbata cewa; kamalar iyaye tana da tasiri ga 'ya'yansu, don haka ne ma aka karfafi aure da na gari, don haka sai ka ga dan rago, ya taso rago, dan sadauki, ta taso sadauki, mai kaifin kwakwalwa da mai dadaddiyar basira, sai ka ga 'ya'yansu sun yo su.

Don haka muka ga Allah madaukaki yana yabon 'ya'yan annabawa (a.s) da wasiyyansu yana mai kiran su zuriya ce sashensu daga sashe. Aali Imaran: 33. Sai dai wannan ba shi kadai ba ne; domin yana bukatar tarbiyyantarwa, da koyarwa, da kuma halittar Allah da hikimarsa ga 'ya'yan annabawa da salihai na gari, don haka rayuwa a irin wadannan salihan gidaje, da kuma al'umma saliha, da abokai salihai, yana iya sanya tasowa cikin tarbiyya ta gari, sannan kuma sai ludufin Allah da kyautarsa da yake ba wa wanda ya so.
Don haka wani lokaci; kokarin da mutum yake yi nasa na kansa, da kuma al'ummar da ya taso, da yanayinta yana daga cikin abubuwan da suke haifar da salihancin bawa da kamalarsa. Idan Annabi (a.s) ko wani wasiyyin Annabi (a.s) ya yi kokari, ya samu kamalar da ta cancanta a samu wannan baiwa ta Allah (s.w.t), ya yaki ransa mai neman yin sabo, to babu wani abu da zai hana Allah ya yi masa wannan baiwa mai daraja.
Misalin Yusuf (a.s) da kissarsa da Zulaiha babban misali ne a nan; Yusuf: 23. Haka nan ma misalin gudun da Annabi Musa (a.s) ya yi daga mutanensa; Surar Kasas: 23-24, 15-20. Kuma akwai misalai masu yawa da suke nuni ga rayuwar samartakar annabawa (a.s) da kokarinsu tun suna kanana har zuwa girmansu. Wadannan abubuwan da wasu suna samuwa ta hanyar halitta, wasu kuwa ta hanyar zabin dan Adam duk suna taimakawa wurin samun wannan falalar ubangiji mai girma. Don haka idan Allah ya duba zukatan bayinsa da kokarinsu sai ya zabi mafifitansu ya yi musu ludufinsa a cikin bayinsa, ya kuma ba su aiki mai girma na isar da sakonsa, da kasancewarsu ma'auni na shiriyar dan Adam a cikin bayinsa.

Amma batun mai cewa: Idan dai isma ta kasance tana hana zababbun bayi yin sabo a matsayinta na kyautar Allah, to ashe ke nan ba zasu iya sabo ba koda kuwa sun so, kuma ke nan ba su cancanci yabo ko lada ba, don sun bar sabo?
Muna iya cewa; Isma ba ta cire musu zabi, kuma duk sa'adda suka so suna iya sabawa, kamar dai hankali ne da Allah ya yi wa bayinsa ludufi da shi, wanda suna iya sanin mummuna da kyakkyawa da shi. Masu hankula sun san cewa zalunci yana da daci, da zafi, kuma ba sa son a yi musu zalunci, amma kuma sai su zalunci wani, suna iya sanin cewa wani abu zai kai su ga cutuwa amma kuma su aikata shi, wannan kuwa yana nuni da cewa wannan ilimi da suke da shi bai hana su zabin kansu ba.
Haka nan ma lamarin annabawa (a.s) ilimin da aka ba su ba ya hana su zabin kansu, kuma ba ya cire musu ikon sabawa, sai dai su suna kokarin ganin ba su saba ba fiye da kowane mutum, kuma Allah madaukaki ya san haka garesu, don haka sai ya zabe su da wannan falalar tasa. Muna iya kawo misalai domin kusanto da tunani ne kawai, misalin wannan a fili yake a kasashe, ta yadda an san ministoci sun san maras kyau, amma ba kowa ake zaba ba sai wanda aka san ba zai ci amana ba a bisa ilimin zahiri, sai dai wannan ba ya hana shi cin amana idan ya so ya ci.

Da shugaba ya san wadanda ba zasu ci amana ba a bisa badini da hakika to da su zai kawo a matsayin ministocinsa, sai dai ilimin mutane takaitacce ne, don haka sai su dogara da zahiri. Amma Allah mahaliccin kowa ya san wanda zai kiyaye har a badini, don haka ba ya zabar mutum sai wanda ya san yana da kiyayewa a zahirinsa da badininsa, sannan sai ya zabe shi a matsayinsa jakadansa, kuma ya ba shi baiwa da falala da ilimi maras iyaka.
Da wannan ne zamu ga cewa a fili yake babu wata isma da take hana zabi ga ma'asumi, kuma babu ismar da take kara zube ba tare da sanin tsarkin ruhin zababbun bayi ma'asumai ba. Don haka sun cancanci a girgiza musu, kuma a yaba musu, da wannan ne ma muka ga Allah madaukaki a cikin ayoyin Kur’ani mai girma yana girmama su girmamawa! Yana nuna kimar ayyukansu sakamakon dagewarsu kan biyayya gareshi dagewa!.

Wednesday, 28 May 2014


Hakkin Jama'ar Kasa
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Amma hakkin jama'ar kasa da kake jagoranta shi ne ka sani cewa sun zama jama'arka ce saboda rauninsu da kuma karfinka, don haka wajibi ne ka yi adalci a cikinsu, ka zama garesu tamkar uba mai tausayi ne, ka yafe musu jahilcinsu, kada ka gaggauta musu da ukuba, kuma ka gode wa Allah a kan abin da ya ba ka na karfi kansu".
Adalci tsakanin al'umma ba tare da fifiko ba shi ne kashin bayan samun nasarar shugaba, wannan adalcin yana da ma'ana mai fadi don ya hada da adalci a siyasa, da tattalin arziki, da zamantakewa, da addini, da al'adu, da rayuwa, da tunani, da dukkan wani abu da yake kewaye da al'umma na hakkin jiki, ko ba najiki ba.
Al'umma tana da hakki a matsayinta na Daidaikun mutane da al'umma a dunkule, wacce take da hakkin jagoranta ya kare mata hakkin kare zahirin rayuwarta, da kuma hakkin kare mata badinin rayuwarta, ya auna kowannensu da ma'auni daya, ya tausasawa da tausayawa, ya kawar da tsoronsu, ya biya bukatunsu, ya karbi gaskiya da nasiha gunsu, idan ya ki to sai su koma gaya masa karya, domin ko an gaya masa gaskiya sai ya yi fushi da su.
Suna da hakkin ya kula da lafiyarsu, da tsaftar gari , da kula da tsarin birane da gidaje wadatattu, da kula da iliminsu, da kula da tsaronsu, da abubuwan more rayuwa, da kula da annashuwa da wasanninsu.

Imam Ali (a.s) ya ce da Ziyad dan Babansa, a lokacin da ya maye shi da Abdullahi dan Abbas a yankin Farisa da ayyukanta, a cikin wata magana mai tsayi tsakaninsu da ya hana shi game da dada haraji-: "Ka aiwatar da adalci, ka guji tsanantawa (ba tare da hakki ba), da yin zalunci, domin tsanantawa tana jawo kaurace wa wuri, zalunci kuwa yana kawo yaki ne" .
Sayyidi Ali dan Abi Dalib (a.s) yana rubatawa zuwa ga Muhammad dan Abubakar yayin da ya sanya shi gwamnan Misira, yana cewa: "Ka kaskantar da fukafukanka, ka tausasa bangarenka, ka sakar musu da fuska, ka daidaita su a bayar da lokaci da kallo, don kada masu girma su yi kwadayin zaluncinka gare su (talakawa), kuma kada raunana (talakawa da marasa galihu) su yanke kauna daga adalcinsu garesu .
Kuma Allah madaukaki zai tambaye ku zama da bayinsa game da karamin aiki da babba, da na zahiri da na boye, idan kuwa ya yi muku azaba, to ku ne kuka yi zalunci, idan kuwa ya yi afuwa to shi ne ya yi rangwame.
Ku sani ya ku bayin Allah cewa, masu jin tsoron Allah sun tafi da rabon duniya da ladan lahira, sai suka yi tarayya da ma'abota duniya cikin duniyarsu, amma 'yan duniya ba su yi tarayya da su ba cikin ladan lahirarsu ba, sai suka zauna duniya da mafi kyawun yadda aka zauna ta, suka ci ta da mafi kyawun yadda aka ci ta, sai suka rabauta da duniya kamar yadda masu holewa suka rabauta da ita, suka dauki abin da masu girman kai suka dauka daga gareta, sannna sai suka cirata daga gareta da guzuri isasshe, da kasuwanci mai riba, suka samu dadin gudun haram a duniyarsu, suka samu yakinin cewa su ne makotan Allah gobe a lahirarsu, babu wani nemansu da ake mayarwa, kuma babu wani jin dadinsu da ake ragewa.

Ya ku bayin Allah ku ji tsoron mutuwa da kusantarta, ku yi mata tanadi, domin tana zuwa lamari mai girma, da babbar magana, da alherin da babu sharri tare da shi har abada, da sharrin da babu alheri tare da shi har abada. Wane ne ya fi kowa kusanci da aljanna fiye da mai aiki cikinta! Waye kuma ya fi kowa kusanci da wuta fiye da mai yin aikinta! Ku sani ku abin farautar mutuwa ne, idan kun tsaya mata sai ta kama ku, idan kun guje mata sai ta cimma ku, ta inuwarku lizimtarku (zama tare da ku), ga mutuwa a kulle ta a makwankwadar kanku, duniya kuwa ana nade ta daga bayanku; (wato duk wani minti daya da kuka ba wa baya, sai a nade shi, ba zai sake dawo muku ba!)
Ku ji tsoron wuta da zurfinta mai nisa ne, zafinta mai tsanani ne, azabarta sabuwa ce, gida ne da babu rahama cikinsa, kuma ba a amsa wani kira a cikinta, kuma ba a yaye wani bakin ciki a cikinta.
Idan kuna son tsoronku da Allah ya tsananta, kuma zatonku gareshi ya kyautata, to ku hada tsakaninsu, domin mutum kyakkyawan zatonsa ga ugangijinsa yana kasancewa ne gwargwadon tsoronsa ga ubangijinsa, kuma mutanen da suka fi kowa kyautata zato ga Allah, su ne suka fi kowa jin tsoron Allah.
Ka sani ya kai Muhammad dan Abubakar cewa ni na sanya ka jagoran mafi girman jama'a a guna mutanen Misira, kai ya cancanta ka saba wa son ranka, kuma ka kare addininka, kuma ko da ba ka da komai sai awa daya ta rage maka. Kada ka fusata Allah da neman yardar wani mutum daga halittunsa, domin Allah yana cike gurbin waninsa, amma babu wani mai cike gurbin Allah.

Ka yi salla a lokacin da aka sanya mata, kada ka gaggauta lokacinta don wani abu, kuma kada ka jinkirta ta daga lokacinta saboda shagaltuwa da wani abu, kuma ka sani cewa kowane abu na aikinka yana bin sallarka ne.
Ka sani jagoran shiriya da jagoran bata ba daidai suke ba, haka ma masoyin Annabi da makiyin Annabi ba daya suke ba, kuma Annabi (s.a.w) ya gaya mini cewa: Ni ba na ji wa al'ummata tsoron mumini ko mushriki; amma mumini imaninsa zai hana shi (cutar da ita), amma mushriki Allah zai rinjaye shi da ikonsa, sai dai ni ina ji muku tsoron duk wani munafukin boye, masani a harshensa, yana fadin abin da kuka sani, yana aikata abin da kuke ki" .
Muna ganin wannan nasiha ga jagoran da aka nada wa Misira ta isa ga dukkan mai hankali, kuma mun kawo dukan wasikar ne saboda muhimmancinta bai kebanta da jagora ba kawai, domin duk abin da aka kawo a ciki ya shafi kowane mutum mai neman tsira gobe kiyama.

Don haka yana daga cikin hakkin wanda ake jagoranta -dan kasa- a samar masa da aminci, da kariya, da lafiya, da ilimi, da hakkin fadin ra'ayinsa, da hakkin zamantakewa, da na walwala, da dukkan abin da ya shafi ci gaban rayuwarsa ta Duniya da Lahira.
Shugaba ya sanya alaka mai karfi tsakanin ma'aikatansa masu hidima ga al'umma da ita al'ummar kanta; misali akan samu tazara tsakanin masu tsaro da al'ummar kasa!. Samun tazara mai yawa tsakanin masu tsaron kasa da al'umma, ta yadda al'umma ba ta ganinsu wani bangare nata. Wannan kuwa yana faruwa ne sakamakon karancin wayewa da masu tsaro ba sa ji ko kadan cewa suna aiki don al'ummarsu ne kamar suna aiki don shugaba ne.
Wannan mummunan kuskure ya sanya masu kare doka sai su yi zalunci babu tausayi, har ma takan kai ga lahantawa ko salwantar da rai, kuma ga karbar cin hanci da ya zama ruwan dare. Koda yake a ciki akwai mutane masu hankali da kula da aiki da son taimakon al'umma kuma ba sa karbar cin hanci, irinsu ne suke iya mutuwa wajan kare mutanensu, amma da yawa ba haka suke ba sai dai kokari wajan neman na aljihunsu kawai sun manta da manufarsu.

Wani lokaci kamar suna cike da jin haushin mutane ne, da sun kama mai laifi sai duka da azabtarwa, alhali shi mai laifi, mai kare doka ba shi da hakkin yi masa wani abu sai dai ya kai shi kotu ta yanke masa hukunci.
Ban taba sanin cewa al'umma tana da tazara mai yawa da 'yan doka ba sai ranar da na samu nawa rabon, har ma wani yana jinginamu da wata kasa kai ka ce su ba mutane ba ne. Wani daga cikinsu ya ce: Irin wannan ku rika guduwa tun da ku ba ma su laifi ba ne! Kai ka ce su makafi ne da ba sa ganin mai laifi!. A ofishinsu ne na ga wani ana ta dukansa wai ya yi taurin kai a shiga mota, ana buga kansa da kasa, shi kuwa yana ta la'antar duk wani uba ko uwa na dan sanda.
Kuma a nan ne na yi mamakin yadda wani tsararre yake la'antar uwar ma da ta haifi dan sanda, har ma ya ce: Babansa ya taba cewa da shi tun da ya rasa aiki ya yi aikin dan doka. Sai ya ce: Ai baba gwara ka tsine mini in san ni tsinanne ne da in yi wannan aiki. Ya kara da cewa: Wallahi in gawa ta kai dubu to shi zai iya gano ta dan sanda a ciki don fuskarsa ba ta cikawa da imani.

A lokacin ne na san cewa lallai akwai tazara mai yawa sosai tsakanin 'yan sanda da al'umma, amma ra'ayin mutane da yawa ya tafi a kan cewa: Zafin zalunci da take hakkin dan Adam shi ya jawo haka, ta yadda mai tsaron kasa yake ganin yana yi wa shugaba aiki ne ba al'ummarsa ba, kuma yana ganin hadafinsa shi ne ya huce haushinsa kan al'ummarsa, sai ya cire wa al'umma jin cewa shi daga cikinta yake.
Haka al'amarin yake game da soja, kamar yadda dan sanda yake da hakkin kare cikin kasa da samar da aminci, haka ya zama wajibi a kansa ya kare kasa daga waje kada wani ya kai farmaki kanta. Amma duk da haka sai al'umma ba ta jin su nata ne haka su ma ba sa jin al'umma ta su ce. Da za a yi rigima tsakanin wani dan kasa da soja, da zaran sojoji sun isa wurin ba sa tambaya, a wurinsu mai gaskiya shi ne mai kaki na soja.
Rashin ganin juna a matsayin abu daya ya shafi har matsayin auratayya, domin na sha jin soja (ladani ne) yana nasiha a masallacin Barikin Bukabu da yake Kano yana cewa: Me ya sa ba a zuwa daga gari a auri 'ya'yansu? Ko su ba kamar sauran mutane suke ba. Haka nan aka jahilci hakkin juna tsakanin mai tsaro da wanda ake tsaro har ya zama kamar al'umma daban-daban ce a cikin al'umma daya.

Duba ka ga me Imam Ali (a.s) yake cewa game da mai tsaron kasa: "Runduna: Ita ce kariyar al'umma da izinin Allah, kuma adon shugabanni, izzar Addini, hanyoyin aminci, al'ummar kasa ba ta tsayuwa daram sai da su" . A wani wurin yana cewa: "Ka sanya wa rundunarka jagora wanda ya fi su nutsuwa da biyayya ga Allah da Manzonsa a ganinka. Wanda ya fi sirri na gari (wato mai dabi'u masu kyau), wanda ya fi su hakuri, da ilimi, da sanin tafiyar da al'amuran al'umma, da rashin saurin fushi, kuma da karbar uzurin mutane. Mai tausayawa talakawa, maras bayar da dama ga masu karfi. Wanda takurawa ba ta harzuka shi, rauni (karayar zuci) ba ya dunkufar da shi . A cikin wannan akwai nuni da cewa: Cin hanci shi ne abin da yake kawo ba wa mai karfi dama ya taka doka. Kuma akwai nuni da cewa: Bin hakkin dan kasa wajibi ne a kan hukuma a ko'ina ne yake, al'amarin da ya yi karanci a kasashenmu ko ma ba a san da shi ba.

Yana daga cikin hakkin dan kasa a samar masa da wurin shakatawa da walwala da wuraren hutawa da na wasanni da shi da iyalinsa da yaransa. Wani abin takaici irin wadannan filayen da ake warewa unguwanni domin wasanni sau da yawa maciya amanar al'umma suka sayar da su al'umma tana gani, mafi ban haushi da muni shi ne mafi yawa ba su san ma cewa wannan hakkinsu ba ne.
Game da Arzikin Kasa kuwa; sau da yawan talakawa ba sa ganin suna da hakki a arzikin kasa sai 'yan kadan, al'amarin ya kai ga wasu masu tafiyar da al'amarin al'umma suna ganin hakan. Sau da yawa mai mulki ba ya kiyaye hakkin wanda yake mulka game da arziki da albarkatun kasa, idan kuwa ka ce zaka yi magana kan sauran kayan rayuwa sai dai ka mutu da bakin ciki.

Duba ka ga wutar lantarki, da ruwan famfo, da man fetur da kasar nan take ita ce ta biyar a duniya a yau. Kuma duba ka ga wasu kasashe da mun fi su karfin tattalin arziki amma ba su da wata matsalar irin wadannan abubuwan rayuwa, man fetur kuwa a wajensu kusan mafarki ne wani ya ce ya ga dogon layi ko babu, kuma a gidaje akwai wuyarin na wutar lantarki da fayef na famfo da na Gas, wannan kuwa duk sun yi shi ne cikin shekaru kadan.
Sannan mutanensu suna biyan kudi kankani ne domin duk talaka yana iya biyan kudin. Haka ma a gidaje akwai kayan sanyaya gida a lokacin zafi kuma da abin dumama daki lokacin sanyi, amma wadannan abubuwan a kasarmu a gun talaka wani kayan masu jin dadi ne.
Wani abin kunya da 'yan kasarmu suke sha a duniya shi ne; ga shi kasar a waje tana da kima saboda suna jin labarin tana da arziki, amma hatta da gasar kwallon kafar da aka yi a kasar sai ana yi ana dauke wuta.

Irin wannan al'amarin ya faru wata rana yayin da muka isa tashar jiragen sama ta Kano, ga fankokin kansu suna bayar da zafi ne amma duk wannan bai isa ba sai aka dauke wuta, wani mutum (ba dan Nijeriya ba ne) ina ji ya ce: Kai ka ga Air port sai ka ce kango. Haka nan ake tara wa 'yan kasar abin kunya a kasashen waje kai ka ce masu mulki ba sa zuwa wasu kasashe suna ganin abin da yake faruwa.
Idan kuwa ka waiwaya kotu abin ya yi muni sosai, amma akwai ma'auni na gane kotun zalunci da kotun adalci, Idan ka ga kotu mai kudi da sarki suna jin tsoronta to ana adalci ne kuma ana bin gaskiya ne, amma idan ka ga talaka kawai ne yake tsoron kotu to ka sani ana zalunci ne.
Wani lokaci akan ja shari'a da ya kamata a yanke ta a sati ko awowi kadan amma sai ta yi watanni da shekaru har ma mai hakki ya ce ya yafe, ko ya gaji ya bari don kansa.
Wani lokaci hakkin yana rutsawa da kudin marayu ne amma sai ka ga kotu ta ajiye a banki tana samun kudin ruwan, wani lokaci ma ba ya isa sai an diba daga hakkin maraya an sa a aljihu.

Wani lokaci kuma akan iya mirgide gaskiya ko jifa da hauka ga wani don wani ya kubuta, da haka ne hakkoki masu yawa na mutane suke salwanta.
Idan muka waiwayi garuruwa kuwa zamu ga Rashin kula da tsafta daga bangaren gwamnati da na al'umma yana daga cikin mummunan al'amari da ya addabi birane da kauyuka, ta yadda zaka ga duk ko'ina ana iya zuba shara . Ga mummunan tsarin da garuruwa suke fama da shi, sai a sayar da hanyoyi har da hanyar ruwa ta yadda damina da kwararar ruwa zasu wahalar da talaka, ga karancin manyan hanyoyi da matsattsun kananan lunguna .
Idan kuwa damina ta zo talakawa suna fargaba ne, ga miyagun lunguna da kududdufai marasa hanya, amma ba za a rushe gidaje a fadada hanyoyin ruwa da na motoci da yin kwatami don samar da magudanar ruwa ba.
Mafi girman abin takaici shi ne abin da na gani a Jami'ar Bayaro da na dade ban ga irinsa ba, sai na ga takardu a ko'ina a kasa, matattakala duk da tabo ta yi bakin kirin, muna tsaye muna hira sai wani ya watso ruwa daga sama duk ya kusa bata mu, idan kuwa ka wuce wasu wurare wari yana tashi.

Sai na fara tunanin Jam'iar Tehran da wuri ne kodayaushe kamar ka sanya abincinka a kasa ka ci, na rika tunanin cewa a yanzu da wani zai zo daga abokanmu daga Jami'ar ya ga wurin kwanan dalibai kawai da an ji kunya. Kuma da zaka tambaya a kan me aka gina imani? Daya daga mafi muhimmancinsu ita ce tsafta: Hatta ma wasu hukunce-hukuncen Allah yakan sanya su ne domin kai wa ga cimma samuwar tsafta a cikin al'umma.
Ba ma jami'a ba, a irin wadannan kasashe a cikin gari duk wani yanki a kowane dare yana da motoci na musamman wadanda da dare sukan wanke titinan yankin. Amma wani abin takaici a kasarmu ba ma kawai tsaftar gari ba, kana iya ganin yanki da miliyoyin mutane suke rayuwa ba tare da wani isasshen ruwan sha ba.
Sayar da hanyoyi don gini, sannan da za a rusa da su talakawan ne zasu tsine wa wanda ya rusa, alhalin shi wanda zai saya ya kamata ne ya fara zuwa ya ga taswirar gari, da kotu, da hukuma, domin ya tabbatar da ba hanya aka sayar masa ba, sai dai!.

KIMAR MUTUM


Kimai Mutum

Da sunan Allah madaukaki
Mutum halitta ce mai girma daga cikin halittun Allah madaukaki wanda ya girmama shi fiye da kowace halitta, sai dai wannan halitta mai girma da kima mai wuyar sha'ani yana iya kaiwa matakin da ya fi kowace halitta kamar mala'iku madaukaka, kamar yadda yana iya kaiwa mafi munin halitta da yake kasan darajar alade, kuma wannan lamari ya sanya mutum mai wuyar sha'ani, murdadde.
Daya daga cikin mafi girman ni'imar da Allah ya yi wa mutum ita ce bude masa hanyoyi biyu na kamala da na kaskanta. Madaukaki yana cewa: "Mu mun nuna masa tafarki ko ya kasance mai yawan godewa ko mai yawan kafircewa". (Insan: 3).
Da fadinsa: "Mun shiryar da shi tafarki biyu" (Balad: 10).

Domin mutum ya samu daukaka da kamalar dan'adamtaka yana bukatar ya samar da alaka uku ne wacce kowacce daga cikin tana da dokoki da hanyoyi da zai iya kyautatawa. Wadannan alakokin mafi muhimmanci da kima da daraja da girma ita ce alaka da mahalicci, sannan sai alaka da mutum, sai kuma alaka da sauran halittu. Sannan wadannan alakokin suna shiga cikin juna ne, ba su kasance hannun riga da junansu ba, don haka kyautata kowacce daga cikinsu tana da alaka da kyautata sauran. Idan mutum ya kyautata alakarsa da Allah madaukaki to yana nufin ya kyautata duka ukun ne. Sannan a wannan rubutun namu zamu karfafi bayani kan alakar mutum da dan'uwansa mutum ne.
Idan mun duba alakar mutum da dan'uwansa mutum zamu ga mutane sun kasu gida biyu; imma dai suna da kimanta jinsinsu na mutane ko suna kaskantar da su.
A ilmance an sanya wannan lamarin a matsayin ma'aunin gane mutum mai kima da daraja, domin idan mutum mai kima ne sai ya kimanta dan Adam domin kansa yake nunawa ta yadda kimarsa takan sanya shi jin sauran mutane suna da kima, amma idan kaskantacce ne sai ya yi tsammanin kowa ma haka yake. Kuma haka lamarin yakan juya ga wanda aka girmama idan mai kima da daraja ne sai ya girmama ka, amma idan mai kaskanci ne sai ya yi takama. Masu hikima suna cewa: "Idan ka girmama mai daraja sai ka mallake shi, idan kuwa ka girmama kaskantacce sai ya yi dagawa da girman kai" (Al'mu'utamaratus Salas: Husain Shakiri/ s 147).

Kamalar Annabi (s.a.w) da imamai magadansa masu daraja ce ta sanya mu gane cewa su ne masu mafi daukakar darajoji a cikin kowane fage na ilimi da sani, da kyautata alaka da mahaliccinsu da sauran bayi mutane, da kuma sauran halittu, fiye da kowane mahaluki. Duba abin da ya zo a littafin Risalatul Hukuk na Imam Zainul'abidin (a.s) (s; 7) yayin da wata baiwarsa take zuba masa ruwa yana yin alwala da buta, sai butar ta subuce ta fada fuskarsa ta ji masa ciwo, sai ya daga fuskarsa ya kalle ta. Sai ta ce masa: Allah madaukaki yana cewa: "Da masu hadiye fushi", sai ya ce: Na hadiye fushina. Sai ta ce: "Da masu yin afuwa". Sai ya ce: "Allah ya yi miki afuwa". Sai ta ce: "Allah yana son masu kyautatawa". Sai ya ce: Ke 'ya ce saboda Allah! (ya 'yanta ta).

Duba yadda wannan baiwa tasa ta rotse masa fuska amma sakamakon fasa wannan fuska mai daraja shi ne ma'abocin wannan fuska madaukakiya ya 'yanta wannan baiwa. Ina ne mutum zai iya samun irin wannan mu'amala, da wannan dabi'a mai tsananin yalwa da girmama in ba a irin wadannan cikakkun mutane masu daraja ba!.
Kamar yadda Ali bn Yusuf al-Hilli ya kawo a cikin littafin nan "Al'adadul Kawiyya/ s 155" game da wata ruwaya ta Sufyanus Sauri cewa ya shiga wurin Imam Sadik (a.s) sai ya gan shi duk launinsa ya canja, sai ya tambaye shi game da hakan, sai ya ce: "Na kasance na hana mutanen gidana hawa saman daki ne, na shiga gida sai ga wata baiwata wacce take renon wasu yarana ta hau saman tsani ga yaro tare da ita, da ta gan ni, sai ta tsorata ta dimauce, sai yaron ya fado kasa ya mutu. Sam launina bai canja ba saboda mutuwar yaron, sai dai launina ya canja ne saboda firgicin da ta samu saboda ta gan ni, sannan sai ya ce mata: Ke 'ya ce saboda Allah, babu komai kan ki -ya fada mata haka har sau biyu-.
Idan ka duba wadannan masu daraja da yadda suka san ubangijinsu sai wannan ya sanya su sanin dan Adam da sauran halittu, sai suka kasance babu wani abu na cutarwa da yake iya faruwa daga garesu zuwa ga wani halitta, maimakon haka sai dai ma su samu cutuwa kuma su yafe. Don haka sai suka kasance rahama ga dukkan talikai, fitilar haskakawa domin gane gaskiya daga bata, tudun tsira. Kuma manzon rahama (s.a.w) ya siffanta su da cewa su ne tudun tsira yayin da yake kamanta su da jirgin Annabi Nuhu (a.s), da kofar tubar Banu Isra'il.

A yanzu ne zamu gane cewa; domin kowane mutum ya kasance rahama ga talikai dole ne ya kasance ya san ubangijinsa, ya kiyaye kansa, da wannan ne zai kasance haske mai haskakawa duniya, fitilar da take kona kanta domin wasu su samu haske.
Yanzu zaka kwatanta wadannan masana Allah (s.w.t) da kaskantattun bayinsa wadanda ba su san komai ba sai kawukansu, ba su san Allah ba. Sannan ga cututtukan rayi sun cika su, idan kana neman mai girman kai da jiji-dakai ka same su, to ka kai magaryar tukewa. Su suna dagawa saboda kawai sun ga sun isa "Lallai mutum yana dagawa, saboda kawai yana ganin kansa ya wadatu"(Alaki: ).
Wasu mutanen babu wanda ya tsira daga sharrinsu, sannan na kasa da su yana gigicewa saboda halayensu, sannan mafi yawan al'amuran al'umma suna hannun irinsu a cikin kasashe. Akwai misalin wani ambasadan Nijeriya a wata kasa (a 2003-2007) wanda kamar yadda bai san kimar kasarsa da al'ummarsa ba. Rashin mutuncinsa ya mamaye hatta da gidansa ta yadda matarsa ta yi mummunan abin da zai ba ka mamaki ta kori mai yi mata hidimar shara da wanke-wanke domin kawai ta fasa mata tangaran, alhalin santsinsa ne ya sanya kubucewarsa daga hannunta.

Duba nisan da yake tsakanin irin wadannan mutane biyu, tsakanin kamilin mutum masanin Allah cikakken sani wanda yake jin zafin tsoratar da baiwarsa ta yi alhalin ta kashe masa da, amma ba wannan ne tunanin da yake damusa ba, sai tunanin tsoron da ya same ta sakamakon laifin da ta yi, kuma wannan ya sanya shi 'yanta ta. Da kuma mutumin da ya dulmiye cikin kogin son duniya da tsananin jahiltar Allah madaukaki, da kallon bayi a matsayin abin biyan bukatarsa kawai ta yadda wannan kungurmin jahilin mutum wanda ya narke kan son duniya da ganin girmanta, da jahiltar Ubangijinsa da kuma rashin sanin kansa, ya dauki tangaran dinsa ya fi dan Adam kima, ta yadda duk wani wulakanci yana iya yi masa saboda tangaran dinsa!.
Wani abin da ya fi wannan rashin imani shi ne na wani mutum maras mutunci da ya taba kade wani yaro ya mutu sai iyayen yaron suka yafe, shi wannan mutumin ba ma dan Nijeriya ba ne. Amma da yake mutumin ba shi da kimar mutuntaka da dan adamtaka tare da shi ko kwarzane, sai ya rika yi musu dariya bayan ya tafi da shi da abokansa 'yan kasarsa, yana mai cewa; ya dauka zai biya diyya ne, ashe wadannan mutanen wawaye ne, yanzu sun bar masa diyyar kyauta kenan!.

Wannan mutumin ya cika maras kima, kuma ya kai matukar makurar kaskanci, yayin da ya dauki alherin da wasu suka yi masa abin da yi wa dariya da isgili!. Lallai maganar masu hikima ta gaskata yayin da suke cewa: Idan ka girmama mai karimci sai ka mallake shi, amma idan ka girmama kaskantacce sai ya yi dagawa. Domin babu wani mai fahimtar alheri sai ma'abocin alheri, amma kaskantaccen mutum wanda bai san alheri ba, idan ka yi masa alheri sai ya yi dagawa, ko ya ga wani wayo ne ya ba shi hakan. Misalin Karuna babbban misali ne a wannan fage yayin da yake cewa: "Ai duk sanina (dubarata) ne suka ba ni wannan dukiya..." (Kasas: 78).
Idan mutum ya daukaka yana da matukar girma da daraja, amma idan ya fita daga kimar nau'insa, sai ya koma mafi kaskantar halittun duniya. A ilimin Mantik ana yin bayanin cewa; mutum shi ne mai rai mai hankali, sai ga mutum a yau ya komai mai rai mai farautar dan'uwansa mutum. Ba zaka ji komai ba a duniya sai kisa, da fashi, da yaudara, da zambo, da gaba, da kiyayya, da fushi, da rashin zaman lafiya, da rashin tsaro, da talauci, da cututtuka, da makamantansu. A Jiya ne ma wani yake bugo mini waya cewa; Ai 'yan fashi sun tare hanyar su Tsohon Gwamna Abubakar Rimi, sai ya samu bugawar zuciya sai ya mutu kafin a karasa asibiti!.
Kuma haka nan kissar take ga dubunnai da miliyoyin mutanen da suke rayuwa a duniya, a kullum firgici, da tsoro sai sun yi kisa bisa dalilai iri-iri. Kamar yadda a kullum Allah ne kawai ya san yawan matan da ake zubarwa mutucinsu ta hanyoyi mabambanta mafi muninsu shi ne fade!.

Wannan kuwa ita ce makomar dan Adam matukar ya yi nisa da sakon Allah, a koda yaushe dan Adam ya yi nisa daga tafarkin haske, to zai zurfafa cikin duhun faganniya kenan.
Don me ya sanya mutum ba zai yi tunanin meye matsalar ba! Don me ba zai koma cikin hankalinsa ya yi tunani ba?! Shin muna tsammanin haka Allah madaukaki yake son duniya ta kasance ne?! Shin muna tsammanin cewa Allah bai yi duniya don rahama ba, ya yi ta ne don wahala?! Shin muna tunanin cewa wadannan abubuwan da suke faruwa ba su da dalili ne?! kuma shin mun sanya tunani domin ganin mun kama hanyar warwara?!
Ganin halin da duniya take ciki ya sanya mutanenta sun yanke kauna daga samun gyara, wannan kuwa shi ne ya fi komai muni, domin ba masu yanke kauna sai mutane batattu. Idan mutane suka yanke kauna to tabbas sun kauce hanyar Allah ne, amma muminai suna ganin hanyar gyara a wartsake, sai dai duniya ba ta sallama wa maganarsu, don haka dole ne wannan faganniya da dimuwa ta ci gaba.

Amma Allah madaukaki ya yanke duk wani uzuri ga dan Adam, kuma ya girmama shi, ya shiryar da shi duk wani tafarki, ya yi masa duk wata falala yana mai cewa: "Hakika mun girmama 'yan Adam, muka dauke su a tudu da kogi, muka arzuta su daga dadada, kuma muka fifita su a kan mafi yawan abubuwan da muka halitta fifitawa. (Isra'i: 70)
Sannan ya fifita shi a kan duk wata halitta kowace iri ce, ya sanya shi mai matsakaicin hali da idan ya ga dama sai ya fi mala'ika, idan kuwa ya ga wata damar sai ya fi duk wata halitta kaskanci. Kuma wannan ruwayar tana nuna mana haka a sarari yayin da take cewa: An karbo daga Imam Sadik (a.s): -yayin da Abdullahi dan Sinan ya tambaye shi Mala'iku ne suka fi ko 'ya'yan Adam?- sai ya ce: "Amirul Muminin Ali dan Abu Dalib ya ce: Ubangiji madaukaki ya sanya wa mala'iku hankali babu sha'awa, ya sanya wa dabbobi sha'awa babu hankali, sai ya sanya wa 'dan Adam duka biyun, to duk wanda hankalinsa ya rinjayi sha'awarsa to shi ya fi mala'ika, kuma duk wanda sha'awarsa ta yi galaba kan hankalinsa to ya fi dabbobi kaskanta. (Biharul Anwar: 60/299/5).

Idan mutum ya samu kamala yana iya zarcewa ya tafi babu iyaka ga kamalarsa domin daga Allah take wanda ba shi da iyaka. Yana iya kasancewa shi kadai ya fi dukkan mutane da sauran halittu daraja kamar yadda yake ga Annabi (s.a.w) da alayensa (a.s). Don haka ne zamu ga wata ruwayar tana nuni da hakan tana mai cewa: Daga Annabi (s.a.w): "Babu abin da ya fi dubunsa daga irinsa sai mutum". (Kanzul Ummal: 34615). Don haka ne zaka ga mutum daya amma ya fi miliyoyin mutane daraja.
Babbar ni'imar da Allah madaukaki ya yi wa mutane shi ne ta rashin toshe musu kofar kamala matukar suna son su samu kamalar. Kuma wannan kofa har su mutu ba a toshe ta, sannan kuma akwai wasu kofofin da ba su da iyaka da suke a bude har bayan mutuwa!.
Sannan akwai abin mamaki ga wannan halitta ta mutum mai sirri maras iyaka, sai dai Allah madaukaki ya yi mana bayani ta hannun annabawansa da wasiyyansu ka n dalilin da ya sanya shi halittar wannan halitta mai ban mamaki.
Ubangiji madaukaki yana cewa: Ban halicci mutun da aljani ba sai don su bauta mini. (Zariyat: 56).

Imam Ali (a.s) ya ce: "An umarce ku da tsoron Allah ne, kuma an halicce ku don kyautatawa da biyayya ne". (Nahajul balaga: Ibn Abil hadid/3/108)
Imam Husain (a.s) ya ce: "Ya ku mutane, Allah mai daukakar ambato bai halicci mutane ba sai don su san shi, idan suka san shi sai su bauta masa, idan suka bauta masa sai su wadatu daga bautar waninsa. Sai wani mutum ya ce: Ya dan manzon Allah (s.a.w), ina fansarka da iyayena, mene ne sanin Allah? Sai ya ce: Sanin kowane mutanen zamani Imaminsu wanda yake wajibi ne su yi masa biyayya". (Biharul Anwar: 23/83/22).
Imam Sadik (a.s) yana cewa: -yayin da wani zindiki ya tambaye shi cewa; saboda me Allah ya halicci halitta alhalin ba ya bukatar su, kuma babu wanda ya tilasta masa kan halitta su, kuma ba ya cancanta ya yi wasa da mu?- "sai Imam (a.s) ya ce: Ya halicce su domin su yi abin da zasu samu rahamar Allah da shi ne, sai ya yi musu rahama". (Biharul Anwar: 10/167/2).

Magana kan wannan lamari tana bukatar rubutu na musamman don haka sai mu kulle ta hakan, sai dai duk da hakan mutum yana da wani rauni maras misali. Duba abin da mahaliccinsa yake cewa: "An halicci mutum mai rauni". (Nisa'i: 28).
Sannan wasiyyin manzon rahama Muhammad (s.a.w), Imam Ali (a.s) yana cewa: Mutum miskini ne; Ajalinsa boyayye ne, ciwuwwukansa taskace suke, aikinsa kiyayye ne, sauro yana sanya shi zogi, shakewa (kwarewa) tana kashe shi, dan gumi yana sanya shi wari. (Nahajul balaga: Ibn Abil hadid /20/62).
Wannan ruwaya tana nuna mana matukar raunin mutum a cikin samammun bayin da Allah madaukaki ya halitta.
Ya kai dan Adam ka koma ka san matsayinka gun ubangijinka, ka san jagoran zamaninka, domin ka samu tsira gun Allah (s.w.t) daga dukkan kaskanta, ka kuma samu kamalar da ba ta da iyaka a wurinsa!.

HAKKIN MAI ILMANTAR DA KAI


Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Kuma hakkin mai tarbiyyantar da kai da ilimi -mai ilmantar da kai-, shi ne ka girmama shi, ka kuma karrama majalisinsa, da kyautata sauraronsa, da fuskantowa zuwa gareshi, kuma kada ka daga sautinka, kuma kada ka amsa wa wani mutum wani abu da yake amsa masa sai dai ya kasance shi ne wanda yake amsawa, kada ka yi wa wani magana a majalisinsa, kada ka yi gibarsa, kuma ka yi kariya gareshi idan aka ambace shi da mummuna, kuma ka suturta aibinsa ka bayyanar da darajojinsa, kada ka zauna da mikiyinsa, kuma kada ka yi gaba da masoyinsa. Idan ka yi haka, to mala'ikun Allah zasu yi maka sheda cewa ka nufe shi kuma ka san iliminsa saboda Allah ne ba don mutane ba".

Wannan ita ce shiryarwar Imam Aliyyu Sajjad (a.s) ga dalibi dangane da malaminsa, amma malami shi ma akwai hakkin dalibi a kansa, sai dai na malami ya fi girma, don haka shi ma malami yana hawa kansa ya tausaya wa dalibai, ya san cewa dansa ne don haka yana neman tsiransa ne, sannan kada ya yi wa dalibinsa gori ko ya yi masa mummunar ma'amala ko ya kausasa masa hali.
Malami mai hikima shi ne wanda yake yi wa dalibansa nasiha, ya nisantar da su daga miyagun halaye, kada ya muzanta musu wani ilimi da ba a wajansa suke koyon sa ba, kamar idan shi malamin nahawu ne to kada ya rika kushe musu Ilimin mandik, ya rika yi musu magana daidai fahimtarsu, kada ya yi musu rowar Ilimi.
Ilimi ko ilmi an fassara shi da ma'anoni daban-daban bisa yadda kowane ilimi yake kallon sa, misali ilimin falsafa yana ganin ilimi shi ne halartowar wani abu gun wani abu, idan abu maras mariskai na zahiri (wato maras jiki na zahiri) ya samu halarta gun wani kamarsa, kamar yadda rayin mutum take samun ilimi da wani abu ta hanyar daukar fotokofinsa da yake halarto mata sai ta san shi. Amma ilimin sanin tunanin dan Adam da yadda za a gyara shi wanda aka fi sani da ilimin mantik da ya tashi sai ya ce; ilimi shi ne halartar surar wani abu a cikin tunani.

Sannan wasu ruwayoyi sun yi nuni da cewa ilimi shi ne biyayya ga Allah, sabo kuwa shi ne jahiltar Allah, don haka zamu ga ashe ke nan ba wani abu ba ne jahilci sai sabo, ba wani abu ba ne ilimi sai biyayya ga Allah.
Sannan akwai wasu bayanai game da ilimi da wasu malaman yamma suka tafi a kansa da ma'anar cewa duk wani abu da ba ya iya yiwuwa a yi bincikensa ta hanyar tajribar mariskai to wannan abin ba ilimi ba ne, don haka duk wani ilmi da muke gani kamar ilimin addini, ba ilimi ba ne, domin babu wata laboratare da za a iya bincike a gano akwai Allah ko babu don haka addini ke nan ba ilimi ba ne. Kuma idan muka dauki ilmin falsafa shi ma ba ilimi ba ne domin babu wata laboratare da zamu iya binciken wani abu samuwa.
Don haka ne sai wannan bayanin yake nuna ilimi a matsayin wani abu ne da ya shafi duk wani abu da yake da alaka da zahirin samammu, amma duk wani ilimi da yake binciken wasu abubuwa da ba a riskar su da zahiri da mariskai kamar Allah, rayuka, da makamantansu to wannan ba ilimi ba ne.

Wannan isdilahi ne da ya faro daga turai tun lokacin da suka yi juyin tunani da ya samar da sabon tunani a turai, sai suka dauki addini da duk abin da ya shafe shi a matsayin wani abu da ba ilimi ba.
Idan mun duba duka wannan bayanai game da ilimi zamu ga kowane ilimi yana duba mene ne ma'anar ilimi daidai gwargwadon nau'in binciken da ya dogara kansa, ko kuma bisa akidar mai bincike.
Don haka ne zamu ga falsafa tana ganin halartar samamme gun samamme (wanda yake halarta ce ta maras jiki gun maras jiki) domin yana bahasi kan samuwa ne. Amma ilimin mantik tun da yana binciken gyara tunanin dan Adam ne sai ya ga ilimi a matsayin halartar surar wani abu a cikin tunani. Sannan idan muka duba yadda masu binciken ilimin dabi'a suka yi bayanin ilimi zamu ga sun yi bayaninsa yadda ya yi daidai da imaninsu ne, ta yadda ba su yadda da wani abu ilimi ba sai idan ya kasance za a iya binciken sa ta hanyar laburatare.

Ilimi yana da kima matuka kuma darajarsa a kan komai ba ta boyuwa, ubangiji ya yabi masu ilimi kuma ya yi nuni da cewa su kadai ne suke tsoronsa, sai dai wannan ilimi da zai kashe a bisa hakika shi ne ilimi a wurin Allah, ba abin da yake shi ne ilimi a wurin sauran mutane ba.
Kuskuren da mutane suke yi sai su ga wani wanda suke ce masa malami yana munanan ayyuka, ba ya tsoron Allah, sai su ce wannan malami ba ya tsoron Allah, alhalin wannan ba malami ba ne a wurin Allah, shi dai kawai wani mutum ne da ya san wasu abubuwa na shari'ar addini, sannan sai ya dauki kayan malamai ya sanya, sannan mutane suka yi imani da shi a matsayin malami, amma a wurin Allah ba malami ba ne.
Imam Ali yana siffanta ilimi a cikin Nahajul balaga daga cikin maganarsa da ya yi wa Kumail dan Ziyad an'Nakha'i. Kumail ya ce: Imam Ali (a.s) ya riki hannuna, sai ya fito da ni zuwa makabarta, yayin da ya kai sahara sai ya yi lumfashi mai tsawo sannan sai ya ce:
"Ya kai Kumail dan Ziyad, Hakika wannan zukata jaka ce, wacce ta fi su ita ce mafi kiyayewa, to ka kiyaye abin da nake gaya maka: mutane uku ne: Masani na Allah, da mai neman sani mai tsira, da kuma yuyar gayya masu bin duk wani mai kira, suna masu karkata tare da kowace iska, ba su haskaka da hasken ilimi ba, kuma ba su karkata zuwa ga wata madafa mai aminci ba".

Ya Kumail dan Ziyad, sanin ilimi addini ne da ake yi, da shi ne mutum yake samun biyayya a rayuwarsa, da kyawun taraswa bayan mutuwarsa, ilimi mai hukunci ne, dukiya kuwa abin hukuntawa.
Ya kai Kumail dan Ziyad, masu taskace dukiya sun mutum alhalin suna raye, malamai kuwa masu wanzuwa ne matukar zamani ya wanzu: Idanuwansu suna rasa -bacci- misalansu suna cikin zukata.
Lallai hakika a nan akwai tarin ilimi mai yawa -ya nuna kirjinsa- da ma na samu masu daukarsa! Sai da na samu masu saurin fahimta amma ba abin amincewa ba gareshi, wadanda suke amfani da addini a matsayin tsanin samun duniya, suna masu danne bayin Allah da ni'imarsa, da kuma danni masoyansa da hujjojinsa, ko kuma -ban samu wani wanda zan ba wa wannan ilimi ba sai- mai karkata zuwa ga rikon gaskiya amma ba shi da basira a tare da shi, shakku yana shiga zuciyarsa da zaran wata shubuha ta zo masa.
Ku sani babu wannan babu wancan! Ko kuma -ban samu wani wanda zan ba wa wannan ilimi ba sai- mai zari da jin dadi, mai saukin ja ga sha'awa, ko kuma -ban samu wani wanda zan ba wa wannan ilimi ba sai- mai ruduwa da tarin -dukiya- da boyewa, wadanda babu ruwansu da wani addini, abin da suka fi kusanci da shi su ne dabbobin kiwo! da haka ne sai ilimi yake mutuwa da mutuwar masu rike da shi.

Ya ubangiji haka ne! Babu wani lokaci da duniya zata zamanto babu mai tsayuwa da hujjar Allah, Imma dai zahiri mashahuri, ko mai jin tsoro mai boyuwa, domin kada hujjar Allah da ayoyinsa su baci.
Ya girman wancan -ina shi- ina wadancan? Wadancan wallahi! Su ne suka fi kowa karancin adadi, da girman daraja, da su ne Allah yake kiyaye dalilansa da ayoyinsa, har sai sun mika ta ga tsararrakinsu, su kuma kafa ta a cikin zukatan makamantansu, ilimi ya zo musu a cikin hakikanin basira, suka kuma kusanci ruhin yakini, suka tausasa abin da masu shekewa suka tsaurara shi, suka samu nutsuwa da abin da jahilai suka samu dimauta da shi, kuma suka sahibanci duniya da jikinsu, rayukansu suna rataye da mahalli mafi daukaka, wadannan su ne halifofin Allah a cikin duniyarsa, masu kira zuwa ga addininsa, kauna dai kauna zuwa ga ganinsu!. -sannan sai imam Ali (a.s) ya ce masa juya (tafi) idan ka so-. Nahajul-balaga; Hikima: 139.

Idan mun duba zamu ga wannan magana ta imam Ali (a.s) tana da ma'anoni masu darja da kima, da farko fadin Kumail dan Ziyad an'Nakha'i cewa; "Imam Ali (a.s) ya riki hannuna, sai ya fito da ni zuwa makabarta, yayin da ya kai sahara sai ya yi lumfashi mai tsawo sannan sai ya ce". Zamu ga Imam Ali (a.s) ya yi nuni da daya daga cikin hanyoyin tarbiyya ga dalibi, yayin da ya kama hannun dalibinsa domin ya nuna masa wani abu mai kima da daraja.
Sannan kuma daukar sa da ya yi zuwa sahara da wurin da yake mai sukuni da shiru kamar makabarta shi ma wata hanya ce mai amfani wurin tarbiyyar dalibi domin gaya masa wani abu muhimmi domin wannan yakan sanya shi tuna abin da aka gaya masa, da zauna masa a zuciya.
Bayan samun wannan yanayi mai kyau domin isar da sako muhimmi sai Imam Ali (a.s) ya fara da cewa: "Ya kai Kumail dan Ziyad, Hakika wannan zukata jaka ce, wacce ta fi su ita ce mafi kiyayewa, to ka kiyaye abin da nake gaya maka". Wannan ma wata hanya ce mai girma a matsayin gabatarwa domin shirya dalibi ya karbi magana mai muhimmanci, sai ya fara da nuna masa nau'in zukata, domin ya kiyaye me za a gaya masa.
Sannan sai Imam Ali (a.s) ya fara da cewa: " mutane uku ne: Masani na Allah, da mai neman sani mai tsira, da kuma yuyar gayya masu bin duk wani mai kira, suna masu karkata tare da kowace iska, ba su haskaka da hasken ilimi ba, kuma ba su karkata zuwa ga wata madafa mai aminci ba".

A nan ne fifikon ilimi da muhimmancinsa yake bayyana a fili, domin mutane guda uku, ko dai ya kasance mai ilimi masani da ubangijinsa, ko ya kasance mai neman sani, ko kuma ya kasance halakakke, wanda ba shi da wani haske, kuma duk inda ya ji wani kira sai ya bi ba tare da sanin gaskiya ko karyar wannan kiran ba, irin wadannan su ne wadanda ba su da wata madafa mai kyau.
Sannan sai Imam Ali (a.s) ya ce: Ya Kumail dan Ziyad, sanin ilimi addini ne da ake yi, da shi ne mutum yake samun biyayya a rayuwarsa, da kyawun taraswa bayan mutuwarsa, ilimi mai hukunci ne, dukiya kuwa abin hukuntawa.
A nan ma wata kimar ilimi ta sake bayyana a fili ta yadda zamu ga na farko shi kansa ilimi addini ne, kuma duk wanda ka saurara ka karba daga gareshi to ka karbi addini daga gareshi ne, yana iya kasncewa na gari ko waninsa. Sannan kuma idan babu ilimi babu biyayya, don haka wanda bai san Allah ba, kuma ya yi da'awar yana biyayya gareshi ya yaudari kansa, sau da yawa irin mutanen da suka jahilci Allah idan sun tashi domin bauta masa sai su sawwala wani gunki a kwakwalwarsu kamar yadda wani yake gaya mini sai ya ga kamar wani zaki ne babba a gabansa yake bauta wa, ko wani sarki a kan karagar mulki. Irin wadannan mutane da suka jahilci Allah bas u da bambanci da Abujahal, sai bambancin cewa shi yana da gunki na fili da yake bautawa, su kuwa suna da gunki na kwakwalwarsu da suke bautawa.

Don haka ne zamu ga Imam Ali (a.s) bayan ya nuna cewa da ilimi ne ake samun biyayya sai kuma ya nuna cewa babu wani sakamako da ake samu sai da ilimi da fadinsa "da kyawun taraswa bayan mutuwarsa" wato bayan mutuwar bawa.
Sannan kuma sai ya yi nuni da wani abu muhimmi na cewar ilimi shi ne gaba da komai har dukiya, ita dukiya it ace ya kamata a sarrfa ta yadda aka so, amma ilimi shi ne hasken da yake nuni da yadda za a sarrfa ta, don haka mutane suna iko kan dukiya, shi kuma ilimi shi ne yake da iko a kan mutane sai Imam (a.s) ya yi nuni da hakan a fadinsa: "ilimi mai hukunci ne, dukiya kuwa abin hukuntawa".
Sannan Imam Ali (a.s) ya ce: "Ya kai Kumail dan Ziyad, masu taskace dukiya sun mutu alhalin suna raye, malamai kuwa masu wanzuwa ne matukar zamani ya wanzu: Idanuwansu suna rasa -bacci- misalansu suna cikin zukata".
A nan zamu ga ya sake nuna cewa dukiya da ilimi duk abubuwa ne da ake taskacewa, sai dai mai taskace dukiya ya bambanta da mai taskace ilimi, domin shi mai taskace dukiya ya halaka, kuma shi matacce ne tun kafin ya mutu, amma mai taskace ilimi yana rayuwa ne har abada, koda kuwa ya mutu a zahiri to bai mutu ba.
Amma su waye masu ilimi sai mai daraja ya yi nuni da cewa suna rasa bacci da dare, wadannan abubuwan da sukan hana su bacci suna da yawa, sun hada da duba cikin ilimi, da munajati da Allah, da tausayin al'umma.

Sannan ana iya fassara shi da samuwarsu ta narke cikin zatin Allah (s.w.t) ta yadda ba sa ganin kawukansu sai dai ubangijinsu, don haka ne suke muhimmantar da lamurran Allah da bayinsa a kan nasu, kamar yadda zamu ga suna kwana suna yi al'ummar Allah da bayinsa addu'a kamar yadda sayyida Zahara da muke juyayin ranar wafatinta da shahadarta a yau ta shahara da wannan, ta kasance tana kashe dare gaba daya tana ibada tana yi wa al'umma da makota addu'a, danta Imam Hasan (a.s) yana ibada tare da ita dukkan dare alhalin yana kasa da shekaru tara, yana tambayarta ya baba! Na ga ina ibada gaba dayan dare kina yi wa muminai addu'a amma ban ji ko sau daya kin yi wa kanki ba? Sai ta ce: "Ya kai dana, na waje tukun sannan gida"!. Ko kuma ana iya fassara shi da "makoci tukun sannan gida"!. (Ilalus Shara'i: 1; 181).
Sannan Imam (a.s) ya yi nuni da cewa misalansu a zukata suke, domin ya nuna cewa masu wannan siffofi suna da ilimin sanin Allah ba kawai a kwakwalensu da tunaninsu ba, wadannan masana Allah ne wadanda suke da ilimi cikakke da shi da zukatansu. Su ba da ilimi na tunani kawai suka san ubangijinsu ba, su sun san Allah madaukaki da zukatansu, ta yadda babu wani abu da suke fuskanta da zukatasu sai shi. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Ban taba ganin wani abu sai na ga Allah a cikinsa ko a farkonsa ko tare da shi", yana cewa: "Ban taba bautawa ubangijin da ban gan shi ba". Al'aka'idul islamiyya: Markazul Mustapah: j 2, s; 311).

Wannan yana nuna mana ilimin badini wanda aka fi sani da cewa ilimi ne na kashafi da yake da shi, wannan ilimin ba a kwakwalwa yake ba, ilimi ne da yake a zuciya. Don haka ne Imam (a.s) ya nuna cewa sai da ya ga ubangijinsa da wannan ilimi na zuciya, sannan sai ya bauta masa.
A nan ne zamu ga bambanci tsakanin ilimi na mariskai, da kuma na kwakwalwa, da na zuciya da martabobin da suke tsakaninsu masu nisa. Kamar dai bambancin mutumin da ya ji labarin wuta da siffofinta, da wanda kuma ya ga wuta da yadda take kona abubuwa, da wanda ya shiga wuta ya dandani zafinta ne.
Sannan sai Imam Ali (a.s) ya fadi cewa; "Lallai hakika a nan akwai tarin ilimi mai yawa -ya nuna kirjinsa- da ma na samu masu daukarsa! Sai da na samu masu saurin fahimta amma ba abin amincewa ba gareshi, wadanda suke amfani da addini a matsayin tsanin samun duniya, suna masu danne bayin Allah da ni'imarsa, da kuma danne masoyansa da hujjojinsa, ko kuma -ban samu wani wanda zan ba wa wannan ilimi ba sai- mai karkata zuwa ga rikon gaskiya amma ba shi da basira a tare da shi, shakku yana shiga zuciyarsa da zaran wata shubuha ta zo masa".

A nan zamu ga Imam Ali (a.s) yana nuna kirjinsa da cewa akwai ilimi mai tarin yawa, amma al'ummar ba zata iya daukarsa ba, sannan ya kawo dalilan haka:
Na farko su ne mutanen da zasu iya fahimta amma idan suka sani zasu yi amfani da shi wurin tara duniya da danne bayin Allah da fatawowin son rai domin su samu wani abin duniya gun sarakuna da masu mulki, wadannan su ne masu sayar da ayoyin Allah da kankanin kudi na rayuwar duniya.
Sai na biyu; su ne mutanen da suke da ikhlasi amma ba su da wayewa da basira saboda karancin hankalinsu, suna iya samun ilimin amma ba ya canja yadda suke ganin rayuwar duniya da lahira, sannan ba sa iya wayewa. Don haka ne ko yaya shubuha da abubuwa masu rikitarwa suka zo sai su dabarbarce.
A nan ne abin da muka rubuta a wata makala kan cewa al'umma tana da zababbu da kuam bita-zuwai, sannan muka nuna cewa ilimi ba ya sanya mutum cikin zababbu sai idan ya haskaka tunaninsa da zuciyarsa. Matukar ba haka ba, to ko ya shekara 50 yana karatu zai kasance yana tunani kamar yadda wanda ya rayu a titi yake tunani, wannan lamarin yana daga cikin abin da aka jarrabe mu da shi a cikin makarantun ilimin addini, sai ka ga dalibi ya yi karatu shekaru 16 amma ba shi da tunani kuma wannan ilimin bai canja mahangarsa kan rayuwa da addini, da sanin Allah ba.
Don haka ne sai mu samu wasu ba su halarci makaranta ba, amma suna da wayewa da ita tantance mai kyau, wasu kuwa sun halarta amma ba su da wannan hasken. Wannan babu bambanci a makarantun addini ne ko kuwa a Jami'o'i, sau da yawa kakan samu farfesa amma ba ya buda tunaninsa. Kakan samu farfesa a ilimin lissafi (mathematic) mantik (Logic) amma duk wannan hankalin da yake da shi a ilmance idan ya zo al'ummarsa sai ka same shi cikin masu bautar shanu!.

Sannan sai Imam Ali (a.s) ya yin nuni da cewa: "Ku sani babu wannan babu wancan! Ko kuma -ban samu wani wanda zan ba wa wannan ilimi ba sai- mai zari da jin dadi, mai saukin ja ga sha'awa, ko kuma -ban samu wani wanda zan ba wa wannan ilimi ba sai- mai ruduwa da tarin -dukiya- da boyewa, wadanda babu ruwansu da wani addini, abin da suka fi kusanci da shi su ne dabbobin kiwo! da haka ne sai ilimi yake mutuwa da mutuwar masu rike da shi".
Imam Ali (a.s) ya sake ci gaba da lissafa mutanen da ya samu wadanda ba zai yiwu a ba su ilimi ba, sai ya ci gaba da lissafa na uku da cewa; shi ne mutum mai zari da jin dadi, mai saukin ja ga sha'awa, wanda ba shi da iyaka a sha'awarsa, ba shi da kaidi ga jarin duniya da neman kece raini da jin dadi da holewa, mai katon ciki da neman mata domin kawar da sha'awarsa.
Sai kuma na hudunsu wanda yake mai ruduwa da tarin -dukiya- da boyewa, burinsa ya ga bankunansa sun cika, ta yadda zai samu matakin yanke talauci, kuma duk abin da zai yi na son rai domin ya samu duniya zai yi. Irin wadannan mutanen sau da yawa sukan samu sirrin ayoyin Allah sai su mayar da su abin sihiri.
Don haka sai Imam Ali (a.s) ya siffanta wadannan mutanen da cewa su babu ruwansu da wani addini, don haka sun fi kusa dabbobi a siffofinsu fiye da mutane.
Sai Imam (a.s) ya yi nuni da cewar da haka ne ilimi yake mutuwa, domin idan malami bai samu wanda zai ba wa wannan amana ba, bai halatta ya sanya ta wuri lalatacce ba kamar gun irin wadannan mtuane guda hudu, don haka sai malami ya mutu, sai ilimin da yake tare da shi ya mutu.

Don haka ne sai Imam (a.s) ya koka zuwa ga ugangijinsa da cewa: Ya ubangiji haka ne! Babu wani lokaci da duniya zata zamanto babu mai tsayuwa da hujjar Allah, Imma dai zahiri mashahuri, ko mai jin tsoro mai boyuwa, domin kada hujjar Allah da ayoyinsa su baci".
Tun da Imam Ali (a.s) a karshen rayuwarsa bai samu wanda zai ba wa ilimi ba sakamakon cewa munafukai sun kashe dukkan sahabbansa masu ikhlasi da imani sahihi, ta yiwu wani ya tambaya cewa shin ilimi ya kare da rasuwarsa ke nan? To domin gudun kada wani ya yi wannan tunani sai Imam Ali (a.s) ya yi nuni da cewa bayansa a kowane zamani akwai wasiyyin annabi (a.s) da zai ci gaba da rike sakon Allah (s.w.t), imma dai wannan wasiyyin da muka fi sani da imami a zahiri yake, kamar shi Imam Ali (a.s) da Hasan da Husain da kuma sauran imamai tara bayan Husain (a.s), imma dai boyayye kamar Imam Mahadi (a.s) imami na goma sha biyu kuma karshen wasiyyan annabi (s.a.w) wanda ya buya da umarnin Allah da ilhamar ubangiji (s.w.t) saboda tsoron kisa tun sama da shekaru dubu daya ke nan yana mai jiran umarnin Allah da bayyana.
Sannan sai Imam Ali (a.s) ya yin nuni da karancin adadinsu yana girmama karancin adadin yana mai cewa: "Ya girman wancan lamarin! -ina shi- ina wadancan? Wadancan wallahi! Su ne suka fi kowa karancin adadi", Imam Ali (a.s) yana mai rantsuwa da Allah domin nuni zuwa ga cewa adadin yana da matukar karanci. Idan mun duba dukkan littattafan musulmi sunna da shi'a duka sun yi ittifaki da cewa manzon Allah (s.a.w) ya fadi cewa su goma sha biyu ne kawai.

Sannan sai Imam Ali (a.s) ya ci gaba da nuni ga siffofinsa yana mai cewa: "da girman daraja, da su ne Allah yake kiyaye dalilansa da ayoyinsa, har sai sun mika ta ga tsararrakinsu, su kuma kafa ta a cikin zukatan makamantansu".
Wato bayan adadi mai karanci, sai kuma girman daraja, domin sun fi sauran annabawa daraja kamar yadda manzon Allah (s.a.w) ya yi nuni da su a fadinsa cewa: "Malaman al'ummata sun fi annabawan Banu Isra'il daraja". (Awa'ilul Makalat: Sheikh Mufid; s 178).
Sannan ya yi nuni da cewa da su ne Allah yake kare dukkan halitta, kamar yadda manzon Allah ya yi nuni da cewa matukar suna nan to lamarin al'umma yana nan kamar yadda yake a ruwayar Muslim da waninsa. Wasu ruwayoyin kuma sun yi nuni da cewa idan suka kare to babu duniya dole ta tashi, ko dole ne ta rushe gaba daya.
Sannan a fadinsa "har sai sun mika ta ga tsararrakinsu, su kuma kafa ta a cikin zukatan makamantansu". Yana nuna cewa duk sa'adda wani daga cikinsu ya zo yana kasancewa kamar magabacinsa ne, babu wani abu da yake jahilta a cikin duk wani ilimi, a tare da shi akwai dukkan abin da duniya take bukata babu ko tawaya daya. Imami tsaran imami ne kuma makamancinsa ne, don haka babu wani wanda zai zo sai wanda zai biye masa ya kasance kamarsa a komai babu wani bambanci.

Idan kuma muka duba su zamu ga suna da ilimi da ba su taba karatu gun wani ba, sai Imam (a.s) ya yi nuni da yadda suke samun ilimi cewa dukkan wasiyyin annabi (s.a.w) yana samun iliminsa imma daga koyarwar imamin da ya gabace shi, ko kuma ilhama daga Allah madaukaki, don haka sai yake cewa: "ilimi ya zo musu a cikin hakikanin basira, suka kuma kusanci ruhin yakini". Wannan hanyar samun ilimi babu wani wanda Allah ya hore wa ita hakikanin horewa da ma'anarta ta hakika sai su. Don haka ne ya zama dole ga sauran mutane su nuna mana dalilinsu, da inda suka samo, amma su manzon Allah (s.a.w) ya riga ya yi wasiyya da su, don haka su suna da lasisi daga Allah kai tsaye, kuma jefa musu ilimi a zukatansu daga Allah yana tare da hasken littafinsa da ba ya saba masa faufau.
Sannan Imam (a.s) ya yi nuni da rashin kuskure a iliminsu sabanin ilimin sauran mutane sai ya fadi siffofinsa yana mai cewa: "suka tausasa abin da masu shekewa suka tsaurara shi, suka samu nutsuwa da abin da jahilai suka samu dimauta da shi, kuma suka sahibanci duniya da jikinsu rayukansu suna rataye da mahalli mafi daukaka, wadannan su ne halifofin Allah a cikin duniyarsa, masu kira zuwa ga addininsa, kauna dai kauna zuwa ga ganinsu!.
A nan zamu ga Imam (a.s) yana nuni da nau'i biyu na ilimi; ilimin da yake babu kuskure a cikinsa wanda yake daga Allah da manzonsa zuwa ga wasiyyansa, da kuma ilimin masu neman duniya da shi, da wadanda suka kaucewa gaskiya suna sane ko bisa jahilci.
Idan ilimi ya kauce wa gaskiya, sai ya tsananta wurin da aka tausasa, ko ya yi akasin hakan ya tausasa wurin da aka tsananta, sai ya takaita ko ya wuce gona da iri. Ya kuma sake nuni da dimautar jahilai da ake kira malamai da abin da su wasiyyan Annabi (a.s) suka nutsu da shi, da kuma akasin hakan, wanda ya yi bincike mai zurfi zai ga yadda irin wadancan mutane suke haramta halal saboda suna samun dimautuwa saboda ita, suka kuma halatta haramun saboda suna samun nutsuwa da ita.

Sannan sai ya yi nuni da cewa iliminsu yana da alaka da Allah madaukaki da tsoronsa, kuma ilimi ne na hakkul yakin, kamar yadda a baya kafin wadannan sadarori ya yi nuni da ilmul yakin, da na ainul yakin. Don haka sai Ali (a.s) ya ce: "kuma suka sahibanci duniya da jikinsu rayukansu suna rataye da mahalli mafi daukaka, wadannan su ne halifofin Allah a cikin duniyarsa, masu kira zuwa ga addininsa, kauna dai kauna zuwa ga ganin su".
Su suna rayuwa da ruhinsu a lahira, amma jikinsu yana wannan duniya ne, alakarsu da duniya kamar 'ya'yan itace ne da suka nuna ta yadda ko yaya iska ta kada su sai su fado su bar jikin uwa. Haka nan alakar jikinsu da rayukansu ta ke, amma lahira kuwa rayuka suna manne like da ita, ta yadda komai girgiza ba zasu rabu da ita ba.
Wannan su ne siffofin halifofin Allah a wannan duniyar, kuma su ne suka cancanci a bi su. Domin rashin damfaruwarsu da duniya yana nuna babu wata maslaha da suke nema a cikinta ga kawukansu balle su yi zalunci. Sannan iliminsu da zahiri da kuma badinin samammu yana ba su damar sanin yadda zasu shimfida adalci a tsakaninsu. Sannan saninsu da Allah madaukaki yana ba su yakini da babu shakku a cikinsa, don haka wadannan su ne suka fi cancantar kasancewa masu wakiltar Allah a kan bayinsa.
Daga karshe bayan wadannan kalamai masu daraja sai imam (a.s) ya juya yana gaya wa Kumail cewa yana iya tafiya kamar yadda muka kawo a sama cewa: "-sannan sai imam Ali (a.s) ya ce masa juya (tafi) idan ka so-".
Sannan Imam Ali (a.s) yana tabbatar mana da wannan siffofi nasu masu daraja yayin da yake cewa: "Ban taba kokwanton gaskiya ba tun da na gan ta". Nahajul-balaga; Hikima: 174. Wannan siffa ce ta wanda al'umma ya kamata su bi, domin duk wanda yake da yakini kan lamarinsa shi ne ya fi cancanta da biyayya ba wanda yake kan kokwanto ba.
Wadannan hikimomi masu daraja ba don Imam (a.s) ya furta su an nakalto su daga gareshi ba, da duniya ta rena masa, wannan yana nuna mana girmansa (a.s), sannan yana nuna mana gaskiyar maganarsa yayin da yake cewa: "Mutum boyayye ne karkashin harshensa". Hikima: 140, domin da maganarsa da zancensa ake sanin kimarsa.
Sannan a nan muna iya fahimtar cewa kowane mutum yana da matsayinsa domin irin wadannan kalamai masu kima da daraja suna nuna mana wani sirri a wata marhalar rayuwar Imam Ali (a.s), wanda ba kowane zai iya gaya wa wannan ba, idan mutum ya san kimarsa da darajarsa, da iyakacin matsayinsa ya rabauta. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Mutumin da bai san kimarsa ba, ya halaka". Hikima: 141.
Sannan idan akwai wata magana mai daraja da kima to bai kamata ba a yi shiru ba a isar da ita ba, domin akwai wadanda suka dace da ita, don haka ya hau kan malami ya bayyanar da ilimi yayin bukatar hakan, kamar yadda yake wajibi kan jahili ya yi shiru. Imam Ali (a.s) ya ce: "Babu alheri cikin yin shiru ga hukunci, kamar yadda babu alheri cikin yin magana da jahilci". Hikima: 172.

Ilimin Gaibi
Sannan akwai wani bahasi da ake yi game da ilimin gaibi wanda yake cikin bahasosin da aka tayar da jijiyar wuya a kansu. Sai dai yana da kyau mu san me ake nufi da gaibi domin amsar ma'anar sanin gaibi ta fito a fili. A cikin littattafai ya zo cewa; Gaibi shi ne duk wani abu da ya boya ga mutum. Kitabul Ain: Khalil Farahidi; 4/454, Lisanul Arab: 1/654, Majma'ul Bahrain: 2/134.
Don haka muna ganin gaibi shi ne abin da ya boyu daga gabobinmu da muke riskar abubuwa da su, wadanda muke kiran su da "Mariskai", wadannan mariskar sun hada da ji, da gani, da lasa, da shafa, da shaka. Sai dai a cikin Kur'ani mai girma an yi amfani da kalmar Gaibi ga dukkan abin da yake ba mahalarci ba ne. kamar yadda ya zo a cikin Surar An'am: 73.
Da kuma fadinsa: "Masanin gaibi da sarari, kuma shi ne mai hikima mai masaniya". Kamar yadda ya zo a surar Tauba: 94, da 105.
Domin lamarin mas'alar gaibi ya bayyana garemu sosai ya zama wajibi mu yi duba zuwa ga kashe-kashen gaibi; idan mun duba zamu ga gaibi ya kasu gida biyu: Sakakken gaibi, da Gaibin dangantaka. Sakakken gaibi; Shi ne gaibin da yake sake ba kaidi, wanda yake babu wani wanda ya san shi sai mahaliccin duka, kuma babu wata hanya da za a iya saninsa, irin wannan gaibin ya hada da sanin zatin Allah madaukaki, da sanin hakikanin siffofinsa da sauransu. Amma Gaibin danganta; Shi gaibi ne wanda saninsa ya danganta da matsayin ilimin mai saninsa da kusancinsa da mabubbugar gaibi duka wato; Allah mahalicci. Yana buda wa bayinsa saninsa daidai gwargwadon yardarsa da su, da karfin dauke sakonsa da suke da shi, da kuma zamani ko wurin da zai ba su wannan sanin na gaibi, kuma ya yi nuni da hakan a cikin surar Jinni: 26-28.

Da wannan ne wani abin yake zama gaibi dangane da wani mutum, amma ba gaibi ba ne dangane da wani, sai aka ambace shi Gaibin dangantaka. Sai wani abu ya kasance gaibi ga mariskai amma bai gaibi ba ne ga hankali; mariskai ba sa iya riskar dokoki gama-gari, sai dai suna riskar daidaikun halittun da ake iya riskar su a fili ta hanyoyi mabambanta kamar ji, da gani, da shaka, da tabawa. Haka nan ma abin da yake cikin gida ba gaibi ba ne ga wanda yake cikinsu, amma gaibi ne ga wanda yake wajen gidan. Sai wani abu ya kasance gaibi gun mutane amma ba gaibi ba ne gun wasu dabbobi, ko aljanu, ko mala'iku; musamman zamu ga akwai wasu dabbobi da suke iya gani ko jin wasu sauti da dan Adam ba ya iyawa. Haka nan wani abin yake gaibi a wurin dukkan halittun Allah, amma babu wani abu da yake gaibi a wurin Allah madaukaki, domin shi ne ainihin ilimi.

Shin Akwai Wanda Ya San Gaibi Ban Da Allah?
Idan muka duba ayoyin Kur'ani mai girma zamu ga suna nuna mana sanin gaibi da ma abin da yake sarari duk na Allah ne; ayoyi kamar: Naml: 65, da An'am: 59. Sai dai idan mun lura zamu ga sanin gaibi da ma'anar da ya zo a wannan ayoyin bai kore samuwar saninsa ga wasu bayi da Allah ya zaba ba, don haka ne zamu iya fahimtar ma'anar babu wanda ya san gaibi sai Allah tana nufin asalin saninsa, da cewa; babu wanda ya san gaibi da kansa sai ubangiji madaukaki. Amma wanin ubangiji idan ya san gaibi to da sanarwar ubangiji ne ba da kansa ba, don haka saninsa da gaibi yana bin sanarwar da Allah ya yi masa ne, da ba shi kyautar wannan ilimi da Ubangiji madaukaki ya yi, don haka ne zamu ga ayar nan ta surar Jinn: 26-28, da sauran ayoyi kamar: Aali Imran: 179, 44, da Yusuf: 102, duk suna nuni da haka.
A cikin Kur'ani mai girma ya zo da bayanin annabawa (a.s) da Allah madaukaki ya sanar da su gaibi, idan mun koma wa ayoyi kamar haka: Yusuf: 41, da Aali Imran: 49, zamu ga yadda annabawa suka san gaibi kuma suka gaya wa mutane shi. Kamar yadda zamu samu labarun fadin abubuwan da zasu wakana da imam Ali (a.s) da sauran imamai (a.s) suka yi, kamar yadda ya zo a cikin Nahajul Balaga: 186, An'am: 75, da Kafi: 1/257. Sai dai sun sanar da mutane cewa wannan duk daga koyarwar manzon Allah (s.a.w) ce da ya sanar da su, wato ba sun sani ba ne su a kashin kansu, sai dai sanarwa ce daga Allah da manzonsa.

HAKKIN SARKI KO SHUGABA AKAN JAMA'ARSA

Hakkin Sarki (Shugaba)
Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Amma hakkin jagora shi ne ka san cewa shi jarrabawa ce gareka, kuma shi abin jarrabawa ne game da kai saboda abin da aka sanya a hannunsa a kanka na iko, kuma ka tsarkake masa nasiha, kada ka yi gogayya da shi, ka ga ke nan ka sanya shi ya sanya hannunsa a kanka sai ka kasance dalilin halakarka -da gamawa da kai- da halakarsa -da zaluntarka-.
Ka kaskan da kai da tausasawa domin ba shi yarda da kai da abin da zai kame shi daga gareka, kuma ba zai cutar da addininka ba, kuma ka nemi taimakon Allah a kansa a cikin dukkan wannan.

Kuma kada ka dora kanka a kansa, kada ka yi gaba da shi -da saba masa-, domin idan ka yi haka to sai ka sanya shi ya yi laifi a kanka -ta hanyar gamawa da kai- kuma ka yi laifi ta hanyar sanya shi -yin ukuba- a kanka, sai ka sanya kanka fada wa abin ki, ka sanya kansa ta halaka saboda kai, kuma kai ne ke nan ka zama mai taimaka masa a kanka, kuma mai tarayya da shi a abin da ya yi maka na mummuna. Babu karfi sai ga Allah".
Asalin hakkin mulki na Allah ne gaba daya, kuma ayoyi masu yawa sun yi nuni da hakan a cikin Kur'ani mai girma da hadisai madaukaka. Fadinsa madaukaki: "Mulkin sammai da kasa na Allah ne", yana nuni da hakan. Sai Allah ya mika wannan lamarin a hannun annabawansa, ya aiko su ba domin komai ba sai domin dan Adam ya bi su ya samu rahamarsa, amma sai mutane suka bijire musu, suka saba wa Allah madaukaki game da biyayyarsu.
Wadannan hikimomi na Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s) suna nuna mana yadda mutum zai yi taku da shugaba a cikin al'ummarsa cewa kada ya yi wani abu da zai sanya shi ya kasance abin gaba da shi da jagoransa har ya kai shi ya zama abin fadansa. Domin yin haka yana nufin su biyu da shi da shugaban duk su halaka, domin idan shugaban ya kashe shi ko ya daure shi ko ya doke shi a kan saba masa to yana da zunubin zaluntarsa, shi kuwa idan ya yi haka har ya tunzura shugabansa ya yi masa haka to shi ma ya yi laifin sanyawa a zalunce shi.

Imam Aliyyu asSajjad bai tsaya nan ba, har sai da ya yi nuni da babban laifin shi wanda ya sanya jagoransa ya kashe shi da cewa; shi ma ya yi tarayya da jagoransa wurin kashe kansa!.
A nan ne zamu fahimci cewa sarki ko shugaba da Imam Sajjad (a.s) yake nufi a cikin wannan bayanin shi ne jagoran da yake ba ma'asumi ba ne. Domin jagora kamar annabi ko wasiyyin annabi ba shi da siffofin da Imam Sajjad (a.s) ya kawo, domin shi ba ya fusata don kansa sai don Allah madaukaki.
Da sannu zai bayyana gareka cewa shi jagoranci asali Allah ya ba wa annabi ne da wasiyyinsa bayansa, amma sakamakon mutane sun ki jagorancinsu sai suka yi gaban kansu, sai dai ita shari'a sau da yawa akan samu wani abu da ba ta yarda da shi ba, sai dai tun da ya samu, to sai ta kasance tana da nata hukunce-hukunce a kanta.
Don haka ne zamu ga tun da hukuma ta kubuce wa wasiyyan annabi (s.a.w) amma wannan ba yana nufin su yi banza da wannan sarakuna da shugabanni ba, don haka sai suka dauki matakin shiryar da wadannan jagororin da kuma al'umma, da nuna musu hanyar gaskiya, da yi musu nasiha, da gyara akidu da tunanin al'umma kan mene ne gaskiya domin su dace da abin da Allah yake son a sauran janibobin rayuwarsu. Sannan sai Allah ya yi musu hisabi gwargwadon saninsu da nisantarsu da wadanda Allah ya yi umarnin biyayya garesu na wasiyyan annabi (a.s).

Wasiyyan annabi (s.a.w) su ne wadanda aka sanya musu alhakin fassara Kur'ani ga mutane domin suna da ilimi daga annabi da ilhama daga Allah, don haka ne Manzon Allah (s.a.w) ya hada su da Kur'ani a matsayin alkawari karami kuma nauyi bayan Kur'ani wanda yake shi ne alkawari babba nauyi mafi girma, don haka ne suke da wannan alhakin a kansu.
Sannan su ne suke da hakkin jagoranci kamar yadda yake shi ne ra'ayin Shi'a da ya tafi a kan cewa mulki na Allah ne shi ne yake bayar da shi ga wanda ya so, don haka Allah ya ayyana wanda zai jagoranci al'ummar nan, sai dai al'ummar ce ta ki, kamar yadda al'ummun baya suka ki wadanda Allah ya ayyana musu. Ahlussunna da dukkan kashe-kashensu da kuma Wahabiyawa suna ganin mulki yana hannun mutane ne da suke zabar wanda suka so, don haka duk wanda suka zaba shi ne jagora, kuma ayyana shi ba ya hannun Allah!.
Sai dai Shi'a duk da suna ganin iko na Allah ne da ya sanya shi hannun annabi (s.a.w) da wasiyyansa (a.s) sai dai ba su da ikon dankara shi kan mutane sai idan mutane sun yarda.

Don haka da mutanen Madina ba su yarda da shugabancin annabi (s.a.w) ba, da ba shi da ikon dora shi da karfi kan mutane, da har ya koma ga Allah bai kafa hukuma ba, kamar yadda sauran wasiyyansa suka yi bayansa.
A nan ne ya kamata mu yi magana kan siyasar musulunci wacce take lamari ne da ya shafi jagorancin jama'ar musulmi kamar yadda yake bisa dokokin shari'a. Amma musuluncin siyasa abu ne maras kyau, domin shi ne amfani da wata manufa domin samun cimma wani hadafi da guri.

Ma'anar farko wato siyasar musulunci tana da kyau domin amfani ne da siyasa domin yin hidima ga addini, kuma hanyar jagoranci kamar yadda musulunci ya gindaya. Amma ma'ana biyu ta munana matuka domin tana nufin a yi amfani da musulunci ne domin cimma wani buri ko hadafi na siyasa, wannan lamari matuka ya munana kuma mun ga misalansa a siyasar duniya a kasashe daban-daban.
Mece Ce Siyasa?

Wasu Suna Cewa: Siyasa a dunkule ta kunshi jagorancin al’umma da tsarin tafiyar da al’amuransu (da yake cikin tsarin da dan’Adam yake a kansa a kasashe da ya hada da majalisar dokoki da ta yin doka (kotu) da ta zartarwa (wacce ministoci da shugaba suke cikinta).
Ashe kenan muna iya cewa jagorancin al’umma a dunkule shi ne ake nufi da siyasa, kamar yadda kalma ce ta larabci da take nufin jagorancin al’umma da tafiyar da al’amuransu. Ko da yake kada mu manta da yadda ake amfani da wannan kalmar da ma’anar yaudara, ko kuma sanya bangaranci a cikin warware wasu al’amura ko kuma kushe wani abu da ya fito ba daga namu bangaren ba, da makamantan hakan.

Idan mun duba tarihin rayuwar dan’Adam tun farkon samuwarsa yana tare da siyasa ne, sai mutum na farko ya kasance shugaba da zabin Allah a kan zuriyarsa, sai ya kasance annabi ne da yake karbar sako daga Allah (s.w.t) kai tsaye domin ya shiryar da shi kan yadda zai tafiyar da al’amuran jama’a a duniya, kai wani tunani da ya zo mini a kwakwalwata da na dade ina mamakinsa shi ne; cewar Allah (s.w.t) a farkon maganarsa game da dan’Adam da zai halitta ya fara ne da maganar siyasa yayin da yake gaya wa mala’iku cewa; zan sanya halifa a duniya. Halifa kuwa yana nufin mai maye gurbin Allah (s.w.t) a kowane abu a duniya da ya hada da tafiyar da al’amuran bayi wanda shi ne bangare mafi muhimmanci, domin kuwa shi ne ya shafi shiryar da dan’Adam kan al’amuransa na duniya da lahira.
Duba ka gani yayin da Allah (s.w.t) ya ce da mala’iku: “Ni mai sanya halifa (mai wakiltata) a bayan kasa ne…” Bakara: 30. Da fadinsa: “Ya kai Dawud mu mun sanya ka halifa (mai wakiltar Allah cikin tafiyar da al’amuran bayi) a bayan kasa, sai ka yi hukunci tsakanin mutane da adalci…” surar Saad: 26.

Da wannan ne zamu iya gane cewa tun farko addini yana damfare da siyasa kai tsaye, kuma tushen addini ya kafu kanta koda kuwa wasu daga malaman musulmi sun ki yarda da hakan.
Amma dayawan ruwayoyi sun nuna mana ba yadda za a yi a cire jagoranci daga tushen addini, don haka imani da jagorancin annabawa (a.s) da kuma wasiyyoyi da wasiyyai (a.s) da suka bari yana daga tushen addini, kuma idan mutum bai yi imani da su ba koda kuwa ya fi kowa biyayya ga Allah a sauran bangarori Allah ba zai karbi ibadarsa ba, don haka ne ma duk wanda ya mutum bai san jagoran zamaninsa ba to ya yi mutuwar jahiliyya. (Minhajul karama, Allama Hilli, Shafi: 27). Domin zai zo a lahira babu wani abu da Allah zai karba na ayyukansa. Don haka yarda da manzon Allah (s.a.w) da wasiyyoyinsa da wasiyyansa (a.s) wanda ya hada da Kur'ani da halifofinsa (a.s) wadanda bai bar mutane ba sai da ya gaya musu wadannan halifofin nasa kuma ya fadi adadinsu cewa su sha biyu (a.s) ne kuma ya fadi sunanyensu sannan kuma Manzon Allah mai tsira da aminci ya gaya wa mutane ba zasu taba kauce wa hanya ba suna tare da Kur'ani har sai sun riske shi a tafkin alkausara a ranar lahira.

Ashe ke nan siyasa ita ce tushen addini da idan ma ba ka zama dan siyasa ba karkashin jagorancin da Allah (s.w.t) ya gindaya maka to kai ayyukanka ba zasu karbu ba har abada, zaka yi mutuwar jahiliyya ne. Don haka ne ma halifan manzon Allah (s.a.w) da ya yi wasiyya da shi na farko kuma jagoran Ahlul-bait (a.s) ya tambayi manzon Allah (s.a.w) bayan ya gaya masa kamar yadda al’ummar annabi Musa (a.s) da Isa (a.s) ba su bi wasiyyansu ba shi ma al’ummar nan ba zata bi shi ba, ya tambayi manzon Allah (s.a.w) cewa; zan yi wa al’ummar nan hukuncin kafirai ne ko kuma hukuncin wadanda suka fada fitina? Sai manzon Allah (s.a.w) ya amsa masa ya yi musu hukuncin wadanda suka fada fitina ne. Wannan kuwa lallai fitina ce, domin babu bala’in da ya kai ga cewa; Allah ba zai karbi duk ibadojin mutum ba!! A nan ne zamu samu natijar amsar tambayarmu cewa; shin addini yana tare da siyasa. Don haka muna iya gani cewa; asali ma tushensa ya doru ne kan siyasar.

Amma tun da al’umma sun kauce wa siyasar Allah (s.w.t) da manzonsa (s.a.w) da wasiyyansa (a.s) kuma jam’iyyarsu mai cike da tsiran dan’Adam a duniya da lahira wacce take jam’iyya ce ta imani na gaskiya, to mene ne hukuncin sauran jagorori da ake rikonsu a matsayin shugabanni? Kuma mene ne sakamakon da ya samu al’umma sakamakon kauce wa siyasar Allah (s.w.t) da jam’iyyarsa. Kuma me ya kamata wannan al’ummar ta yi game da jagoran gaskiya kuma halifan annabi (s.a.w) na sha biyu da yake wannan ne zamaninsa?
Wannan sai ku biyo mu ba shi idan Allah ya sa mun samu lokaci a nan kusa…
Amma tun da al’umma sun kauce wa siyasar Allah (s.w.t) da manzonsa (s.a.w) da wasiyyansa (a.s) kuma jam’iyyarsu mai cike da tsiran dan’Adam a duniya da lahira wacce take jam’iyya ce ta imani na gaskiya, to mene ne hukuncin sauran jagorori da ake rikonsu a matsayin shugabanni? Kuma mene ne sakamakon da ya samu al’umma sakamakon kauce wa siyasar Allah (s.w.t) da jam’iyyarsa. Kuma me ya kamata wannan al’ummar ta yi game da jagoran gaskiya kuma halifan Annabi (s.a.w) na sha biyu da yake wannan ne zamaninsa?
Musulunci addini ne na tsari wanda bai yarda dan’adam ya zauna haka nan babu daula ba, don haka ne ma ya kasance ya dauki matakin kiyaye tsarin rayuwar al’umma da yake akwai maslaharsu a ciki, sannan kuma sai ya shimfida dokokin da yake kiran su hukunci na biyu wadanda sun saba da na asali. Ina ganin domin fahimtar wannan al’amari yana da kyau mu kawo misalan wasu kissoshi da suka zo a littattafan addini:

1. Wata rana Annabi Ibrahim (a.s) yana tafiya a gaban sarkin da ya so ya kwace matarsa amma ya kasa, wanda daga baya ya ba shi kyautar Hajara babar Annabi Isma’il (a.s) sai suka fito suna tafiya gaban farfajiyar fadar sarkin, sai Annabi Ibrahim (a.s) ya shiga gabansa yana tafiya, sai Allah madaukaki ya yi masa wahayi cewa; ya kai Ibrahim (a.s) ka sani babu makawa al’umma ta samu shugaba nagari ne ko fajiri; abin da ake nufi da nagari a nan shi ne wanda Allah (s.w.t) ya zaba a shar’ance a matsayin jagoran al’umma ko kuma jagoran da yake kiyaye kansa daga haram kuma yake aikata duk wajiban da suke aknsa, kuma yake aiwatar da adalci, fajiri kuwa yana nufin duk wanda yake ba bisa wannan ba.
Sai sarkin ya ga Annabi Ibrahim (a.s) ya koma bayansa yana tafiya, sai ya tambaye shi me ya sa na ga ka koma bayana, sai ya ce: Ubangijina ne ya yi mini wahayi da in girmama ka. Wannan al’amarin ya sanya sarkin ya ga girman Ubangijin Ibrahim (a.s) har ya karkato zuwa gareshi.

kissar Annabi Yusuf (a.s) ba nesa take da mu ba, a cikin kur’ani mai girma yayin da ya nemi a ba shi ministan arziki da albarkatun kasa, don haka ne ma wani wanda ya yi wa Imam Ridha (a.s) rashin kunya yana zarginsa da shiga fadar sarki Ma’amun dan Harunar Rashid, sai Imam Ridha (a.s) ya ba shi amsar da ta sanya shi yin nadama, yana mai nuna masa cewa; tsakaninsa (a.s) da Annabi Yusuf (a.s) ya zabi wanda ya fi laifi a wurinsa yayin da shi Imam Ridha ya karbi sarautar Yarima ne bisa tilas, amma Annabi Yusuf (a.s) ya nemi ministan arziki da albarkatun kasan Misira yana mai rokon sarki ya ba shi wannan matsayi, sannan kuma Imam Ridha (a.s) ya kasance a fadar musulmi ne masu shaidawa da Kadaitar Ubangiji madaukaki, yayin da Annabi Yusuf (a.s) ya zauna a fadar mutane ne da suke bauta wa gumaka!

A nan ne zamu ga muhimmancin kare tsarin al’umma da kuma yin hidima ga al’umma da kiyayewa bisa adalci, mu sani Imam Ali (a.s) yana cewa: “Mulki yana wanzuwa tare da kafirci amma ba ya wanzuwa tare da zalunci”. (Sharhi usululkafi: Mazandarani, j 9, s 300.
Sai dai wani yana iya tambaya cewa; Me ya sa wadannan manyan bayin Allah (s.w.t) guda uku: Annabi Ibrahim (a.s) da Annabi Yusufi (a.s) da Imam Ridha (a.s) suka dauki wadannan matakai, ashe ba hakkinsu ba ne su rike jagorancin al’umma sai kuma suka dauki wadannan matakai a gaban wadannan sarakunan lokutansu?
Sai mu ce: matakai ne da suke sassabawa da sabawar yanayi, don haka ne ma hukuncin Allah a kowane fage da ya hada da siyasa yake sassabawa, misali da Imam Hasan (a.s) ya zo lokacin Imam Husain (a.s) da zai yi yaki ne da Yazid, kamar yadda da Imam Husain (a.s) ne a lokacin Imam Hasan (a.s) to da zai yi sulhu da Mu’awiya. Don haka ne mukan ga wani lokaci Annabi (a.s) ko Imami (a.s) ya dauki matakin da ya saba da na waninsa (a.s) kamar matakin Annabi Isa (a.s) a daular Rum da ya saba da matakin Annabi Musa (a.s) a daular Misira kafinsa da kusan shekaru 1100. Ko kuma Annabi daya ya daukin matakan siyasa da suka saba a lokuta biyu kamar yadda Annabi Ibrahim ya kira sarkin Babil a kan Tauhidi har ya kona shi, amma sai kuma bai yi wannan kiran ba ga sarkin Siriya da na Misira. Kuma muna iya ganin Imam Ali ya yi hakuri ya zauna lafiya da halifofin farko bai dauki matakin yaki ba, amma sai ya dauki wannan matakin tare da Mu’awiya, wanda da ya kyale tabbas da ya zama shugaba a zamaninsa shi ma bayan Usman dan Affan, kuma a zahiri yake wadannan matakai sun sassaba.

Wani yana iya tambaya ya ce: To yaya zamu gane wadannan matakai sai in ce yana da wuya ka gane domin abu ne wanda yake bukatar shiriya daga Allah (s.w.t), kuma mutane sun ki yarda su karbi wannan shiriya don haka duk wani bala’in da suka fada su suka jiyo wa kansu, kuma duk da ba zamu iya ganewa ba saboda wahalar sanin wane yanayi ne, kuma wane mataki ne, kuma a wane lokaci ne, kuma waye zai yi, da sauran wahalhalu da suka dabaibaye wannan lamarin amma wasiyyin Annabi (a.s) na karshe ya zartar da matakan wadanda suka gaje shi suka san koyarwarsa suka dauki ilimi daga abin da ya bari suka kai matakin sani na koli duk da kuwa zai iya kasancewa cike da kurakurai, amma da yake bisa hasken doka ne don haka sai ya kasance kuskure ne wadannan manyan malamai zasu iya yi mai lasisi daga Allah, sabanin wani wanda ba a ba shi lasisi daga Allah ba ko Annabi (s.a.w) ko wasiyyin Annabi (a.s), kuma bai ma san koyarwarsu ba.
Wahalar wannan al’amarin ta kai ga cewa; tun da ake tashi domin gwagwarmayar yakar sarakuna masu mulki a cikin sama da shekaru dari biyu da hamsin na wasiyyan manzo (s.a.w) har zuwa karamar boyuwar wasiyyinsa na sha biyu kuma halifansa na karshe da ya yi albishir da shi, ba mu samu wata gwagwarmayar siyasa ta kifar da daula ba da ta samu goyon baya daga wasiyyan Annabi (a.s) sai ta Mukhtar da ya dauki fansa ga makasan Imam Husain (a.s) shi ma ba yarda ta karara ba ce, sai kuma gwagwarmayar Zaid bn Ali tare da karfafawar da suka yi cewa; ba za a taba samun nasara ba, al’amarin da ya kai ga kashe dukkan wadanda suka tashi suka yi wannan motsin.

Idan mun duba a fili yake cewa shugabannin addini na gaskiya da Allah da manzonsa suka ayyana sun riga sun bayar da matakan da ya dace a dauka na shiryar da al’umma zuwa ga tafarkinsu da tarbiyyarsu ga sanin Allah (s.w.t) da hakkokinsa da kuma hakkokin ‘yan’adam da kuma wadanda suka hau kansu, da kuma komawa zuwa ga malamai masu gadon tafarkinsu kawai banda sauran malaman da suke hana mutane saninsu kamar yadda suka kira su da sunan masu fashin imani wanda ya fi na rayuka da dukiyoyi muni. Kuma su ne zasu nuna yadda za a yi mu’amala da kowane mutum ne tun daga sarakuna da shugabanni da kowane jagoran wata al’umma ba tare da rikon su a matsayin su ne jagororinsu na shiriya ba, don haka rikon wani mutum daban jagora kuma shugaba mai shiryarwa ga tafarki sabaninsu to daidai yake da mutuwar jahiliyya!!!

2- Amma abin da ya samu duniya sakamakon kauce wa siyasar Allah (s.w.t) da jam’iyyarsa wannan wani abu ne da yake a fili, muna iya ganin yadda duniyar dan’adam ta bace kan al’amarin duniya da lahira ta fada cikin alakakai da surkukiya; amma al’amarin lahira a fili yake cewa mutane sun kasa sanin addinin gaskiya ko mazhabar gaskiya suna ta dimuwar da ta fi dimuwar shekaru arba’in ta Banu-Isra’ila muni, domin dimuwar yau ta rashin sanin gaskiya ce, wannan kuwa sakamakon ‘yan fashi da suka yi yawa a kan hanyar isa zuwa ga Allah madaukaki ne, sannan kuma dimuwa ce da ba wanda ya san sanda zata kawo karshe. Don haka kamar yadda suka dimauce kan al’amarin lahira ta yadda suke bin kowane irin kira doo. Haka nan ma suka dimauce kan lamarin duniyarsu ta yadda babu wani wanda ya isa ya fitar da duniya daga dimuwarta ta al’adu da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da tarbiyya da makamancinsu ta yadda zai fito da ma’anar adalci a kowane fage wanda yake nufin gaskiya a komai ba tare da tauyewa ba sai wanda yake ya san Allah (s.w.t) hakikanin sani wanda kuma babu wani wanda yake haka sai wanda Allah (s.w.t) ya zaba na annabi (s.a.w) ko kuma wasiyyinsa (a.s), amma su ma da sharadin al’umma ta yarda da jagorancinsu.

Amma abin da ya yake cikin tunanin wasu masu ganin cewa don me ya sa Annabi (s.a.w) ko kuma imami (a.s) bai dauki wasu matakai ba na shari’a? sai mu ce duk wannan yana komawa ne zuwa ga rashin yardar mutane; Misali me ya sa jagororin da manzon Allah (s.a.w) ya yi wasiyya da su ba su riki jagoranci ba? Sai mu ce: yana daga sharuddansu mutane su yarda da su sannan sai su riki jagorancin al’umma. Muna iya ganin yawancin annabawa (a.s) ba su riki jagorancin al’umma ba na tafiyar da mulkinsu saboda al’ummar ba ta yarda ba, don haka ne ma zabe yake da muhimmanci a wannan zamani namu, kuma shari’a ta ki yarda da wani ya jagoranci mutane koda kuwa annabi (a.s) matukar mutanen ba sa so.
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Allah ya tsinewa mutumin da ya jagoranci mutane alhalin ba sa sonsa.

Don haka ne ma Imam Ali (a.s) ya ki jagoranci saboda mutane ba su zabe shi ba, amma da suka zabe shi ya riki mulki kuma da wani ya tashi domin ya kwata daga gareshi sai ya yake shi da mutanen.
Mulki a hannun bayin Allah (s.w.t) nagari da ya zaba ita ce hanyar shiryar da bayi, don haka idan suka ki Allah madaukaki bai yarda a tilasta su ba. Amma kuma idan mutane suka ki yarda da zabin Allah (s.w.t) -duk da Allah ya kyale su bai yarda a tilasta su karbar wanda ba sa so ba- amma bala’o’in duniya da na lahira zasu durfafe su.
Mu duba mu gani mana a lokutan jagorancin manzon rahama (s.a.w) da Imam Ali (a.s) ba a taba samun wani ya mutu da yunwa ko talauci ba, kuma ba a samu yawaitar jahilci da rashin tsaro ba, kuma ba a samu karancin abinci da yunwa ba saboda tsarin da suka zo da shi a hukumarsu duk da kuwa kowannensu hukumarsa cike take da yake-yake!

Muna iya gani abin da Imam Ali (a.s) ya yi yayin da ya ga wani tsohon bayahude a hanya a Kufa yana bara sai ya tambaya ya ce: me ye haka! Mu duba mu gani bai ce wane ne wannan ba, sai ya ce mene ne wannan, wato bakon abu ne a daularsa a samu bara. Sai ya yi fada kan cewa; wannan bayahuden ya yi wa mutane ayyuka yana saurayi sai da ya tsufa sannan sai a kyale shi!? sannan ya sanya masa albashi daga Baitul mali!
Me kuwa zai sanya dan’adam ba zai wahala ba alhalin ya kauce wa tsarin da zai fisshe shi daga bala’in duniya da lahira, mu sani duk duniya babu wani wuri da ake bin tsarin addinin musulunci kamar yadda Allah (s.w.t) da manzonsa (s.a.w) suka zo da shi, wani wurin ana gaba da addini ne, wani wurin kuma ana jahiltarsa ana yin wani abu daban da sunan addini amma addini ba haka ya ce ba, ba komai ake yi ba sai fahimtar mutanen wurin game da addini. Wani wurin kuma an fahimci addin kamar yadda manzo (s.a.w) da wasiyyansa (a.s) suka zo da shi, amma fa al’adu sun hana a aiwatar da shi. Wannan sai ya sanya duk duniya ba inda ake yin addini koda kashi 50% cikin dari a duk fadin wannan duniyar.

Wasu sun dauka an zo duniya domin shan wahala ne don haka sai suka dauka wahalar da ake sha da ma haka duniya take! wannan lamarin kuwa ya taso daga jahilcin dan’adam ne, ko kuma daukar da ya yi wa abin da yake faruwa kamar daman haka ya dace ya faru! Mu sani duniya da lahira duka an yi su domin samun kamalar dan’Adam ne, bambancin al’amarin shi ne akwai wahalar ibada a wannan duniya. Kuma rashin lafiya da cututtuka duka Allah ya bayar da maganinsu sai dai dan’adam ya nisanci wanda zai yi masa maganin ne. Sannan muna ganin yadda manzon Allah (s.a.w) da Imam Ali (a.s) suka yaki talauci da yunwa ta karfin tsiya da kuma kawo aminci da ilimi da tarbiyya da sauransu. Imam Ali (a.s) yana cewa: Da talauci mutum ne da na kashe shi (Sharhu Ihkakul hakk: J 32, shafi: 257)
Arzikin duniya ya ishi dan’adam amma ya wanzu a bankunan masu mulki da iko ana boye shi ana juya shi, kuma wannan lamarin shi ne abin da Allah ya yi gudunsa yana mai cewa; “…domin kada ya kasance yana juyawa tsakanin mawadata daga cikinku…”(Hashari: 7), amma dan’adam da aka yi arzikin saboda shi sai ya kwana cikin yunwa da musibu da talauci.

Amma batun cewa; me ya kamata wannan al’ummar ta yi game da jagoran gaskiya kuma halifan annabi (s.a.w) na sha biyu da yake wannan ne zamaninsa?
Kuma me ya kamata wannan al’ummar ta yi game da jagoran gaskiya kuma halifan annabi (s.a.w) na sha biyu da yake wannan ne zamaninsa?
3- Amma abin da ya kamata wannan al’ummar ta yi game da jagoran gaskiya kuma halifan annabi (s.a.w) na sha biyu da yake wannan ne zamaninsa shi ne ta koma zuwa ga koyarwarsa, ta san wane ne shi sannan sai ta san wadanda ya ce ta koma musu wajen sanin addininsu, to da wannan ne zasu iya zama ‘yan jam’iyyar Allah madaukaki.
Da wannan ne zasu koma zuwa abin da ya fada a littafinsa: “Kawai hukunci na Allah ne” (al’an’ami: 57). Da fadinsa: “…Hukunci nasa ne…” (al’kasas: 88). Da kuma dukkan ayoyin da suka yi nuni da fasikanci ko kafirnci ko zaluncin wanda bai yi hukunci da abin da Allah ya saukar ba, da wannan ne sai su aikta ayyukan da suke kansu na mu’amala da dukkan wani dan’adam bisa yadda shari’a ta ce musu kamar yadda ya zo daga wajen Allah madaukaki. Sai ya kasance alakokinsu da kowa bisa yadda Allah ya so ne kuma jagoransu na wannan zamani ya tsara ya nuna musu. Da wannan ne zasu kasance ‘ya’yan jam’iyyar Allah madaukaki wacce take da sakamakon yardarsa duniya da lahira.

Irin wadannan malamai da suke bin tafarkin Allah madaukaki da manzonsa (s.a.w) da wasiyyansa (a.s) su ne wadanda manzon rahama (s.a.w) yake cewa: “…hakika malamai magada annabawa ne” (kafi: j2, sawabul ilm, hadisi: 1) da fadin Imam Ali (a.s) cewa; “Malamai su ne masu jagorancin mutane” (Gurarul hikam: 137), da fadin manzon Allah (s.a.w) da yake nuna cewa; idan malamai suka bata to zasu batar da wannan al’umma.
Wani abin mamaki shi ne yadda wasu malamai suka ki fahimtar al’amarin jagoran al’umma bisa gurbatacciyar fahimta sakamakon kaucewa wasiyyar da annabi (s.a.w) ya yi na su bi abin da yake kunshe cikin Kur’ani bisa fahimtar ahlin gidansa (a.s) wadanda Allah madaukaki ya tsarkake su kuma manzon Allah (s.a.w) bai bar wannan duniya ba sai da ya yi wasiyya da su kamar yadda muka yi nuni a baya da halifofinsa goma sha biyu ne kamar yadda ya kawo su kuma ya yi wasiyya da su.

Wani abin mamaki shi ne yadda wasu sukan yi kokarin su boye wasiyya ko su yi musunta, ko kuma su daukar wa kansu yarda da cewa; manzon Allah (s.a.w) ya fadi sha biyu amma bai kawo sunayensu ba, don haka sai su shiga neman kawo sunayen da kansu kamar dai Allah ya yi wahayi cewa; manzonsa (s.a.w) ba zai cika addininsa su ne zasu zo daga baya su cika. Irin wannan son rai yana nan kunshe cikin littattafai daga wasu masu irin wadancan mahanga ta su cika addini da kansu! Allah ya tsare mu tabewa!
Mu sani cewa; tafiyar da al’amarin siyasa da jagorancin al’umma abu ne na wadanda Allah ya zaba ya mika musu ya sanya shi a hannunsu wadanda muka ce imma dai annabi (a.s) ko kuma wasiyyin annabi (a.s) idan kuwa ba haka ba to wanda ya hau wannan mahalli a wajen Allah sunansa fajiri fasiki komai kuwa takawarsa ta zahiri, domin ma’aunin da muke hange da shi, shi ne dai ma’aunin da Allah yake hange da shi.

Idan kuwa yana son kada wannan suna ya hau shi to kada ya sake ya hau wannan mataki sai idan annabi (a.s) ko wasiyyin annabi (a.s) ko kuma wanda wasiyyin annabi (a.s) ya ce ya hau wannan matsayin sakamakon ba a gane shi a fili koda kuwa an gan shi, sai ya mayar da mutane zuwa ga malamai masu wasu siffofin da shi ya ayyana su da kansa da shiryarwar ubangijinsa madaukaki da kuma ta annabin rahama (s.a.w).
Imam Ali (a.s) yana cewa da alkali shuraihu: Ya shuraihu ka zauna a mazaunin da babu mai zama a wurin sai annabi (a.s) ko kuma wasiyyin annabi (a.s) ko kuma tababben tsinannen mutum (al’wasa’il: babin hukunci: babi 2, h 2, shafi: 6). Kamar yadda Imam sadik (a.s) yake cewa: Ku ji tsoron mulki domin shi mulki na malami ne masani da hukunci da adalci wanda yake shi ne annabi (a.s) ko kuma wasiyyin annabi (a.s) (Daga al’wasa’l: kamar na bayansa). Don haka ne ma ake fassara ma’anar malamai a irin wadannan hadisai da annabi (a.s) ko kuma wasiyyin annabi (a.s).

Amma hanzari ba gudu ba: Dayawan malamai sun tafi a kan cewa; idan aka samu wani mumini da yake karbar shawara daga malamai wadanda suke kan tafarkin manzon Allah (s.a.w) da koyarwarsa sahihiya (a.s) ya kasance yana karbar shiryarwa da yadda zai tafiyar da al’amuran al’ummarsa daga garesu to wannan ya fita daga cikin wannan tabewa kuma irin wadannan mutane ba sa ciki saboda su ma yanzu suna karkashin umarnin Allah da manzonsa da wasiyyansa da kuma malamai mabiyansu ne, kuma sun fita daga sunan fajirci, ko dagutanci.

Kamar yadda malamai suka yi fahimta ga hadisin da yake cewa duk wata tuta da aka daga (wato duk wata gwagwarmaya da ake yi) kafin bayyana Sufyani to ta dagutu ce (wato; ba halattacciya ba ce), wasu malamai sun tafi a kan hakan, amma muna iya ganin Imam khomain (k) jagoran juyin musulunci a Iran a 1979, yana ganin hadisin bai hada da tutar da aka daga kuma ta kasance ba ta saba da koyarwarsu ba, sai ya kasance kenan ya halatta malamin da yake bin hanya sahihiya da sharadin ya samu lasisin wasiyyan annabi (a.s) zai iya yin wani motsi bisa sharuddan da suka gindaya. Sai ya kasance wannan kauce hanya bai hada har da shi ba, wannan dai mas’ala ce mai girma da ta tayar da jijiyar wuya saboda santsinta da kuma wahalarta kamar yadda dai sauran mas’alolin siyasa suke. Kuma nan ba zauren karatu ba ne balle mu fadada magana.