Saturday, 31 May 2014

IZALA DA TAWASSULI DA ANNABI (s.a.w.w)

HUKUNCIN YIN TAWASSILI DA ANNABI KO DARAJAN ANNABI KO WANI SALIHIN BAWA 

♥ ♥ بسم الله الرحمن الرحيم Sauda dama nakanji mutane suna addu‘ah da cewa (ya Allah ka bamu abu zaka... Don darajan annabi (saw) ko makamanci haka, Wanda hakan yasa naga ya kamata ayi ma mutane matashiya don wani ji kawai yake ana fad be san ingancin hakan ko rashinsa ba, Kai tsaye malaman muslunci sun tabbar da cewa ba‘a tawassli da wani mutum don darajansa ko matsayinsa ko fifikonsa acikin mutane koda kuwa annabin Allah (saw) kuma (hakan bai nuna annabi bashi da wani daraja ba a‘a yana dashi marar misaltuwa,) Malaman sunnah suka ce yin hakan ya sa6a koyarwan annabi (saw) Sai-dai ana iya yin tawassili da addu‘an annabi ko wani salihin bawa cikin bayin Allah (wato: in kana buQan abu awajen Allah ya halatta kaje wannan wani bawa salihi kayi kamun Qafa dashi ya maka addu‘a wanda hakan ake kira da TAWASSILI) Malaman sunnah suna kafa hujja da wasu hadisai ingantattu daga cikin akwai wannan hadisi wanda imamul bukhari ya rawaito... وعن أنس أن عمر رضي الله عنه كان إذا قحطوا استسقى بالعباس بن عبد المطلب وقال; أللهم إنا كنا نستسقى إليك (بدعاء) نبينا فتسقينا, وإنا نتوسل إليك (بدعاء) عم نبينا فاسقنا, فيسقون (ma‘ana) anas (ra) yace umar dan-khattab ya kasance in an samu fari (babu ruwan sama) sukanyi kamun Qafa da Abbas dan-abdul‘muddalib sai suce ya Allah da mu kasance muna tawissili da (addu‘an) annabin ka saika shayar damu to yanzu (tunda annabi baya nan) muna tawassili da addu‘an baffan annabinka ya Allah ka shayar damu (sai su daga hannu sama suce Abbas kayi addu‘ah su kuma suna cewa amin) Me sharhin wannan hadisi yake cewa وفى عمل عمر هذا هدم لعقيدة المبتدعة القاءلين بالتوسل بالموتى من اﻷنبياء والصلحين إلى الله, فما من شك أن عمر والصحابة كانوا يعلمون أن النبي (ص) هو أفضل الخلق عند الله حيا و ميتا, وأن مكانته عند ربه لم تنقص بالموت بل زادت, فالتوسل بالنبي (ص) إنما كان بدعاءه فى حياته لا بجاهه, كما أن التوسل بالعباس إنما بدعاءه لا بجاهه, (Ma‘ana) Yace wannan abu da sayyadina umar ya aikata yana nuna martani/raddi ne ga masu aQidar cewa ana iya tawassili da mamata cikin annabawa ko salihan bayi (wato kamun Qafa dasu zuwa ga Allah) Kuma babu shakku akan cewa umar (r.a) da sauran sahabbai duka sun san babu wani mutum me falala da daraja awajen Allah sama da annabi (saw) acikin rayuwansa dama bayan mutuwan sa. Kuma matsayin awajen ubangijinsa bai ragu ba sai dai ma Qaruwa yayi, amma duk da haka basuje kabarinsa sukayi kamun Qafa dashi ba, Kuma anan tawassli (kamun Qafa) da sukayi da annabi ana nufin da addu‘an annabi ne bada zatinsa (jahi) ba alokacinda yake raye Hakama shi abbas bada zatinsa ko (jahinsa) suka yi tawassili ba a‘a da addu‘ansa ne, Abunda mallam yake nuna mana anan shene Duk da cewa sahabbai sunsai babu mafi falala kamar annabi amma basa tawassili dashi sai-dai kawai sukai masa kukansu ya roQa musu Allah, Kuma inda ana tawassli da annabi ko wani salihin bawa a bayan mutuwansa ai da sayyadina umar beje gun abbas ya musu addu‘ah ba Tunda ga kabarin annabi acikin garin madina da saiyaje kawai, Misalan suna da yawa.
HUKUNCIN YIN TAWASSILI DA ANNABI KO DARAJAN ANNABI KO WANI SALIHIN BAWA ♥ ♥

بسم الله الرحمن الرحيم

Sauda dama nakanji mutane suna addu‘ah da cewa (ya Allah ka bamu abu zaka... Don darajan annabi (saw) ko makamanci haka,
Wanda hakan yasa naga ya kamata ayi ma mutane matashiya don wani ji kawai yake ana fad be san ingancin hakan ko rashinsa ba,

Kai tsaye malaman muslunci sun tabbar da cewa ba‘a tawassli da wani mutum don darajansa ko matsayinsa ko fifikonsa acikin mutane koda kuwa annabin Allah (saw) kuma (hakan bai nuna annabi bashi da wani daraja ba a‘a yana dashi marar misaltuwa,)

Malaman sunnah suka ce yin hakan ya sa6a koyarwan annabi (saw)
Sai-dai ana iya yin tawassili da addu‘an annabi ko wani salihin bawa cikin bayin Allah (wato: in kana buQan abu awajen Allah ya halatta kaje wannan wani bawa salihi kayi kamun Qafa dashi ya maka addu‘a wanda hakan ake kira da TAWASSILI)

Malaman sunnah suna kafa hujja da wasu hadisai ingantattu daga cikin akwai wannan hadisi wanda imamul bukhari ya rawaito...
وعن أنس أن عمر رضي الله عنه كان إذا قحطوا استسقى بالعباس بن عبد المطلب وقال; أللهم إنا كنا نستسقى إليك (بدعاء) نبينا فتسقينا, وإنا نتوسل إليك (بدعاء) عم نبينا فاسقنا, فيسقون

(ma‘ana) anas (ra) yace umar dan-khattab ya kasance in an samu fari (babu ruwan sama) sukanyi kamun Qafa da Abbas dan-abdul‘muddalib sai suce ya Allah da mu kasance muna tawissili da (addu‘an) annabin ka saika shayar damu to yanzu (tunda annabi baya nan) muna tawassili da addu‘an baffan annabinka ya Allah ka shayar damu (sai su daga hannu sama suce Abbas kayi addu‘ah su kuma suna cewa amin)

Me sharhin wannan hadisi yake cewa
وفى عمل عمر هذا هدم لعقيدة المبتدعة القاءلين بالتوسل بالموتى من اﻷنبياء والصلحين إلى الله, فما من شك أن عمر والصحابة كانوا يعلمون أن النبي (ص) هو أفضل الخلق عند الله حيا و ميتا, وأن مكانته عند ربه لم تنقص بالموت بل زادت,
فالتوسل بالنبي (ص) إنما كان بدعاءه فى حياته لا بجاهه, كما أن التوسل بالعباس إنما بدعاءه لا بجاهه,
(Ma‘ana)
Yace
wannan abu da sayyadina umar ya aikata yana nuna martani/raddi ne ga masu aQidar cewa ana iya tawassili da mamata cikin annabawa ko salihan bayi (wato kamun Qafa dasu zuwa ga Allah)
Kuma babu shakku akan cewa umar (r.a) da sauran sahabbai duka sun san babu wani mutum me falala da daraja awajen Allah sama da annabi (saw) acikin rayuwansa dama bayan mutuwan sa.
Kuma matsayin awajen ubangijinsa bai ragu ba sai dai ma Qaruwa yayi, amma duk da haka basuje kabarinsa sukayi kamun Qafa dashi ba,

Kuma anan tawassli (kamun Qafa) da sukayi da annabi ana nufin da addu‘an annabi ne bada zatinsa (jahi) ba alokacinda yake raye
Hakama shi abbas bada zatinsa ko (jahinsa) suka yi tawassili ba a‘a da addu‘ansa ne,

Abunda mallam yake nuna mana anan shene
Duk da cewa sahabbai sunsai babu mafi falala kamar annabi amma basa tawassili dashi sai-dai kawai sukai masa kukansu ya roQa musu Allah,

Kuma inda ana tawassli da annabi ko wani salihin bawa a bayan mutuwansa ai da sayyadina umar beje gun abbas ya musu addu‘ah ba
Tunda ga kabarin annabi acikin garin madina da saiyaje kawai,

Misalan suna da yawa.
♥ ♥

بسم الله الرحمن الرحيم

Sauda dama nakanji mutane suna addu‘ah da cewa (ya Allah ka bamu abu zaka... Don darajan annabi (saw) ko makamanci haka,
Wanda hakan yasa naga ya kamata ayi ma mutane matashiya don wani ji kawai yake ana fad be san ingancin hakan ko rashinsa ba,

Kai tsaye malaman muslunci sun tabbar da cewa ba‘a tawassli da wani mutum don darajansa ko matsayinsa ko fifikonsa acikin mutane koda kuwa annabin Allah (saw) kuma (hakan bai nuna annabi bashi da wani daraja ba a‘a yana dashi marar misaltuwa,)

Malaman sunnah suka ce yin hakan ya sa6a koyarwan annabi (saw)
Sai-dai ana iya yin tawassili da addu‘an annabi ko wani salihin bawa cikin bayin Allah (wato: in kana buQan abu awajen Allah ya halatta kaje wannan wani bawa salihi kayi kamun Qafa dashi ya maka addu‘a wanda hakan ake kira da TAWASSILI)

Malaman sunnah suna kafa hujja da wasu hadisai ingantattu daga cikin akwai wannan hadisi wanda imamul bukhari ya rawaito...
وعن أنس أن عمر رضي الله عنه كان إذا قحطوا استسقى بالعباس بن عبد المطلب وقال; أللهم إنا كنا نستسقى إليك (بدعاء) نبينا فتسقينا, وإنا نتوسل إليك (بدعاء) عم نبينا فاسقنا, فيسقون

(ma‘ana) anas (ra) yace umar dan-khattab ya kasance in an samu fari (babu ruwan sama) sukanyi kamun Qafa da Abbas dan-abdul‘muddalib sai suce ya Allah da mu kasance muna tawissili da (addu‘an) annabin ka saika shayar damu to yanzu (tunda annabi baya nan) muna tawassili da addu‘an baffan annabinka ya Allah ka shayar damu (sai su daga hannu sama suce Abbas kayi addu‘ah su kuma suna cewa amin)

Me sharhin wannan hadisi yake cewa
وفى عمل عمر هذا هدم لعقيدة المبتدعة القاءلين بالتوسل بالموتى من اﻷنبياء والصلحين إلى الله, فما من شك أن عمر والصحابة كانوا يعلمون أن النبي (ص) هو أفضل الخلق عند الله حيا و ميتا, وأن مكانته عند ربه لم تنقص بالموت بل زادت,
فالتوسل بالنبي (ص) إنما كان بدعاءه فى حياته لا بجاهه, كما أن التوسل بالعباس إنما بدعاءه لا بجاهه,
(Ma‘ana)
Yace
wannan abu da sayyadina umar ya aikata yana nuna martani/raddi ne ga masu aQidar cewa ana iya tawassili da mamata cikin annabawa ko salihan bayi (wato kamun Qafa dasu zuwa ga Allah)
Kuma babu shakku akan cewa umar (r.a) da sauran sahabbai duka sun san babu wani mutum me falala da daraja awajen Allah sama da annabi (saw) acikin rayuwansa dama bayan mutuwan sa.
Kuma matsayin awajen ubangijinsa bai ragu ba sai dai ma Qaruwa yayi, amma duk da haka basuje kabarinsa sukayi kamun Qafa dashi ba,

Kuma anan tawassli (kamun Qafa) da sukayi da annabi ana nufin da addu‘an annabi ne bada zatinsa (jahi) ba alokacinda yake raye
Hakama shi abbas bada zatinsa ko (jahinsa) suka yi tawassili ba a‘a da addu‘ansa ne,

Abunda mallam yake nuna mana anan shene
Duk da cewa sahabbai sunsai babu mafi falala kamar annabi amma basa tawassili dashi sai-dai kawai sukai masa kukansu ya roQa musu Allah,

Kuma inda ana tawassli da annabi ko wani salihin bawa a bayan mutuwansa ai da sayyadina umar beje gun abbas ya musu addu‘ah ba
Tunda ga kabarin annabi acikin garin madina da saiyaje kawai,

Misalan suna da yawa.

AN KAFA KUNGIYAR IZALA NE DON...

AN KAFA KUNGIYAR IZALAH NE SABODA KAUDA BIDI'AH DA KUMA TSAIDA SUNNAR ANNABI MAI TSIRA DA AMINCIN ALLAH


AN KAFA KUNGIYAR IZALAH NE SABODA KAUDA BIDI'AH DA KUMA TSAIDA SUNNAR ANNABI MAI TSIRA DA AMINCIN ALLAH
27/3/2013

'Yan'uwa Musulmi masu kaunar Sunnah! Muna kara tunatar da ku cewa lalle an kafa Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'iah Wa Iqamatis Sunnah ne a 1978 saboda a kauda dukkan wata bidiah da aka cusa cikin addinin Musulunci da sunan neman wata fa'ida a wurin Allah, sannan kuma a tsaida sunnar Annabi mai tsira da aminci cikin dukkan Aqiidah, da dukkan Ibaadah, da dukkan Mu'aamalah. Wannan shi ne dalilin kafa Kungiyar Izalah, kuma wannan ita ce manufar Izalah.

Saboda haka duk mutumin da ya ce an kafa kungiyar izala ne saboda kare wata mazhaba daga cikin mazhabobi, ko saboda kare muradun wani mutum daga cikin mutane, to lalle wannan mutum bai fadi gaskiya ba, lalle wannan mutum ya shara wa Kungiyar Izala karya, lalle wannan mutum ya ci amanar mutanen da suka hadu suka kafa wannan Kungiya tamu mai albarka.

Kuna iya fahimtar cewa duk wata mazhaba da ta saba wa nassin hadithin Manzon Allah, ko ta saba wa wani zahirin hadithin manzon Allah, cikin wata mas'ala daga cikin mas'aloli, to babu ruwan Kungiyar izala da bin wannan mazhabar cikin wannan mas'alar, a'a abin da Kungiyar Izala take yi shi ne: Sai ta bi nassin wannan hadithin, ko zahirin wannan hadithin ta bar abin da wancan mazhabar ta fada, saboda imanin da kungiyar take da shi na cewa ba a aiko mana da kowa ba cikin maluman wadannan mazhabobi, a'a wanda kawai Allah Ya aiko mana a matsayin Manzo shi ne: Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah.

Ga misali daya tak zan ba ku a wannan darasi namu: Tun da aka kafa wannan Kungiya tamu ta Izala, kungiyar take ta yin yaki da daura layu da guraye, kuma take ta bayyana wa al'ummar Duniya cewa daura laya shirka ce, hujjarta kuwa a kan wannan magana nata ita ce: Hadithan Manzon Allah da suka inganta cikin wannan mas'alar, kamar hadithin:-
((من تعلق تميمة فقد اشرك)).
Ma'ana: ((Duk wanda ya rataya laya to hakika ya yi ahirka)). Intaha.
A nana Annabi bai banbanta tsakanin layar da Alkur'ani ko wani ambaton Allah yake cikinta da kuma wacce babu wannan a cikinta ba, saboda haka Kungiyar izala ta yi aiki da umumi ta haramta dukkan abin da za a kira Laya.

Da luma hadithin:-
((ان الرقى والتمائم والتولة شرك)).
Ma'ana: ((Lalle Tawaida-tawaida, da kuma Layu, da Abubuwan sanya soyayya ko kiyayya tsakanin namiji da mace, shika ne)). Intaha.

Kungiyar Izala ta ci gaba da yakar layu dare da rana duk kuwa da cewa a mazhabar Malkiyyah halal ne mutum ya daura laya ko gurun da yake dauke da wasu ayoyin Alkur'ani ko kuma wasu kalmomi na ambaton Allah, kamar yadda ya zo cikin littattafan fikhun Malikiyyah kamar haka:-
1. Ya zo cikin Alfawaakihud Dawaanii sharhin Risalah t1/340 kamar haka:-
((ولا باس بالمعاذة وفيها القران)) 
Ma'ana: ((Babu laifi a daura layar da Alkur'ani yake cikinta)). Intaha.
2. Ya zo cikin Jawaahirul Ikliil sharhin Mukhtasar 1/21 kamar haka:-
((وحرز بساتر وان لحائض)).
Ma'ana: ((Layar da baduku ya rufa ta da fata halal ne a rataya ta, koda kuwa mace ce mai haila)). Intaha.
3. Ya zo cikin As'halul Madaarik kamar haka:-
((يجوز تعليق التمائم وهي العوذة التي تعلق على المريض والصبيان وفيها القران وذكر الله تعالى اذا خرز عليها جلد ويجوز تعليقها على المريض والصحيح خوفا من المرض والعين)).
Ma'ana: ((Yana halatta rataye layu, watau abin tsarin da ake rataya wa mara lafiya da kuma yara, alhali akwai Alkur'ani ko ambaton Allah Madaukaki a cikinsu, matukar dai an rufa layun da fata. Kuma rataya su na halatta ga mara lafiya, da ma wanda yake mai lafiya ne, saboda tsoron kada ya kamu da rashin lafiya ko kambun baka)). Intaha.

'Yan'uwa Musulmi masu kaunar Sunnah! Wannan ita ce Kungiyar Izala, sam ba ta barin abin da ya tabbata a cikin sunnar Annabi mai tsira da amincin, sannan ta koma ta yi riko da fatawar wata mazhaba daga cikin mazhabobi. 
Kuma Wannan shi zai tabbatar muku da cewa: Dukkan mutumin da za ku ji shi yana kyamar sahihiyar sunnar Manzon Allah cikin wata mas'ala yana cewa mu malikiyyah ne saboda haka mu abin da yake rubuce cikin mazhabar malkiyyah kadai za mu bi, domin ai su ma maluman Malikiyyan sun san da wancan hadithin amma kuma suka ki bin shi, saboda haka mu ma a nan da su za mu yi ko yi domin su ma ai magabata ne!! 
Lalle duk wanda kuka ji yana irin wadannan maganganu na shakiyanci da rashin mutunta sunnar Annabi, to lalle ku tabbatar da cewa ba dan izala ba ne na gaskiya, lalle ku tabbatar da cewa shi wannan shakiyyin mutum ya ci amanar Kungiyar Izala.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya tabbatar da dugaduganmu a kan sunnar Annabi mai tsira da aminci. Ame

KUNGIYAR IZALA CE TA DAWO DA RUHIN ADDINI A ZUKATAN AL'UMMAR NAJERIYA (



KUNGIYAR IZALA CE TA DAWO DA RUHIN ADDINI A ZUKATAN AL'UMMAR NAJERIYA (1)
Daga Yasir Ramadan Gwale, Kano State.
Kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa'Iqamatus Sunnah, kungiya ce da aka kafata domin kawar da dukkan bi'di'o'in da aka jinginawa addinin Musulunci tare da tabbatar da cikakkiyar koyarwa Addinin Musulunci a bisa tsarin koyarwar Al-Qur'ani da Hadisan Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam Ingatattu, da kuma fahimtar magabata na kwarai. Kungiyar Izala kungiya ce da ta kunshi hazikan Malamai wadan da suka karantu suka san Addinin Musulunci kamar Yadda Manzon Allah Ya zo da shi.
Kusan wannan kungiya mai albarka ta kafu ne karkashin Jagorancin marigayi Shiekh Abubakar Mahmoud Gumi (Rahimahullah).­ Da Wasu Malamai da Shuwagabanni.
Sheikh Gumi yayi ta fadi tashin ganin an koyar da al'umma addinin Musulunci na hakika ba wai a Najeriya kadai ba a kusan daukacin kasashen yammacin Afurka. Cikin ikon Allah tare da taimakonsa ne Shiekh Gumi da'awarsa tayi nasara sosai, ya bayar da fatawoyin da suka fitar da al'ummar Musulmi daga duhun Jahilci da saita su akan hanya mikakkiya ta kitabu da Sunnah.
Sanin kowa ne cewar kafin bayyanar Izala, al'ummar Musulmi musamman na Arewacin Najeriya sun tasirantu da ayyukan addini da suka saba da hakikanin koyarwar Al'qur'ani da Hadisai Ingatattu. Wannan ce ta sanya dole kungiyar ta samu tirjiya daga mutanan da suka jima suna aikata Bidi'ah wanda suke zaton Addini suke yi. A karon farko anki yadda a fahimci hakikanin abinda IZALA ta zo da shi da gangan da ganganci, dan wadan da suka fahimci hakikanin abinda Izala ta zo da shi sun san cewa idan har al'ummar Musulmi suka fahimci koyarwar addini ta hakika karkashin Izala to la shakka kashinsu ya bushe kuma kasuwarsu ta kare, wannan ce ta sanya suka kasa zaune suka kasa tsaye wajen kira ga magoya bayansu kada su kuskura su saurari Malaman Izala, rahotanni sun nuna cewa wasu malaman sukan fadawa Mabiyansu cewa duk inda kaga Dan Izala yana wa'azi gwargwadon gudunka da shi gwargwadon ladan da zaka samu! Allahu akbar.
A gari irin kano wanda yake ciki da manyan Shehunnan dariqun sufaye kungiyar Izala ta fuskanci tirjiya mai girman gaske. A wasu lokuta ankai ruwa rana sosai tsakanin Malaman Izala masu wa'azi da al'ummar unguwanni da suke ganin babu dalilin da zai sanya a kyale su suyi wa'azi. Domin a lokacin anyi ta gayawa mutane karairayin cewa 'Yan Izala wasu mutane ne masu Gemu da dagaggen wando da suke Zagin Iyayan Manzon Allah (Wal'Iyazubilla­h). Wannan ta sanya Malaman Izala suka sha bakar wahala kafin samun damar fara yin wa'azi a cikin unguwannin Birnin Kano da kewaye.
Kasancewar KANO gari mafi yawan jama'a a fadin Arewa, kuma al'umma masu matukar kaunar duk wani abu da ya shafi addini, ya sanya Kano ta zama wani muhimman filin daga ga kungiyar Izala. Unguwanni irinsu Fagge Masallacin Triumph da irinsu Burged da jami'ar Bayero suna daga cikin guraran farko da suka fara cin gajiyar koyarwar Izala a jihar Kano. Amma unguwannain cikin birni an samu tirjiya mai girman gaske, takai jallin da an daddaki wasu Ustazai an sassari wasu da adduna an farfasa musu lasifikoki kai abin har ya kai da kona tare da yin kashi a cikin Masallaci a cikin birnin Kano. Masallacin 'Yan Rariya dake filin Mushe a Karamar Hukumar Gwale yana daga cikin masallatan Izala na farko farko a cikin birnin Kano, an shafe lokaci mai tsawo ana yin kashi da zuba shara a cikin masallacin, laifinsu kawai shine sunyi Sallar Azahar karfe daya na Rana!
Haka kuma, idan muka kalli Jami'ar Bayero kusan nanne inda Izala bata samu wata tirjiya ba wajen yin wa'azi. Wannan kuwa baya rasa nasaba da cewa Dalibai da malamai na Jami'ah suna da cikakkiyar wayewa ta fahimtar rayuwa da fahimtar inda duniya ta sanya a gaba, dan haka ne Masallacin Jami'ar ya zama wani dandalin Izala a cikin kwaryar birnin Kano. Masu magana sukance Duniya Labari, yanzu Izala har a tsakiyar Tudun Nufawa da Makwarari da Madabo da Kofar Wambai da sauran unguwanni na cikin birnin Kano.
Wannan ne dalilin da ya sanya wasu daga cikin Malaman da suke ganin Izala matsala ce a garesu idan har al'umma suka fahimce su suka fara saduda tare da zubawa sarautar Allah ido. Amma kuma dole wasu suka tashi haikan wajen bincike da Nazarin Ilimin addinin Musulunci, domin tsira da mutunci dan kada mutanan da sukewa kallon yara matasa su ringa kuresu tare da tsiraita iliminsu.
Bayan kafuwar Izala, ta assasa WA'AZIN KASA wanda ake hada kafatanin Malaman da suke Izala a wata jiha domin yin wa'azi tare da kira zuwa ga Al-Qur'ani da Sunnah. Wannan wa'azi da Izala take yi yayi tasiri kwarai da gaske wajen janyo hankulan mutane, tare kuma da sanya 'yan uwantaka ta addini a tsakanin Ustazai. Wani abin sha'awa shine a duk lokacin da Izala ta shiga wata Jiha domin yin wa'azi to shakka babu mutanan wajen da za'ayi wa'azin sukan samu habakar tattalin arziki, domin masu kankanan sana'o'i kanyi ciniki sosai na hajojinsu, a filin wa'azi wani Ustazu zai zo ya karkace ya kirawo Me Ganda ya saye daron gaba daya yace a yankawa jama'a suci su sha romo, wannan ko shakka babu ya kara karfin 'yan uwantaka ta addini a tsakanin Matasa.
Yasir Ramadan Gwale
07-06-2013

TARIHIN SHEKH MAHMUD GUMI

An haifi Shaikh Abubakar Mahmud Gumi (R.A) ne a cikin garin Gumi a Jahar Sakkwato a Arewacin Nijeriya, a shekara ta 1340 bayan Hijira dai dai da shekarar Miladiyya 1922.

Mallam ya tashi ne cikin kyakkyawar tarbiyya da natsuwa da tsafta da neman Ilimi karkashin kulawar mahaifin sa (Alkalin Gumi a wancan zamanin). Kuma yayi karance-karance na zaure a majalisi daban-daban na Malaman da suka shahara anan kasar Hausa a wancan lokaci, tare da karatu na nizamiyya daga nan kasar har kasar Sudan da kasar Saudi Arabiya.

Shaikh Abubakar Gumi mutum ne mai kokarin binciken Al-kurani da Sunna kan hukunce-hukuncen Shari’a, tun daga abin daya shafi Tauhidi, Hadisi, Fikhu da luggar Larabci, wanda karantarwar da yayi ta tabbatar da haka.

Muna fatan Allah (SWT) cikin Rahamar Sa yayi gafara da jin kai da daukaka ga wannan bawa na sa, wanda ya jaddada Da’wah ta Sunna a wannan kasa mai albarka, tun bayan wafatin Shaikh Usman Dan Fodio (RH).

TARIHIN SHEHU IBRAHIM INYASS

TARIHIN SHEHU IBRAHIM INYASS



Tarinhin shehul-islam sheikh ibrahim inyass

Shine sheikh ibrahim dan shehu Adullahi Inyass. An Haifeshi Agarin (daiban yasin) gari ne da mahaifinsa yakafa a kaulakh dake kasar senegal. Ranar alhamis Bayan la`asar 15 rajab ,1900. Hijra 1320.
Yatashi akan kularwar mahaifinsa, ya Haddace Al-Qur'ani a Hannun mahaifinsa Acikin kananan shekaru Ya wallafa littafi A rana daya yana da shekaru 21 aduniya. Ya turo ilimi Zahiri dana Badini Har Yazama baida Tamka a Fagen ilimi a duk duniya. Yazama Gagara Misali acikin son Manzo Allah (SAN) da yabonsa. Faiyar da Shehu Ahmadu Tijjani mai Darika yai Bushara da Zuwanta ta Bayyana a Hannunsa a HiJra 1348.

Yayi HIJra daga garinsu Kaulaka Ranar Safiyar Sallah 1939. Yatafi HaJJin Farko 1937 kuma a wannan shekara ce ya hadin da sarkin kano shehu Abdullahi Bayaro (sarkin AlhaJi) wanda yai Asalin shigowar shehu Nigeria
Shehu yai wallafa littafai Ba’ adadi daga cikin akwai, shahararren Duwaninsa da Kashiful ILbas da Ruhul –Adat . Yaba″YAya 75 MAZA da MATA ya rayu shekaru 75 yarasu A Asibitin London Rana 15 ga Rajab.An rufeshi A Madinarsa a Gaban Masallacinsa Raularsa ta Zama Abin Ziyara a Kowa ne Lokaci

A na Masa Lakabi da

Shehul Islam

Abu Ishaq

Sahibul Faidha

Inyass.

Allah yakaramashi Karama Amin

DON KARIN BAYANI A ZIYZRCI WWW.AL-FATIMIYYA.ORG

TARIHIN SHEKH JA'AFAR

Tarihin Sheikh Jafar Mahmud
Adam***
An haifi marigayi Sheikh
Ja'afar Mahmoud Adam a
garin Daura, a shekara ta 1962
(ko da yake wani lokacin
yakan ce 1964).
Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara
karatunsa na allo a gidansu, a
wurin mijin yayarsa, Malam
Haruna, wanda kuma dan
uwansu ne na jini. Daga nan
kuma sai aka mayar da shi
wajen wani Malam Umaru a
wani gari wai shi Koza,
kimanin kilomita 9 a arewa da
Daura, wanda shi ma akwai
dangantaka ta jini a tsakanin
su, wanda kuma shi ne
musabbabin zuwansa Kano.
Bayan sun zo Kano ne tare da
wannan malami nasa, a
shekara ta 1971 (ko 1972), sai
suka zauna a makarantar
Malam Abdullahi, wanda
asalinsa mutumin jamhuriyar
Nijar ne, amma yake zaune a
unguwar Fagge a Kano. Tun
kafin zuwansu Kano, tuni
marigayi Sheikh Ja'afar ya riga
ya fara haddar Alkur'ani mai
girma, wanda ya kammala a
shekara ta 1978.
Bayan da Malam ya kammala
haddar Alkur'ani mai girma,
kasancewarsa mai sha'awar
ilimi, sai ya shiga makarantu
biyu a lokaci daya a shekara
ta 1980. Ya shiga makarantar
koyon Larabci ta mutanen
kasar Misra a cibiyar yada
al'adun kasar Misra, (Egyptian
Cultural Centre), sannan
kuma ya shiga makarantar
manya da ba su yi boko ba ta
Masallaci Adult Evening
Classes, tunda a lokacin
shekarunsa sun wuce shekaru
na primary, amma duk da
haka a wannan lokaci shi ne
mafi kankanta a ajinsu. Haka
ya rika yin wannan karatu
guda biyu: Waccan
makarantar ya je ta da
daddare bayan sallar isha'i,
waccan kuma ta koyo harshen
larabcin da yamma. Ya
kammala wadannan
makarantu a shekara ta 1983.
Wannan kuma shi ya ba shi
damar shiga makarantar
GATC Gwale a shekara ta
1984, kuma ya kammala a
shekara ta 1988. A shekara ta
1989, malam ya sami gurbin
karatu a jami'ar musulunci ta
Madinah, a inda ya karanta
ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an,
wanda kuma ya kammala a
shekara ta 1993. Sannan kuma
Sheikh Ja’afar ya sami damar
kammala karatunsa na digiri
na biyu (Masters) a Jami’ar
Kasa-Da-Kasa Ta Afrika da
take Khartoum, Sudan.
Sannan kuma, kafin
rasuwarsa, ya riga ya yi nisa
wajen karatunsa na digiri na
uku, wato digiri da digirgir
(PhD), a Jami’ar Usman Dan
Fodiyo da take Sokoto.
Daga cikin malamansa na
ilimi, akwai malaminsa na
farko, mutumin kasar Masar,
Sheikh Abdul-Aziz Ali al-
Mustafa, da kuma Malam
Nuhu a unguwar Dandago,
wanda malam ya karanci ilimi
fikihun malikiyya da wadansu
littattafai na hadisi a gurinsa,
da kuma Malam Muhammad
Shehu, mutumin Lokoja,
wanda Malam ya karanci
nahawu da sarfu da balaga da
adab a wajensa. Akwai kuma
Sheikh Abubakar Jibrin
limamin masallacin Juma'a na
BUK, akwai kuma Dr. Ahmad
Muhammad Ibrahim shi ma na
jami'ar Bayero ta Kano. Daga
cikin malamansa na jami'a
kuma, akwai Sheikh
Abdurrafi'u da Dr. Khalid
Assabt.
Daga cikin karatuttukan da
malam ya karantar da su, sun
hada da tafsirin Alkur'ani mai
girma, Kitabuttauhiid,
Umdatul Ahkaam, Arba'una
Hadiith, Kashfusshubuhaat,
Bulugul Maraam,
Riyaadussalihiin, Siiratun
Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz,
Siffatus Salaatun Nabiiy.
Wasu daga cikin daliban
malam sun hada da Malam
Rabi'u Umar R/Lemo da
Malam Sani Abdullahi
Alhamidi Dorayi da Malam
Abdullah Usman G/Kaya da
Malam Usman Sani Haruna da
Malam Ibrahim Abdullahi Sani
da Malam Ali Yunus
Muhammad da Dr. Salisu
Shehu da Malam Shehu
Hamisu Kura da Malam Anas
Muhammad Madabo.
Kafin rasuwarsa, malam ya
fara gagarumin aikin rubuce
tafsirinsa a harshen Hausa a
karkashin wannan cibiya
(Sheikh Ja'afar Islamic
Documentation Centre).
Marigayi Sheikh Ja'afar
Mahmoud Adam ya rasu ranar
juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428
(13/04/2007) sakamakon harin
da wadansu 'yan ta'adda suka
kai masa, a daidai lokacin da
yake jagorantar sallar asuba a
masallacin Juma'a na Dorayi.
Ya rasu ya bar mata biyu, da
'yaya shida, yayin da aka haifa
masa ta bakwai kwanaki 58
daidai bayan aiwatar da
wannan kisan gilla a kansa.
Dubun-dubatar mutane ne
daga ko'ina cikin kasar nan
suka halarci jana'izarsa, kuma
an binne shi ne a makabartar
Dorayi. Allah ya ji kan sa ya
gafarta masa, ya saka masa
da gidan aljanna. Amin

MANUFAR KUNGIYAR JAMA'ATU IZALATIL BIDI'AH WA IQAMATIS SUNNAH (JIBWIS).



MANUFAR KUNGIYAR JAMA'ATU IZALATIL BIDI'AH WA IQAMATIS SUNNAH (JIBWIS).
Kungiyar kawar da Bidi’ah da tsayar da sunna
Wannan qungiya ta al’ummar musulmi an kafa ta ne tun a shekarar 1978 a Najeriya, kuma shugabanta na farko shi ne Alhai Musa Gandu Muhammad, a qarqashin kulawar Malam Abubakar Mahmud Gumi, tare da Sheikh Isma’il Idris bn Zakariyya, a matsayin shugaban majalisar malamai na farko na kungiyar.
Qungiyar ita ce irinta ta farko a tarihin yada addinin musulunci a Najeriya, hadi da harkar ilmantarwa, tare da daukaka darajar harkokin addinin Musulunci ba tare da wani tsoro ba. Don haka ne sai kungiyar ta sanya wasu ginshiqan manufofi da take so ta cimma domin kai wa ga gaci.
Daga cikin muhimman manufofin wannan kungiya sun hada da:
- Kawar da duhun jahilci daga cikin al’umma, wanda ya yi wa al’umma katutu.
- Hada kan al’ummar musulmi a bisa koyarwar Alqur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW),
- Wayar da kan al’ummar musulmi game da al’amuran addini, domin a gudu tare a tsira tare.
- Fadakar da al’ummar musulmi domin a yi watsi da wasu miyagun littattafai da suke tura mutane cikin halaka.
- Tabbatarwa da cewa Annabi (SAW) ya kammala isar da sakon Allah (SWT).
- Duk wanda ya yi da’awar annabta, ko kuma yake riya cewa Annabi (SAW) yana ziyartarsa da wani sako, to wannan zunzurutun makaryaci ne.
- Yada Musulunci a Najeriya da wajen Najeriya.
- Yin da’awa a kan fadin Manzon Allah (SAW) cewa: “duk wanda ya ga abin qi, to ya sauya shi da hannunsa, idan ba zai iya ba, to da harshensa, in ba zai iya ba, to da zuciyarsa, amma wannan shi ne mafi raunin imani.”
- Kar a boye hujja in dai har ta tabbata daga littafin Allah Madaukakin Sarki, ko sunnar Manzon Allah (SAW).
Wasu daga cikin ayyukan kungiyar sun hada da:
Kasancewar wannan kungiya ta shahara sosai a kasashe daban-daban na duniya, wannan ya sa aka samar da kwamitoci daban-daban domin gabatar da ayyuka da yawa. Wasu daga cikin kwamitocin kungiyar sun hada da:
- Kwamitin Da’awah.
- Kwamitin Tarurrukan Wa’azi.
- Kwamitin Kula da Marayu
- Kwamitin Ilimi.
- Kwamitin Mutane Goma.
- Kwamitin Taimakon Gaggawa.
KWAMITIN ZARTASWA
Shugabanta na kasa a wannan lokaci shi ne Sheikh Abdullahi Bala Lau, khalifa na farko a sashin shugabancin wannan kungiya tun bayan kafa kungiyar, wanda tsohon mataimakin shugaban kungiyar ne a zamanin shugabancin marigayi Alh. Musa maigandu Muhammad, kuma ya gaje shugabancin kungiyar ne bayan rasuwarsa.
- Marafan Tambuwal Shine: Mataimakin Shugaban Kungiya Na Kasa.
- Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe: Babban Magatakardan kungiya
- Sheik Sani Yaya Jingir: Shugaban Majalisar Malamai na kasa
- Sheik Dr. Ibrahim Jalo Jalingo Shine: Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na Kasa
- Alh. Isa Waziri: Shugaban Yan Agaji na Kasa
- Engr Mustapha Imam Sitti: Mataimakin Shugaban Rundunar Yan Aagaji na kasa
kungiyar ta samu karbuwa a sassa daban-daban na duniya. A Najeriya tana da rassa a dukkanin jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya. Haka kuma saboda irin yadda kungiyar take kokarin ilmantar da al’umma, wannan ya sa har ta sami kutsawa zuwa ga wasu kasashe, kamar su; Nijar da Mali da Sinigal da Togo da Kamaru da Cadi da Burkina da Gini, Saudi Arabia da sauransu.
Wasu daga cikin abubuwan da kungiyar ta mayar da hankali wajen yin su, sun hada da:
- Koyarwa a bisa tafarkin Manzon Allah (SAW) ba tare da bin son zuciya ko kuma yin makauniyar biyayya ga wani ba.
- Tsantsar karantar da hakikanin ilimin addinin Musulunci.
- Gabatar da wa’azin kasa a duk makwanni biyu ko uku ko hudu don tunatar da mutane abin da suka manta ko kuma lokutan da suka dace.
- Kafa makarantu domin koyar da ilimin addini da na boko, da sauran fannonin ilimi.
- Kai ziyarori gidajen marayu da gidajen yari da asibitoci, domin tallafar musulmai marasa galihu.
- Samar da taimakon gaggawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
kungiyar ta samar da hamshaqan malamai a sassa wadanda suka sami daukaka ta ilimi a fadin duniya baki daya, saboda jajircewa da kokarin bin tafarkin Manzon tsira, Annabi Muhammad (SAW), sau da kafa.
Haka kuma ta ko wacce fuska tarihin izala zaizo , dogo ko gajere, ba za a taba mantawa da irin gudummar da marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da Sheikh Isma'ila Idris Bin Zakariyya suka bada ba, da irinsu Marigayi Sheikh Ibrahim Bawa Maishinkafa, Sheikh Hudu Chikaji Zariya, Sheikh Adam Maishafi, Sheikh Abubakar Imam Ikara da Sheikh Alhaji Musa Maigandu Muhammad ba, Koda ba manufarmu zayyana sunan kowa ba, amma muna addu'a ga dukkan wadanda suka sadaukar da dukiyoyin su da kuma rayukansu akan wannan harka taci gaban addini, Allah ya saka musu da gidan Aljanna ya hada mu dasu a babban matsayi a lahira.
Haka Suma Dattawan Izala na Farko Irin su Sheikh Dr. Alhassan Sa'eed Adam jos wanda shine Alaramma na farko a tarihin kafuwar kungiyar, da Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe, Sheikh Sa'idu Hassan Jingir, Sheikh Abdullahi Bala Lau, Sheikh Sani Yahaya, Sheikh Rabi'u Aliyu Daura, Alaramma Abubakar Adam Katsina, Alaramma Yahuza Bauchi da Sauran Shuwagabanni da yan agaji, muna addu'an Allah ya saka ma kowa da alkhairi ya hada mu a gidan aljanna fir'dausi.
Wannan kadan ne daga cikin irin manufofin da kungiyar Izala ta kafu a kayi tun asali, kuma a haka za'a tafi da ikon Allah.
Muna Addu'an Allah ya karkato Mana Da Hankulan Jagororin mu a koma Karantarwan Kungiyar ta Asali, Wato Kira kan Kitabu Wassunnah.
Daga Karshe Muna Addu'an Allah ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya bamu ikon binta, ya nuna mana karya karya ce ya bamu ikon guje mata.